YADDA AKE FUNKASO

☘🌿YADDA AKE FUNKASO🌿☘
ALKAMA(gwangwani hudu
FILAWARKI( gwangwani daya)
RUWAN TSAMIYA(kamar rabin gwangwani)
YEAST(cokalin shayi karyayi tsiri)
SIKARI(cokali daya)
RUWAN KANWA (cokali daya) 
MANSUYA ( kwalba daya)
🌿☘yadda  zaki hada🌿☘
Kisami robarki mai murfi ki zuba sikariki da da yeast da ruwan tsamiya da kanwa kamar yadda na auna miki  filawarki ki hadata da garin alkamarki idan yeast ya narke kijuye filawarki ki kwaba sosai ki tabbatar ba gudaji kuma kar kwabin yayi ruwa karkuma yayi tauri tikiki saiki rufe ya samu kamar awa daya zakiga ya tashi ki dora manki yayi zafi sosai ki sami kwabin ki kara juyashi sosai zakiga ya koma ya kwanta kuma zakiga ayayin da kika dada juyashi kwabin ya dada sakin jikinsa saiki sani dan farantinki ki shafe da ruwa kirika gutsurar kullin kina sawa akan dan farantin ki huda tsakiya saiki saka acikin mai zakiga yana dagowa yana fadawa cikin mai a hankali da kulawa abin
Lura shine funkaso bayason yawan juyawa idan kinga kasan ya soyu saiki juya saman shima ya soyu kuma funkaso bayason mai kadan wajan suya yafison mai wada tacce ya sakata ya wala amfanin tsamiya a funkaso shine bazai taba sha miki maiba kuma zai miki suya tai ja tayi kyau wannan shine iya awon danayi idan da yawa zakiyishi to haka zakirika aunawa kina kara yawan abinda na lissafo miki uwargida ko amarya dafatan zaki nutsu wajan gwaji
Nagode BINTU CE  IN OUR KITCHENS😀👍🌿☘

Post a Comment (0)