A GANI NA...


A ganina, yin mu'amala da mutane akan tsarin:
* Idan ban amfanar da kai ba to bazan cutar da kai ba.
* Idan ban sa ka farin ciki ba to ba zanyi sanadiyyar sa ka baqin ciki ba.
* Idan ban yabeka ba to bazan aibataka ba.
* Mafi muhimmanci kuwa abinda duk da bai shafeni ba kuma ba a saka ni ciki ba to ba ruwana da shiga cikinshi matuqar babu lalurar hakan.
Zai kawo raguwar matsaloli da dama da mutane kan haifarwa da junansu a zaman tare....
Allah ka sa mu dace amin.
- Zainab Ja'afar Mahmud

Post a Comment (0)