☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
*🌼🌼🎍KYAUTATA RAYUWA🎍🌼🌼*
*💐HADADDUN((❤))MASOYA💐*
*💫ELOQUENCE WRITERS FANZ💫*
*🥀📚DUNIYAR HAUSA NOVELS 📚🥀*
🏡 《♡GROUPS♡》🏡
KYAUTATA RAYUWA
___________________
______________________________________
*тαяє ∂α нα∂ιи кαи :*
*♡ʍմհíҽѵҽɾԵ íղժíɑ (ҽɾ íղժíɑ)✍🏻*
*♡ʍíʍíϲíօմՏ ɑղցҽӀ ✍🏻*
*♡ʍɾ ʍҽӀօժվ ɑմԵɑղ ҽӀօզմҽղϲҽ ✍🏻*
*♡Ƙíղց ҍօí íՏɑհ ✍🏻*
*♡Qմҽҽղ ղҽɾժҽҽվ ԵմɾɑƘҽҽ ✍🏻*
*♡Dɾ zɑíղմժժҽҽղ✍🏻*
*♡Nɑ'íɾɑ ժɑմցհԵҽɾ✍🏻*
*♡Aհʍҽɾժ✍🏻*
*♡ʍɑíʍɑɾԵɑҍɑ✍🏻*
*♡HɑƒՏɑԵ Թմɾҽ ցɾҽҽղ✍🏻*
*♡Jɑհҽҽժ✍🏻*
*♡ՏհɑʍՏíվվɑ ՏɑӀíՏ✍🏻*
____________________________________
. . . . . . . . . . . . . . SHAFI NA (1)
ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATULLAHI TA'ALA WA BARAKATUHU....
Inayi mana barka da saduwar mu cikin wannan shirin da muka jima munayi muku albishir da ita.
Toh masha Allah daya daga cikin mu ta rigaya da fara bakin kokarin ta wanda alhamdulillahi muna mutukar jindadin shirye shirye da take gudanar mana cikin hikima da nasiha agaremu da kowa.
Bikudratillahi nayi shaawar mana nuni koh kuma in ce tunatarwa akan abinda ya shafe halayya, ra'ayi, muradi, koh yakamata acikin rayuwar Dan Adam musulmi dadai saura.
Acikin wannan shafinmu na farko zanfi karfafa bayanine Akan tsarki. Kuma da na ambaci tsarki bawai ina nufin tsarki bayan haila , beki, koh janaba kawai ba, aa ina magana ne Akan tsarkake ilahirin rayuwa kama daga ;
👉Tun ranan da Dan Adam ya mallake hankalinsa yasan cewa shi musulmi ne toh akwai bukatar ya tsarkake tunanin sa da imaninsa da arzikinsa, ayyukansa, zamantakewar sa da duk wanda Allah ya hadashi a rayuwa ko da iyayen sane ko iyalansa da makwafci har abokanan harkalla.
Amma daga ina yakamata ya fara Don samun cikon buri!
👉🏻Toh ya nima sani Akan addininsa kuma yayi aiki da duk wani sani da yayi dace dashi gwargwadon ikonsa
👉Ya sanya ikhlasi acikin ayyukansa na yau da kullum yazamana cewa tsoron Allah yana tasiri cikin zuciyarsa kowani lokaci. Kome yazo aikata ya rika tuni da cewa sanin Allah ya buwaye komai masanin gaibu da bayyane ne mai ilimin duk wani sirrinsane kuma mai saka alkhairi ne da mafificin alkhairi
Wato ko mai zai aikata gwargwadon girman kwayar zarra na alkhairi ko sharri xai hazashi bisa sikeli ya masa sakayya dashi.
👉Duk abinda zai aikata ya yi shi sabida Allah tare da niman sanin hukuncin Allah acikinsa ko da aikin gwamnatine, soyayya, kasuwanci, aure, karatu,koyarwa koma, dai menene da ya shafe rayuwarsa duk yayi su da zuciya wahid hade da sanya tsoron Allah acikin sa
👉sannan da taimakon hakan zai samu fili ko damar tsarkake zuciyarsa wanda in shaa Allah a shafinmu na biyu kanta zanyi sharhi.
Allah ya mana lamuni da aikata mai kyau acikin rayuwar mu bisalaam
MIMICIOUS ANGEL
🌼🌼🎍KYAUTATA RAYUWA🎍🌼✍🏻*
🍵🍧Asha________Ruwa________Lafiya☕🍜
Masha allah jazakumullahu kairan Allah ya kara mana imani da jin tsoronsa amin
ReplyDelete