_*“BA ZAN DAUKI AZUMI BA HAR SAI NA GA WATA DA IDANU NA.”*_
_*WANNAN 👆🏿 ZANCE NE NA BATATTU.*_
➖➖➖➖➖➖➖➖➖
_Assalamu alaikum Warahmatullah._
_Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu, wanda cikin ikonShi ne na samu damar gabatar da wannan rubutu gare ku, tsira da amincin Allah su kara tabbata ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (ﷺ)._
_Na yi wannan rubutu ne don ya zama tsokaci ga wasu irin mutane musulmai, wadanda suke da wata dabi'a gurbatacciya dangane da ganin watan Ramadan. Irin Wadannan mutane sun yawaita a cikin musulmai musamman ma a kasarmu ta Hausa, su dai sun kasance suna da wata fahimta ne ta cewa Ba za su dauki azumi ba, har sai sun ga wata da idanunsu._
_A zahirin gaskiya, an fi samun irin Wadannan mutane a cikin 'yan dariku da 'yan gargajiya. Domin duk mai irin Wannan fahimtar ba za a kira shi da Ahlus Sunnah ba, domin fahimta ce wacce ta saba wa sunnar ma'aiki (ﷺ). Sannan mafi yawan masu wannan dabi'a za ka samu jahilai ne, ko kuma shagalallu wadanda suka shagala da al'amuran duniya, dalili kuwa shi ne; Za ka samu cewa ba a cika daukan azumi tare da su ba, domin ba a kowane gari bane ake ganin wata a ranar da ya tsaya saboda wasu dalili, amma kuma za ka samu cewa yawancin su tare da su ake aje azumi, koda kuwa ba su cika azuminsu ba, domin ni da idona na ga wadanda a wancan azumin da ya gabata, azumi 28 suka yi aka ce an ga wata, kuma suka ajiye aka yi sallah tare da su. Wannan ze nuna maka cewa lalaci ne da shagala take sawa suke aikata hakan. Kuma koda ma sun ci gaba da azumin, to aikin banza suka yi domin Allah ba zai karba ba, don watan Ramadan ya riga ya tafi a wannan lokacin._
_Shin me Wadannan mutane suke takama da shi ne har girman kai ya sa suka karkace wa fahimtar Annabi (ﷺ)???_
_Ya tabbata a hadisi cewa, Ibn Umar (r.a) ya ce: “ Mutane sun ga wata, sai na ba Annabi (ﷺ) labari cewa; lallai nima na gan shi, sai ya yi azumi, kuma ya umarci mutane da azumtarsa". Abu Dawud ya ruwaito shi, Hakim ya inganta shi da Ibn hibban._
_Wannan ke nuna cewa, fiyayyen halitta (ﷺ) ma, wanda ya fi mu daraja ta kowani fanni, an bashi labarin ganin wata kuma ya gasgata, ya yi azumi kuma ya yi umarni a yi. To don me kai za ka ce sai ka gani da idonka? Ko kafi Annabi hikima da wayau ne?? Ko kuwa girman kai ne da duhun jahilci da shagala???_
_Da zarar an ce ina masoya Annabi (ﷺ) sai ku fara bambami, ku yi ta zagaye gari kuna bugun kirji wai duk da sunan ku masoya manzo ne. To haka ake soyayya bacin ba ku yin koyi da shi? Wallahi duk wanda ya bi wata hanya daban sabanin ta Annabi Muhammad, to Wallahi ya bi hanyar bata._
_Ku sani! Saba wa Manzon Allah, tamkar saba wa Allah ne. Allah (ﷻ) Ya ce:_
*”.... وَمَن يَعصِ اللَّهَ وَرَسُولَهُۥ فَقَد ضَلَّ ضَلَٰلًا مُّبِينًا“*
_*“.... Kuma wanda ya saɓa wa Allah da ManzonSa, to hakika ya ɓace, ɓata mabayyaniya.”* (Al-Ahzab 36)_
_Don haka, Ina kara Fadakar da 'yan uwa Musulmi a kan mu bi Allah da ManzonSa. Mu guji bijiro da wani al'amari na daban a cikin addinin Musulunci._
_Ina yi wa kowa fatan alkhairi. Allah Ya sa mu yi azumin watan Ramadan muna masu imani, lafiya da aminci._
_Dan uwanku a Musulunci:_
_*✍🏿Ayyoub Mouser Giwa.*_
_*📱08166650256.*_
_Daga Zauren Islamic Post WhatsApp._