TSOKACI KAN FATAWAR SHEIK IBRAHIM KHALIL

TSOKACINA KAN FATAWAR SHEKH IBRAHIM KHALIL..........
Naji Shehin malamin ya halatta qarin gashi ga mata, ya halatta qarin girman mama, kuma ya halatta qarin girman mazaunai.
Inda ya haramta kurum idan yazam anyine Dan yaudarar maza.
To a gaskiya ya kamata shehin malamin ya fito ya fadi nassin da yadogara dashi kan wannan halaccin.
Sannan yafadi nassin da ya dogara dashi kan ban-banta tsakanin yi Dan yaudarar maza,da kuma yi Dan ado.
Shidai Abdullahi Dan mas'ud ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ cewa yayi:-
: ﻟَﻌَﻦَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺍﻟْﻮَﺍﺷِﻤَﺎﺕِ ﻭَﺍﻟْﻤُﻮﺗَﺸِﻤَﺎﺕِ، ﻭَﺍﻟْﻤُﺘَﻨَﻤِّﺼَﺎﺕِ، ﻭَﺍﻟْﻤُﺘَﻔَﻠِّﺠَﺎﺕِ ﻟِﻠْﺤُﺴْﻦِ، ﺍﻟْﻤُﻐَﻴِّﺮَﺍﺕِ ﺧَﻠْﻖَ ﺍﻟﻠَّﻪِ .
Kaga ﺍﻟﻤﺘﻔﻠﺠﺎﺕ ﻟﻠﺤﺴﻦ masu janzawa Kansu halitta Dan qarin kyau da Ado sun Shiga ciki.
Dan haka maganar malam ta cewa sai yazama Dan yaudara sannan ya haramta, to ta rushe.
Shin wai Matan da sukeyi Dan wace manufa sukeyi , Dan yaudara  ko kuwa haka kurum ??
Dan mata 'yan uwansu sukeyi ko kuwa Dan maza ??
Shin idan namiji yaga masu irin wannan ya aura,daga baya kuma yagane cogene, shin hakan bazai iya shafar zaman auransu ba ??
To meyasa malam bazai toshe qofar samuwar matsala cikin aureba ??
ﺩﺭﺀ ﺍﻟﻤﻔﺎﺳﺪ ﻣﻘﺪﻡ ﻋﻠﻰ ﺟﻠﺐ ﺍﻟﻤﺼﺎﻟﺢ
Atoshe qofar afkuwar matsala cikin auren,shine abin gabatarwa.
Kodama yin hakan ta halatta.
Kai koda mutafi kan fatawar malam,cewa yana halatta ta wata fuskar yana haramta.
To meyasa malam bazai aiki da qa'idar malaman usul  ta
ﺇﺫﺍ ﺍﺟﺘﻤﻊ ﺍﻟﺤﻼﻝ ﻭﺍﻟﺤﺮﺍﻡ ﻏﻠﺐ ﺍﻟﺤﺮﺍﻡ ba ??
Gaskiya sakin irin wannan fatawa akafar radio ba qaramar barna bace.
Kuma gidan radio freedom kunada laifi,domin kun shirya shirinne Dan magance matsalar sakamakon yawaitar hakan.
To Amma sai kuka bude sabuwar qofa ta shiga matsalar

Post a Comment (0)