Eznah 20

*_EZNAH_*🌹
         _wattpad@mamuhgee_

*20*
Zama gwaggo tayi bayan fitar kamalu taga ananon tabi bayansa da wani mugun kallo tace,

Anano....

Na'am'''tace tana goge fuskarta inda Kamal ya taba cikin qunar Rai sbd jitake kamar tafasasshen barkono ne yata6ata.
Miqewa tsaye tayi ta nufi hanyar toilet din dakin tashige danta wanke fuskarta Kota rage zafin da zuciyarta ke Mata akanta.

Tana fitowa Zama tayi a kujera tareda dibar abincin da gwaggo takawo tea ne Sai kwai soyayye da bread

Saidata bawa abdulshakur yaci ya qoshi kafin taci itama ta kimtsa Abdul din kafin ta tattara kayan ta kar6i kudi gurin gwaggo ta fito tayo gida dantai wanka ta canza Kaya.

Kodata isa gida saidatayi wanka ta shirya kafin ta nufi sashensu mum asee,

Zaune take a Palo yakurah da Kamal na zaune tareda ita suna magana.

Kallon Kamal mum asee tayi tace,

Alhaji yaje kar6o takardu wani guri Dan anjima zasui magana da saheeb Dan haka nasa su bullet su taresa a hanya su kar6emin takardun shikuma sukaisa gidansu dake can daji su rufemin shi cikin rizabuwar gidan harsai nagama hada takardun.....

Katseta Kamal yayi yace,

Mum bana tunanin wannan shawarar tayi sbd zai iya guduwa and wat do you think will happen idan yayi escaping bastard son dinsa yasan komai,,,,no I can't imagine spending the rest of my precious life in any army prison.....

Shut up stupid""""mum asee ta katsesa cikin takaicinsa he always think or say negative.

Ni kullum qarin baqin cikina akan saheeb shine yanda na haifi Mai tosashen Kai shikuma ya kasance Mai komai na yaron arziqi....

Tsuke fuska yayi sbd takaicin yanda kullum Sai mum takirasa da wani mugun suna.

Daria yakurah ta qunshe cikin ranta tace,

Slowly dai you two will become enemies and I will be morethan happy to see that.

Banda shegen rawar kanka daba yanxu Kaine Mai kulada dukiyar saheeb dinva tunda baida Mai kular Masa Amma ka kasa nutsuwa duk wani mugun halin dabbancinka na neman Mata yasani...

Idan mukai Masa allurar yanxu uban waye zaisaka Mana hannu a sauran takardun kumama me kake tunani?
Shi saheeb din Wawa ne kamarka dabazai kaisa asibiti abincika agano allura akai masaba.....

Mum please ya Isa nagaji da yanda kike insulting Dina ko yaushe akan wannan gud for nothing bastard step son din naki,
Idan kinsan ya fini maiyasa tun farko baki za6esaba akaina mitswww...

Miqewa yayi ya wuce a fusace Yana cewa,
I just hate that bastard like hell....

Karo yaji yayi da mutum da sauri taja baya jikinta na'dan rawa ganin irin kallon dayake Mata na zargin taji Mai suke fa'da saitayi saurin tattaro nutsuwa da murmushin yaqe tace,

Inazaka kake sauri haka?

Qura Mata ido yayi batareda ya amsaba yanason karanto yanayinta sbd yaga rudewa atareda ita.

Ganin zai iya ganota yasa tasake washe Masa baki tana cewa,

Lafiya naganka haka?
Mum asee nanan kuwa?
Inason nagaisheta ne kafin nakoma asibiti.

Jin takira mum asee yayi tsaki tareda cewa,
Just get out of my way stupid.

Matsawa tayi ya wuce kamar zai tashi sama.

Ajiyar zuciya tasake tareda binsa da harara tana cewa,

Idiot'""""Nima na Rama mitswww.

Kodata shiga sama sama tagaida mum asee ta fito ta tafiyarta asibiti tana cewa,

Ni da abdulshakur ma yaji sauqi tattarawa zamuyi mu tafiyarmu inda mukafi wayo Dan wlh Zama anan cikin makasa gangancine.

Tana Isa asibitin takasa samun sukuni sbd hakanan taji hankalinta yatashi da abinda za'ayiwa Abba Amma Kuma batasan ya zatayi ba.

Har kusan maraice tana zaune takasa sukuni Sai Kai kawo take ta rasa mafita.

Kamar daga sama saiga zayyan da saheeb sun shigo saheeb fuskarnan a 'daure ko kallon gefenta baiyiba ya gaida Inna kamar bakinsa na ciwo.

Zayyan kuwa tsokanarta ya'danyi saiyaga idanuwanta na zubda hawaye cikin kulawa yace,

Subhanallah maman abdul lafiya kuwa Naga kina hawaye.

Juyowa gwaggo tayi cikin mamaki ta kalleta tace,

Ke lafiyarki kuwa ni tunda kikaje gida Kika dawo Naga kin canza.

Sake matso hawaye tayi gabanta na luguden tsoron qaryar dazata lafto Dan kuwa tunda akace tana kuka taga ya watso Mata shanyayun idanuwansa ya kafeta dasu.

Sosai zayyan ya damu yasake tambayarta taqi magana saima sautin kukan data fara fitarwa 
Juyawa saheeb yayi zai fice Dan ya tsani kayan takaici
Ganin zai fice tayi saurin bu'de Baki da 'daga murya tace,

Dazan dawo asibiti dazu nataho ta gurin layi na hudu bayan na gida Naga kamar motar abban Kamal agurin wasu na qoqarin fitoda Abu direbansa suna qoqarin cusashi cikin wata mota kum......

