SHAWARA GA AMARE

↝ sirrin rike miji
Sirrinrikemiji@gmail.com
Sirinrikemiji@gmail.com
☏+2348037538596
*・SHAWARA GA AMARE・*

1. Tun da dai ke budurwace baki taba aure ba, to ki guji duk wasu kayan da’a ko hakkin maye da za a ba ki don ki sha, domin tun asali irin wadannan magunguna an yi su ne don matan da suka dan jima cikin aure kuma zumar sha’awarsu ta dan fara sanyi.

Wadanda ba su taba aure ba kuwa zumarsu na nan da zafinta, don haka babu wani dalili na zukakata da irin sinadaran zukakawa;

wannan ke sa nan gaba a samu rikirkicewar sha’awa domin yamutsa ta din da aka yi da wadannan sinadarai maimakon a bar ta ta tafiyar da kanta a kan irin tsarin da Allah Ya tsara mata.

2. Amma kina iya shan ‘ya’yan itatuwa da yawa gab da bikin naki, inda hali ma, kina iya daina cin duk wani abinci illa ‘ya’yan itatuwa da ganyayyaki kadai kamar ana sauran sati daya bikin naki.

Don haka ya zama dole, tun ranar farko na auren, ma'abutan biyu su yi kokari wajen kare wannan so da kauna da Allah Ya dasa cikin zukatansu. Ya kamata su yi kokari wajen kara wannan kauna da soyayya da kuma karfafa su. Hanyar cimma hakan kuwa, kamar yadda na fadi ne a baya, ita ce ta hanyar taimakon juna da kiyaye mutumci da manufofin juna. A matsayinsu na ma'aurata biyu, dole ne su kiyaye sirrin juna, kada su fade su ga wasu ko da kuwa dangi ko na kurkusa da su ne, dole ne ku kiyaye irin shigar da kuke yi. Idan har kuka kiyaye hakan, to babu makawa za ku ji dadin zaman aurenku.
☛ click here
http://sirinrikemiji.blogspot.com.ng/2018/04/kafin-daura-muku-aure_1.html

Post a Comment (0)