SHARHIN FIM DIN RAB NE BANA DI JODI

SHARHIN FIM DIN RAB NE BANA DI JODI
Rab Ne Bana Di Jodi Fim Din India ne  da aka yi a 2008, kuma Fim Din ya shafi soyayya ne da ban dariya.
Shi ne Fim Din Jaruma Anushka Sharma na Farko a Bollywood, inda ta fito tare da Jarumi Shah Rukh Khan a cikin sa. Kuma da wannan Fim ne mai bada umurni Aditya Chopra ya dawo bakin aiki bayan hutun da ya dauka na tsawon shekaru 8, domin Tunda ya kammala Mohabbatein bai sake bada umurnin Fim ba sai a Rab Ne Bana Di Jodi.
Sunan Fim Din Da Hindi -
रब ने बना दी जोड़ी
Bada Umurni - Aditya Chopra
Daukar Nauyi - Aditya Chopra Da
Yash Chopra
Rubutawa - Aditya Chopra
Jarumai - Shah Rukh Khan,
Anushka Sharma Da
Vinay Pathak
Hada Sauti - Salim-Sulaiman
Kamfanin Da Ya Shirya -
Yash Raj Films
Ranar Fita - 12 December 2008
Tsawon Fim Din - Minti 164
Kasa - India
Yare - Hindi
Kudin Da Aka Kashe - ₹ 22 Crore
Kudin Da Ya Kawo - Crore Biliyan ₹ 1.85
Fim Din bai samu Tallatawa ba kamar yadda sauran Fina Finan Kamfanin Yash Raj Films suka samu ba, haka kuma bai samu Tallatawa kamar yadda sauran Fina Finan Jarumi Shah Rukh Khan suka samu ba saboda masu shirya Fim Din sun zabi su tafi da aikin Fim Din cikin sirri saboda tashin hankalin da ya Afku a Mumbaai a wannan shekarar.
Lokacin da Fim Din ya fita ya samu Yabo sosai kuma ya kafa Tarihai masu yawa a akwatin Kasuwancin Fina Finan India domin sai da ya kai matakin 'Blockbuster', duk kuwa da cewa an Fitar Da Fim Din ne sati biyu bayan Afkuwar wannan tashin hankali da akayi a garin Mumbaai a 2008.
An Fitar Da Fim Din ne cikin Kila-Wa-Kala domin ba'a san yaya Kasuwancin sa zai kasance ba, amma a karshe, sai da Fim Din ya kawo kudi kimanin Croe Biliyan a duniya gaba daya, hakan yasa ya zama Fim Din da yafi kowane Fim kawo kudi a wannan shekarar kuma Fim Din Shah Rukh Khan Da Yash Raj Films da yafi kowane Fim kawo kudi a wancan lokacin.
Sauti da kidan Fim Din wanda Shahararre Salim-Sulaiman ya hada shi ma ya samu Karbuwa sosai domin sai da ya zama kundin Wakokin Fina Finan Bollywood na farko da ya fara samun damar shiga cikin Zafafan Kundayen Wakoki Goma a Matattarar iTunes.
Rubutun Fim Din shi ma ya samu Yabo sosai, domin kwana daya da fitar Fim Din aka Gayyaci marubutan da su kawo shi a Saka shi cikin Jerangiyar Rubututtukan Fim na  Margaret Herrick Library a Sashin Academy of Motion Picture Arts and Sciences, kuma ana iya samun damar kaiwa gare shi ne kawai domin fadada bincike, Dalibai, Marubuta, masu shirya Fim da jaruman Fim suna cikin wadanda suke kula da shi akai akai.
LABARIN FIM DIN
Wani Managarcin Mutum  mai kunya, Kawaici da tausayi da ake kira Surinder "Suri" Sahni (Shah Rukh Khan ) Ma'aikaci ne a daya daga cikin Ma'aikatun Punjab. Shi ne ya hadu da 'Yar Tsohon Malamin sa kuma Farfesa is an office employee for Punjab Power. Shi ne ya hadu da' YAR Tsohon malamin sa kuma Farfesa, wata kyakkyawar Yarinya mai suna Taani (Anushka Sharma), a Yayinda da ake Shirye shiryen auran ta.
Ba'a jima ba, sai ga mummunan labari ya zo musu cewa wanda zai aure ta da masu yi musu rakiya duk sun mutu a Sanadiyyar Hatsarin mota.
Wannan al'amari ne ya sa Mahaifin Taani ya kamu da ciwon Zuciya, bisa tsoron kada ya mutu ya Barta ita kadai, sai ya roki Surinder daya aure ta, Surinder sai ya amince, domin dama can yana son ta, ita kuma ta amince ne ne kawai ba don tana son shi ba.