Wat"""Taji yafada da qarfi tareda juyowa ya zuba Mata idanuwansa 
Rawa jikinta ya 'dauka ta ha'diye yawu da qyar sbd tsoro Dan tasan ba baffa ka'dai zataciba idan yagano qarya take har innarta saitaci itadai fatarta yayi saurin xuwa gurin da yaransa kafin Abba yabi gurin a daukesa.

Zaro idanuwa gwaggo tayi cikin salati tace,

Anano gskia kike fada kuwa kokuwa iskancin nakine ya mots....

Katse gwaggo tayi da sauri ganin zata 6allo Mata ruwa tasake sakin sabon kuka tana cewa,

Da gske nake nagani da idona.

Juyawa yayi yabar 'dakin Yana Ciro wayarsa yakira office dinsa yabada umarnin motar soldiers biyar tazo ta samesa yanxu.

Kallonta zayyan yayi yace,

Just calm yourself and stop crying Bari muje mugani and I pray ba qarya idonki ya gane Miki ba...

Waro idanuwanta tayi akansa tareda qara ha'diye wani yawun tsoro kafin ta sunkuyar da kanta kukan gaske na zuwar Mata na tsoro Dan matuqar plan dinta baiciba ta ka'de.

Tunda suka fita takasa zaune takasa tsaye sai rawar qafa takeyi 
Gwaggo Sai binta da Ido take cikin tsananin mamakin ikon Allah kafin takasa hakuri tace,

Wallahi wannan zazzaro idanuwan da kike bakida gskia Dan haka tun wuri ki sanardani meke faruwa.

Kallon gwaggon tayi cikin sauri da tsoronta dayake qara bayyana tace,

Gwaggo nikawai ki tashi muje gida mu tattara kayanmu mu koma gurinsu baffa nidai nagaji da Nan 'din gaba 'daya.

Qura Mata ido gwaggo tayi har wani ciki ciki take da Ido sbd tasamu karanto ananon tsaf Dan duk rashin gaskiya ya bayyana atattareda ita

Tasan halin ananon tsaf da rashin ji da gajen hakuri ga shegen wuce wuri Amma tayi tunanin duk ta daina sbd wannan halinda tashiga na samuwar abdulshakur Amma ga alamu Nan sun nuna wani gagarumin abun tayi.

Qyaci tayi tace,

Idanma baki fadaminba duk abin yabiyo baya ai naji Kuma idan ma wata maganar Kika jawo wlh daukarki zanyi muje nakaiki har qauye aliyu ya laka'da Miki mugun duka mudawo.

Itadai shiru tayi tana danasanin shiga abinda bai shafetaba Dan yanxu batasan ya zata Kaya mataba.

Tunda Abba yafito office suka kamo hanyar gida yaga wata baqar mota nabinsu abaya da farko baiyi tunanin su motar kebiba saidayace Abu driver yayi parking bakin titi saiyaga Suma sun tsaya nesa ka'dan.

Cigaba sukayi da tafiya motarma tabiyosu cikin mamaki yace,

Abu ka lurada motar bayanmu mu takebi kuwa?

Kallon mirror Abu yayi yace,

Alhaji tunda muka fito office take biyedamu banfada maka bane Dan Kar hankalinka ya tashi.

Wat to ai hankalina Kam yagama tashi Dan kuwa ba tantama kidnappers ne.

Qarawa motar gudu Abu yayi cikin rawar jiki Jin abban yakira kidnappers hankali tashe Dan kuwa gani yake gara alhajin daukarsa kawai zasuyi shikuwa shegen duka zasuyi Masa subarsa kwance qilama Sai anmasa sakiya kozai dawo daidai.

Atake Suma su bullet suka qarawa motarsu gudu
Aikuwa Abu naganin haka hankalinsa yaqara mugun tashi ya Kuma bawa motar wuta jikinsa na rawa musamman ma dayaga Abba hankalinsa yayi mugun tashi ga tsoro qarara ataredashi
suna shiga layin farko na anguwar motocin soldiers din saheeb na shigowa Aida wani mugun ribas motarsu bullet suka bar layin motar sojojin na Mara musu baya Amma Basu samesuba haka suka dawo.

Abu na ganin motocinsu saheeb yayi wani mugun parking a tsakiyar layi ko motar Bai tsaya kashewaba dashi da abban sukai rige rigen fita motar Dan hankalinsu ba qaramin tashi yayiba.

Abu cikin sojojin yayi a guje jikinsa ba inda baya rawa Dan duniya Allah yayisa da shegen tsoro musamman ma na 6arayi Dan tsaf zasu yankaka kosu harbeka.

Abba motar saheeb daya fito cikin tashin hankali ya nufa Yana zare babbar rigarsa Dan wani mugun zafi yakeji.

Bu'de Masa mota saheeb yayi yashiga ya rufe Masa ya juyo ya kalli yaransa ya Basu umarni kafin ya kalli Abu dake zare idanuwa jikinsa baibar rawaba yace,

Kashiga motar kaja ka qarasa gida da ita...

Zaro idanuwa yayi zaiyi magana wani soldier ya daka Masa wata gigitacciyar tsawar data sashi nufar motar haryana tuntu6e jikinsa na qara karbar rawa.

Shigewa motocinsu sukai sukabar gurin abu ma a mugun gujen ya Mara musu baya Yana kallon bayansa ta cikin mirror.

# vote
# comment
# Share


Post a Comment (0)