ZANYI KATOBARA

ZANYI KATOBARA ZANYI RASHIN KUNYA ZAN FADI GASKIYA you can come and beat me... Rayuwa ÿa mace akan siradi yake tun daga shekara 5 har zuwa girmanta A shekara 5 ana fara aiken mace zuwa siyan pure water biscuits or kayan miya sabida a ganin iyaye cewa ta isa aike Da zarar taje shago sayan abu me shagon in ze ansa kudi wurinta seya haďa da hannunta ya matse ko ya shafa mata hannu wanda in bata da wayo baza ta taba daukar hakan wani abu ba idan me wayo ce tana tsoron iyayenta amma baza ta iya fada cewa ana taba mata hannu in an aiketa bay... Ba iya masu shago kawai suke haka ba har da sauran mutane da ake alaqa dasu yau da gobe... Daga wannan lokacin dayawa zasu na yaudarar ta da biscuits alawa kudi dan kawai ta ringa zuwa suna saka mata hannu a pant... Idan akayi mummunan Rashin saa se ayi raping dinta tana da qaramin shekaru... Duk hakan yana faruwa sabida tana qarama bata da wayo kuma tana tsoron sanar da iyayenta Da zarar ta kai shekara goma zuwa shadaya anan zata gane cewa ta fara girma abinda ake mata ba daidai bane ba Lokacin da jikin mace ya fara nuna alamun girma a shekara sha uku zuwa sha hudu surar jikinta ya fara bayyana a hanyar makaranta ko aike ko wani abu zata ta gamuwa da masu dangwale mata nono suna guduwa ...wata tayi kuka wata ta share amma hakan yana mata zafi a ranta Da mace ta kai 15 years samari zasu fara tururuwar zuwa wurinta Wanda kashi 99.9% ba aure ya kawo su ba kuma ita ma a wannan lokacin ba lallai aure zaa mata ba... A nan zaa samu Wanda yafi kowa dadin baki da iya zance ya sace mata zuciya ita kuwa ganinta duk duniya shi kadai yake sonta yake kaunar ta duk Wanda ze gaya mata kawai gani take cutarta zeyi ya rabata da masoyina... Da ya samu dama daga 15-20years ze rabata da budurcinta wurin amfani da kalamai kamar haka: •KIN FI SO NAJE NA NEMA MATA? •IN BAKI TAIMAKA MAN BA WAYE ZE MAN ? •BAKYA KISHINA ? •SAU DAYA KAWAI •MUNA SABAWA ALLAH KUMA IN MUN ROKE SHI ZE YAFE MANA •BAZAA GANE BA A GIDA •NI ZAN AUREKI BAZAN TABA RABUWA DA KE BA HAR ABADA •BAZAN TABA GUDUN KI BA •BAZAN IYA RAYUWA BABU KE BA •DAYAWA MATA DUK SUNA YI Soyayya, shaidan, zuciya, qaddara, yaudara, tsoro da kuma rauni... wannan sune abinda ze sa ta yarda ta amince ya mata abinda ze mata tun a lokacin zata fara jin dama bata zo duniya ba dama mutuwa tayi kafin lokacin... Tun daga nan ze fara ja baya da ita har ya ringa wulaqanta ta har Zuwa ya rabu da ita gaba daya sabida babu abinda ya saura Wanda yake nema wurinta ya riga ya samu zata shiga tashin hankali daga baya zata jure sannan ta fara sabuwar rayuwa maza dayawa zasuyi ta tururuwa zuwa neman aurenta amma dayawa jikinta suke fara nema in ta qi yarda su guje ta in ta yarda shine zata fara rabawa maza kanta ganin cewa to me ya saura bayan an riga an cuceta/ta cuce kanta tana rayuwa ne bata jin dadin shi baqin ciki ze sa ta fara shan syrup da shisha sabida ta ringa samun nutsuwa shi kuma shan syrup/shisha da lesbianism kamar cross multiplication ake samu daga shan syrup/shisha mace take Zama lesbian... idan kuma ta samu tayi aure ta samu miji me iya riqeta zata ji dadin rayuwar ta in aka samu akasin haka rayuwarta zata ci gaba da mata kunci. banbancin kawai ta yi aure tasan me takeyi... iyaye suna taka muhimmiyar rawa gurin bawa yaransu tarbiyya na kwari saidai da zarar an fita waje kuma ba bi yaransu zasu keyi suna kallan wani irin rayuwa suke Yi a waje ba baza su san wasu irin mutane suke gamuwa dasu ba ko suke muamala dasu adduan iyaye da kariyan ubangiji yake tsallakar da mata daga wannan siradin na duniya... dan haka ina roqan iyaye da su miyar da hankali wurin ma yayansu addua domin wayo ko dabara baze taimaki rayuwar su ta yan matanci se addua kawai Mace Tana da rauni, tana da saukin shawo kanta ,mace ÿa ce ,qanwa ce ,uwa ce ... Kaima zaka haifa duk me kayi ma yar wani zaka gani kan taka.... To laifin me yarka tayi maka da ka zaba mata irin wannan rayuwar? MAZA MU KULA DA MATA DOMIN SU KADAI BAZA SU IYA KULA DA KANSU BA........ Daga naku Nazir ibrahim mai arewa.

Post a Comment (0)