Bayan an daura auren, sai Surinder ya dauki matar sa Taani ya tafi da ita gidan su da ke Amritsar. Inda Kirki da Karancin sa suka sa yake kulawa da ita fiye da tunani, domin har bar mata dakin kwanan sa yake yi ta kwana ita kadai, gashi dai yana son ta amma yana tsoron ya bayyana mata.
Daga baya Taani ta fada masa cewa zata Kokarta taga ta kyautata masa kamar yadda ya kamata mace ta kyautatawa Mijinta, amma ba Zata taba iya son shi ba, domin babu wani sauran gurbin so a cikin zuciyar ta tun bayan RASUWAR tsohon Saurayin ta.
Shi kuwa Surinder, yaji dadi sosai ganin irin yadda Taani ta fara kulawa da shi, don haka sai ya ci gaba da kokarin ganin ya biya mata duk bukatun ta, ciki kuwa harda daukar ta suna zuwa kallon Fina Finan Bollywood a Sinima, kuma hakan yana Matukar farantawa Taani din rai domin tana son Raye-Raye da Wake-Wake.
Watarana, Taani tana yawo a kasuwa, sai taga Sitikar Tallan Gasar rawa. Bayan ta dawo gida, sai ta roki Surinder da ya bata izini ta shiga Gasar Rawar, wacce za'a koyar akan Farashi mai tsada, domin a cewar ta hakan zai taimaka mata wajen sakin jiki tare da mantawa da Damuwar ta. Shi kuma sai ya amince mata, harma da bata kudin yin Rajista.
A irin zuwa kallon Fina Finan da Surinder Da Taani suke yi ne Surinder ya fahimci cewa Mazantakar Maza ne ke burge Taani. Don haka sai ya nemi Shawarar tsohon abokin sa
Balwinder "Bobby" Khosla ( Vinay Pathak ), wanda Wanzami ne, akan yadda ya kamata yayi domin ya samu soyayyar matar sa.
Bobby sai canja masa shiga, zubi da kuma Tsari, ciki kuwa harda aske masa gashin baki, canja masa tsarin gashin kansa tare da bashi wasu Matsatstsun kaya ya sa.
A nan ne suka Kirkiri Raj, daya daga cikin sunayen da Taani take so a cikin wani Fim da suka kalla tare. Bayan an gama sai Surinder ya tafi inda Taani zata yi rawa domin ya ganta ba tare da ta gane shi ba.
Abun Tsautsayi, sai shima aka saka shi a cikin masu yin Rawar. A karshen ajin Rawar, sai duk 'yan Rawar aka raba su gida biyu ta hanyar basu Mabanbantan lambobi. Bisa Kaddara, sai Surinder Taani dukkan su suka sami lamba iri daya, wato '21'. Don haka sai ya zama abokin Rawar Taani a Gasar Rawar.
Duk da kokarin da yake ta yi na ganin ya burge Taani da Salo irin na manyan Jaruman Fim, Taani bata Sakar masa jiki ba, sai ma GARGADI da tayi masa akan kada ya sake neman ya raina mata hankali.
A haka dai suka zamo abokai shi da ita Kasancewar suna aiki tare. Surinder yaji dadi sosai tare da samun kwarin Guiwa Yayinda Taani Taki ta daurama Raj Rakhi a hannun, domin hakan alama ce ta cewa ta dauke shi ne a matsayin Babban yaya kawai.
Ba'a dade ba sai Raj ya yanke Shawarar fita daga cikin Gasar domin bai iya rawa ba. Amma sai Taani ta Karfafa masa Guiwa. Cikin sa'a kuwa suka samu nasarar Hayewa zagayen karshe. Hakan yasa suka yi Gasar Golgappa, bisa Sharadin cewa duk wanda yayi nasara a cikin su zai tambayi/Bukaci komai yaga dama daga dayan. Raj ne yayi nasara, amma sai bai tambaye ta komai ba.
Washegari, sai Raj ya gaiyyace ta bikin zagayowar ranar haihuwar sa a matsayin abinda zai tambaye ta sakamakon Gasar da yaci. A nan ne ya bayyanawa Taani irin yadda yake bikin zagayowar ranar Haihuwar tasa shi kadai a ko yaushe.
Don haka sai suka dan zaga gari haka da Wurare da dama a Punjab, daga karshe dai Raj sai ya bayyana mata soyayyar sa a gare ta.
Taani ta girgiza sosai, kuma ta shiga damuwa sosai, shi ma Surinder sai abin ya dame shi, don haka sai yayi yunkurin bayyana mata soyayyar sa wanda hakan kuma ya kara dagula mata lissafi.
