✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴
ABOKIN FIRA
*Masu Hikima Sun ce*
An halicci Jaki sai aka ce masa za ka je duniya ka yi shekaru arba’in.
Sai ya ce, idan na je me zan yi? Aka ce masa za ka yi ta aiki tukuru tana daukar kaya. Sai ya ce, a rage masa, arba’in sun yi masa yawa.
Sai aka ba shi ashirin. Aka halicci Kare aka ba shi shekaru arba’in. Ya
ce, duk me zan yi da su? Aka ce, za ka yi ta guje guje yara suna korar ka, kana haushi a kan su. Sai ya ce, a rage masa sun yi yawa. Aka ba
shi ashirin. Sannan aka halicci Biri aka ba shi arba’in. Da ya tambaya sai aka ce ma sa, zaka je duniya ne ka yi ta tsalle tsalle a kan itatuwa.
Shi ma ya nemi a rage masa ashirin. To, daga nan aka halicci Mutum aka ba shi shekaru arba’in. Sai nan take ya ce sun yi masa kadan. Ya
roka a hada masa wadancan shekarun da aka rage ma wadancan dabbobi.
Don haka ne Mutum yake rayuwa shekaru arba’in a matsayin Mutum, sannan ya dawo ya yi shekaru ashirin na Jaki yana ta wahalar rayuwa
da neman abinci ma iyalinsa. Bayan su kuma ya yi na Kare bayan ya yi ritaya yana ta fada da ‘ya’yansa. Sannan ya yi ashirin na Biri yana
tsalle tsalle a cikin jikokinsa.