HASSADA MUGUN JARI

✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴

​ ​ABOKIN FIRA​​

​Rubutawa:​ ​Dr. Muhammad Mansur Sokoto​

*HASSADA MUGUN JARI*

Wasu makwabta ne guda biyu, abokan juna; Jibo da Tanko. Jibo mawadaci ne, Tanko kuma talaka. Watarana Jibo ya tashi yin kyauta sai ya nemi shawarar Tanko yana cewa: “Malam Tanko, kyauta nake son yi
ma wani bawan Allah talaka. Mene ne shawararka: in saya masa gida ya tashi daga gidan haya? ko in saya masa mota ya riqa jigila yana
neman abinci da ita? Tanko ya ce: “Alhaji, ka san talakawa fa ba a iya
musu. Kawai ka ba shi Naira dubu goma ya ja jari.” Jin haka sai attajirin
ya ce: Haba Tanko! Ya za ayi dubu goma ta yi jari? Tanko ya ce, wallahi Alhaji duk wanda ka ba shi dubu goma bai gode ba to kuwa hadama ce ta ishe shi. Don haka, ni shawarata kawai ka ba shi dubu goma. Jibo ya
ce, Shawararka kenan? Ya ce, kwarai kuwa. Ai talaka ba ayi masa gata.
Nan take sai Jibo ya zaro Naira dubu goma ya ba shi, ya ce: “Daman kai
ne na yi niyyar yi ma kyautar”! �

⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇
Email: jibwissocialmediaktlg@gmail.com
Facebook: Jibwis Katsina L.G
WhatsApp: 07062584992, 08036487324, 08038977817, 08034453678, 08036958490

Post a Comment (0)