Eznah 13

*_EZNAH_*🌹
        _wattpad@mamuhgee_




*14*
Zaune baffa yake kan tabarma yayi zuru dawowarsa masallaci kenan
Jafar na gefensa zaune shima cikin rashin da'din Rai Sai aliyu dake tsaye gefe shima dai ran ba da'di
Hamma Yusuf  da Usman kuwa daga masallaci gidan mande direba suka nufa suka sanar dashi zasu bisa idan zai koma da safen sbd su dubo can din koza'a dace Dan Sam Babu Wanda ya rintsa a gidan tunda motar daliban ta iso aka nemi Anano ba'a gantaba Nan hankali yayi tsananin tashi gasu ubaidah da nusaiba Koda aka tambayesu Sai kuka suke su kansu basusan Ina Ina zasuce takeba mande direba kuwa kusan hankalinsa yafi na kowa tashi musamman dasu Yusuf sukace ga hukuma zasu miqasa matuqar ba'a gantaba ko Kuma wani Abu ya sameta.

Inna data fito 'daki sanye da hijabin datayi sallah dashi ta gaida baffan bai amsa mataba sbd takaicinta dayakeji na yanda take qoqarin nuna ko inkula kan 6atan na Anano Wai ita kawaici,
  kicin ta nufa tafara qoqarin hura wuta.

Harara baffa yabita da ita Rai a tsananin 6ace cikin hasala yakira sunanta ta qaraso gabansa daidai Nan idonta ya sauka kan Anano dake tsaye qofar shigowa.

Jafar ne yafara ganinta bayan inna yayi saurin miqewa cikin farin ciki tareda hamdala yakira sunanta da 'dan qarfi.

Da sauri baffa ya juya batareda ya balbale Inna da fadan da yayi niyya ba ya miqe Yana cewa,

Alhamdulillah ya Allah,,,,

Qarasa shigowa cikin tsakar gidan tayi ahankali qafafuwanta na hardewa kamar Wadda kwai ya fashewa aciki tazo gaban baffa ta tsaya tareda sunkuyar da kanta qasa sabbin hawayen fargaba da tsoro na gangaro Mata.

Cikin tsananin kulawa da farin ciki baffa ya riqo hannunta 'daya ya nufi tabarmar daya taso Yana cewa,

Ananon baffa me.....

Cak ya tsaya Jin Bata motsa daga inda takeba yayi saurin juyowa Sai alokacin ya lura da Inna da aliyu dasuka kasa motsi sun qurawa ananon Ido cikin wani irin yanayi
Maida kallonsa yayi ga ananon saiyaga tuni sautin kukanta yafara fita ahankali.

Sakin hannunta yayi tareda fuskantarta cikin  damuwa da kulawa zaiyi magana idonsa ya lurada  abinda ke hannunta dunqule cikin farin hijab 'dinta.

Kallonta yafarayi tun daga samanta zuwa qasa,
Gabaki 'daya jini ne a uniform dinta ga fuskarta datai jajir ta kumbura...

Daqyar ya tattaro yawu ya ha'diye suka wuce maqoshinsa daqyar kamar zasu yankesa yakalli ananon cikin son yaqar wani tunanin dakeson shigarsa idonsa qyar akan hannuwanta yace,

Ananon baffa meya sameki Kuma menene wannan a hannunki?

Inna da tuni tafara mantawa da kawaici cikin tsananin fargaba ta matso tareda Kai hannunta dake rawa zata bu'de baffa yayi saurin riqe hannunta still idanuwansa nakan Anano yace,

Anano meya sameki?
Kafadamin idan ba wanine yayi Miki mummunan illa ba....

Kuka tasake fashewa dashi Mai qarfi daidai shigowarsu Yusuf suka qaraso da sauri saidai suna qarewa kayan jikin Anano kallo gabansu yayi mummunan fa'duwa sbd sun saddaqarda fyade akayiwa 'yar qanwar tasu
Bango Yusuf ya dafe Yana karanto innalillahi cikin tsananin tashin hankali.

Usman ma cikin tashin hankalin ya sulale qasa zaune jafar dayake da tsananin sanyi da karyayiyar zuciya tuni yafara hawayen tausayin 'yar qanwarsu da aka 6atawa rayuwa aliyu kuwa baffa yayi saurin riqewa ganin zai iya zubewa qasa sbd halinda yashiga.

Cikin zafin nama da takaici inna ta fuzge hijabin Saida jaririn yakusa fa'duwa cikin wani mugun sauri Anano tayi saurin zubewa qasa ta taresa tareda qanqamesa da sauri jikinta na rawa shikuwa jaririn Sai alokacin yasaki wani irin kukan jarirai Wanda tunda yafado Sai alokacin yayi kuka.

Yusuf,Usman,aliyu da baffa kusan dukaninsu atare suka zabura sunakai kallonsu ga jaririn Dan sai alokacin suka sanda akwai wani Abu acikin hijabin Anano din.

Inna ma ta razana matuqa da ganin jaririn duk da dama tayi zargin akwai wani Abu a hijabin Amma Bata ta6a kawo zataga jariri ba.

