*_AKWAI GADO GA MATAR DA MIJINTA YA MUTU BATA GAMA IDDA BA?_*
*Tambaya*
Assalamu alaikum Mal mutum ne ya saki matarsa Bai dawo da ita ba kuma bata gama idda ba sai ya rasu, shin zata ci gadonsa?.
Allah ya kara ma mal imani DA ilimi mai amfani Ameen.
*Amsa:*
Wa'alaikumus salaam wa rahmatullahi wa barakaatuhu, to dan'uwa Idan miji ya saki matarsa, kuma ya mutu kafin ta gama idda, to za ta ci gadonsa Mutukar saki daya ne ko biyu, saboda har a lokaçın tana nan a matarsa, amma in uku ne babu gado a tsakaninsu, haka nan idan fansar kanta ta yi, saboda ta nisanta daga gare shi.
Allah ne mafi Sani.
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.