☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
*🌼🌼🎍KYAUTATA RAYUWA🎍🌼🌼*
*💐HADADDUN((❤))MASOYA💐*
*💫ELOQUENCE WRITERS FANZ💫*
*🥀📚ER INDIA NVLS/KTCHN📚🥀*
🏡 《♡GROUPS♡》🏡
_________________________________________________________
*тαяє ∂α нα∂ιи кαи :*
*♡ʍմհíҽѵҽɾԵ íղժíɑ (ҽɾ íղժíɑ)✍🏻*
*♡ʍíʍíϲíօմՏ ɑղցҽӀ ✍🏻*
*♡ʍɾ ʍҽӀօժվ ɑմԵɑղ ҽӀօզմҽղϲҽ ✍🏻*
*♡Ƙíղց ҍօí íՏɑհ ✍🏻*
*♡Qմҽҽղ ղҽɾժҽҽվ ԵմɾɑƘҽҽ ✍🏻*
*♡Dɾ zɑíղմժժҽҽղ✍🏻*
*♡Nɑ'íɾɑ ժɑմցհԵҽɾ✍🏻*
*♡Aհʍҽɾժ✍🏻*
*♡ʍɑíʍɑɾԵɑҍɑ✍🏻*
*♡HɑƒՏɑԵ Թմɾҽ ցɾҽҽղ✍🏻*
*♡Jɑհҽҽժ✍🏻*
____________________________________
*⊙BIYAYYA●●●●●●●GA●●●●●●● MIJI⊙*
Yi biyayya ga miji domin samun tsira duk abinda ya baki umarnin kiyi toh kiyi shi matuk'ar be keta addinin musulunci ba, biyayya ga miji na k'arawa mace k'ima, martaba da mutunci,har ma da cigaba a rayuwa kuma yana k'ara soyayyarta cikin zuciyar mijin ta, sannan kuma zai kasance mai alfahari da ita koda kuwa baya yaba halinki na gari toh! A bayan idonki sai ya yaba miki kuma yasan me kike yi koda ace be tab'a furta miki ba.
Ba kowacce mace ce take iya jure yin biyayya ga mijinta ba, da yawan mata shaid'an yakan rinjayi zuk'atansu wajen sab'awa miji da kuma take umarnin sa wanda dalilin hakan mace takan jefa kanta halin data sani, tunda daman aljannar mace na k'ark'ashin tafin k'afar mijinta. Kiyi biyayya ga miji domin samun tsira musamman a wannan wata da muke ciki na *Ramadan* in kikayi biyayya gare shi sai ki samu duk ladan da mata na gari suke samu koda ace kin saba sab'a masa dalilin faranta masa da yin biyayya da kika yi cikin wannan wata sai kiga ya yafe miki laifukan ki na baya ki had'a ladan ki gaba d'aya na cikin wannan wata mai alfarma mai albarka.
*_D'abarani ya rawaito cewa:_*
```قال صل الله عليه وسلم:كان رجل قد خرج إلى سفر وعهد إلى إمرإته آن الا تنزل من العلو إلى السفل و كان آبوهما في الاسفل فمرض فآرسلت المرآة إلى رسول الله صلى الله عليه وسلم تستآذن في النز ول إلى آبيها فقال آطيعي زوجك فمات فاستآمرته فقال آطيعي زوجك فدفن آبوها فآرسل رسول الله(ص)إليها يخبرها آن الله قد غفر لها وﻷبيها بطاعتها لزوجها.رواه الطبراني....```
*(ωαииαи нα∂ιѕιи уαиα вαуαиι αкαи ѕαкαмαкσи вιуαууα gα υмαяиιи мιʝι)*
_MANZON ALLAH (S.A.W) YA FAD'A: WANI MUTUM YA KASANCE YA FITA IZUWA TAFIYA YA ALKAWARTA IZUWA MATAR SA, KA DA TA SAUKO DAGA SAMAN BENE IZUWA K'ASA, MAHAIFIN TA YA KASANCE A K'ASAN SAI YAI RASHIN LAFIYA SAI TA AIKA WATA MATA MACE IZUWA MANZON ALLAH (S.A.W) TANA NEMAN IZININ SAUKOWA IZUWA MAHAIFIN TA MANZON ALLAH (S.A.W) YACE TABI UMARNIN MIJINTA SAI MAHAIFIN TA YA RASU SAI TA SA KE NEMAN IZININSA, SAI MANZON ALLAH (S.A.W) YACE: KIBI UMARNIN MIJINKI SAI AKA BINNE MAHAIFIN TA SAI MANZON ALLAH (S.A.W) YA AIKO IZUWA GARE TA YANA BATA LABARI HAK'IK'A UBANGIJI YA YI GAFARA GA MAHAIFIN TA._ *_D'abarani ne ya rawaito shi_*
Ki zamo mace ta gari domin mijinki yayi alfahari da ke kuma ki samu hanyar tsira wajen ubangijinki.
*_Musulumu ya rawaito cewa_*
```قال صلى الله عليه وسلم: الدنيا متاع وخير متاع الدنيا المرآة الصالحة.رواه مسلم...```
*(ωαииαи нα∂ιѕιв уαвα вαуαиι αкαи мα¢є тα gαяι)*
_MANZON ALLAH (S.A.W) YA FAD'A: DUNIYA ABIN AMFANI CE, MAFI ALHERIN AMFANIN DUNIYA MACE MANAGARCIYA._ *_Musulumu ne ya rawaito shi_*
Allah yasa mu dace amin, dafatan za'ayi amfani da abinda yake na gyara ciki a gyara, anan zamu d'iga aya sai ku tara damu cikin wani sabon shirin karku manta sunan shirin namu *_KYAUTATA RAYUWA_* Dafatan za'a sha ruwa lafiya.
👉🏻 *🌼🌼🎍KYAUTATA RAYUWA🎍🌼✍🏻*
🍵🍧Asha________Ruwa________Lafiya☕🍜