Qurawa yaron idanuwa sukayi cikin tsananin fargaba jafar kuwa jiki na rawa haryana tuntu6e yayi saurin Isa qofar gidan ya rufe harda maqala sakata Dan karma ajiyosu ko wani yashigo gidan.

Cikin rawar hannu baffa ya nuna jaririn Yana kallon usman dake kusa dashi yace,

Usman dubamin meye wannan kamar jariri nake gani....

Jiki a mace usamn yayi qasa da kai murya a sanyaye yace,

Baffa jariri ne a hannunta Kuma me Rai ba matacceba sabuwar haihuwa ma.

Anano''''' Baffa yakira sunanta cikin kammalalliyar murya.

Kasa 'dagowa tayi saima wani kukan data fashe dashi.

Sake Kiran sunanta baffa yayi ta rintse kumburarun idanuwanta da sukaci kuka harsuka gaji ta girgixa Kanta da yayi mugun nauyi sbd kukan datasha dakuma ciwon dayake Mata ta bu'de baki daqyar murya a dashe tace,

Baffa Dan Allah kayi hkr wlh ba abinda kuke tuna.....

Aliyu da tuni zuciyarsa tafara tafarfasa ya wurga Mata wani mugun kallo da jajayen idanuwansa a hasale yace,

Kifadi abinda ke hannunki na waye aka tambaya ba tareda 6ata Mana lokaciba.

Yawun tashin hankali da tsoro ta ha'diye tareda sunkuyar da Kai tace,

Nawane Amma bani....

Wani gigitaccen mari Inna ta saukar Mata tana 'dauke hannu aliyu ya sauke Mata nasa harsaida tayi zaman Yan bori.

Cikin tsananin hasala da zafin zuciya Yusuf ya karbi zancen Yana watsa Mata wani mugun kallo yace,

Dan ubanki Zaki bu'de baki kifa'da Mana 'dan uban waye ahannunki kosaina karya Miki wuya..

Kuka tasake saki tareda qara qanqame 'dan ta rarrafa gaban baffa da tuni jiri yakusa zubar dashi Saida jafar ya taresa ta riqe qafarsa da hannu 'daya cikin hawaye tace,

Baffa Dan Allah ka....

Hannu baffan ya'daga Mata daqyar Dan tuni bakinsa ya mutu Dan har wani rawa yaji zuciyarsa nayi sbd fargaba Dan har lokacin yakasa yarda da abinda ke Shirin tabbatuwa agabansa ya kalleta kalar tausayi murya a sanyaye yace,

Hassana..,

Rintse idanuwanta tayi zuciyarta na Kara karyewa Jin yau yakirata da ainihin sunanta.

Anano wannan yaron na hannunki nakeson kifadamin na waye dan ayi gaggawar mayar dashi tun kafin afara shigowa yi Mana barkar dawowarki agansa ayi Mana wani tunani Dan haka kiyi gaggawar fadar inda kika tsintoshi a mayar dashi Dan wallahi bazai zauna a gidan Nan ba...

A gigice ta 'dago hankalinta na tsananta tashi tuni idanuwanta suka qafe jikinta ya'dau sabuwar rawa.

Wata razananniyar tsawa dabai ta6ayi arayuwarsaba yayi Mata cikin qufula yace,

Ki bude baki kiyi magana.

Rawar jikinta ce ta qaru sbd baffa da tuni tsananin 6acin ransa ya bayyana

Kallon Yusuf baffa yayi Rai a6ace yace,

Kar6esa ka....

Cikin tsananin kuka ta qara qanqamesa tace,

Baffa dan Allah karka rabani dashi bazan iya rabuwa dashiba.....

Duka Inna da aliyu suka rufeta dashi lokaci guda Nan ta sake qanqame 'dan sbd Kar duka ya samesa abinda ya qara hasala kowa kenan Inna ta jawo icce tana cewa,

Gwarama mu kasheki cikin gida tun kafin ma wani yasanda abinda ke faruwa.

Riqe iccen Yusuf yayi yana kallon ananon yace,

'dan uban waye akace?

Ha'diye sabon kukan dayazo mata  tayi Kai tsaye tace,

Nawa ne.

Fixgota Inna tayi  tajata ta jefa 'daki batai wata wataba ta zare wandon makarantar dake jikinta wani razanannen salati tasaki tayi baya tana Kiran sunayen Allah jikinta tuni yayi sanyi yanxu Kam kukane ke Shirin qwace Mata ta fito kallo 'daya tayiwa baffa saita sauke Kai hawayen datake dannewa suka gangaro

Zuciya baffa ya dafe Sai kawai sukaga yayi baya ya zube Yana wata irin jijjiga jafar da Usman sukai kansa Yusuf kuwa waje ya nufa da sauri Dan Kiran mande direba sukai baffan qauyen gabansu wurin sani Mai chemist Dan su shine likitansu.

Aliyu kuwa dakin da anonon take tana fidda kuka Mara sauti hakama yaron tuni ya kara'de gidan da kuka ya nufa a zuciye yahau jibgarta baji ba gani Inna ma zubewa tayi qofar 'dakin tana hawaye cikin mummunan tashin hankali da sanyin jiki.

# vote
# comment
# share
Post a Comment (0)