Da Dai taga abin yayi yawa, sai taje wurin Raj domin ya taimake ta, shi kuma sai yace mata ai kawai su gudu tare suje su fara sabuwar rayuwa, kuma ta yarda. Daga nan sai suka sa ranar guduwan nasu a matsayin daren Washegari, kuma a wannan daren ne za'a kammala Gasar Rawar.
Ran Surinder ya baci sosai Kasancewar Taani ta kasa Fahimtar soyayyar sa a matsayin sai sai dai a matsayin Raj. Daga karshe dai ya fadawa Bobby cewa zai kammala wasan da suke yi da hankalin Taani ta hanyar da yaga ta dace, ta hanyar Sadaukar da son da yake mata tare da bari mata komai nasa shi kuma ya Koma Delhi.
A ranar da za'a yi zagayen karshe na Gasar Rawar, sai Surinder ya dauki Taani suka tafi wata Majami'a domin ta samun albarkar abin bauta akan Gasar, amma a Zuciyar sa fata yake yi mata da ta sami rayuwa mai kyau ba tare da Raj ba.
A nan ne, Taani ta fahimci cewa auren ta da Surinder hadin ubangiji ne. Kuma a karo na farko, sai a wannan lokaci ne ta fahimci irin Nagarta da kuma karamcin da Surinder yake da shi. Taani sai ta fadawa Raj cewa ba Zata iya Zabar sa akan Mijinta ba. A nan ta barshi cikin damuwa da hawaye.
Da lokacin yin Rawar su yazo, Taani sai ta rude, domin Maimakon ta ga Raj, sai taga Surinder a fagen Rawar.
A Yayinda suke Rawar ne Taani ta dinga tunano wasu al'amura wanda suka bayyana mata lallai Raj ba kowa bane face Surinder.
Bayan su gama Rawar ne take Tuhumar sa dalilin sa na yin abinda yayi. Anan ne yake bayyana mata soyayyar sa inda ta amsa masa tana mai yin kuka.
Fim Din ya kare ne Yayinda aka nuno Taani da Surinder sun tafi Japan domin Yawon Shakatawa.
JARUMAN FIM DIN DA MATSAYIN SU
Shah Rukh Khan - Surinder "Suri" Sahni, Raj
Anushka Sharma - Taani
Vinay Pathak - Balwinder 'Bobby' Khosla
Manmeet Singh - Raju
Richa Pallod - Mai Koyarda Rawa
M.K. Raina - Mahaifin Taani
Aneesha Dalal - mai Koyarda rawa
MASU FITOWA TA MUSAMMAN
Kajol
Nargis
Bipasha Basu
Lara Dutta
Preity Zinta
Sharmila Tagore
Rani Mukerji
Neetu Singh
WAKOKIN FIM DIN
1 "Tujh Mein Rab Dikhta Hai"
2 "Haule Haule"
3 "Dance Pe Chance"
4 " Phir Milenge Chalte Chalte
5 "Tujh Mein Rab Dikhta Hai (Female)
6 "Dancing Jodi" Instrumental
7 "Tujh Mein Rab Dikhta Hai" (Hinglish Mashup)
LAMBOBIN YABO (AWARDS)
Apsara Film & Television Producers Guild Awards
Best Actor – Shah Rukh Khan
Best Debut Female – Anushka Sharma
Best Choreography – Shiamak Davar – "Dance Pe Chance"
Best Lyrics – Jaideep Sahni – "Tujh Mein Rab Dikhta Hai"
Female Playback Singer – Shreya Ghoshal – "Tujh Mein Rab Dikhta Hai"
Filmfare Awards
Best Male Playback Singer –
Sukhwinder Singh ("Haule Haule")
Best Scene of the Year
Nominated – Best Film – Aditya Chopra
Nominated – Best Director – Aditya Chopra
Nominated – Best Actor – Shah Rukh Khan
Nominated – Best Actress – Anushka Sharma
Nominated – Best Supporting Actor – Vinay Pathak
Nominated – Best Female Playback Singer – Sunidhi Chauhan ("Dance Pe Chance")
International Indian Film Academy Awards
Nominated – Best Actor
Nominated – Best Supporting Actor – Vinay Pathak
Nominated – Best Male Playback Singer
Nominated – Best Lyrics
Stardust Awards
Nominated – Best Film
Nominated – Best Director
Nominated – Stardust Award for Star of The Year – Male
Nominated – Stardust Award for Superstar of Tomorrow – Female
Star Screen Awards
Nominated – Best Actor – Shah Rukh Khan
Nominated – Most Promising Newcomer – Anushka Sharma
Nominated – Best Choreography
Nominated – Best Male Playback Singer
Nominated – Best Female Playback Singer
Nominated – Best Lyrics
Haiman Khan Raees
@HaimanRaees
08185819176
Infohaiman999@gmail.com

Post a Comment (0)