HUKUNCIN SHAN RUBUTU

TAMBAYA
=========
👇
Asalamu alaikum malam Dan Allah meye hukuncin shan rubutu

AMSA
=====
👇
Akwai Ra'ayin malamai dangane da wannan mas'alar, Wasu malaman suna ganin idan zallar Alqur'ani aka rubuta, matukar dai ba'ayi wani soke-soke ba, babu wani abu.
  Amma wasu malaman suna ganin tinda manzon Alkah saw baisha ba, ba'a samu wani sahabi ya sha ba, kamar idan aka budewa mutane wannan kofar zasu halaka su halakar da wasu, domin wasu sai sun wuce gona da iri. Sabida ba mamaki suna yin wani abun da zasu fake da wannan halatta shan rubutun su halaka su halakar. Wanda wannan shi ake cewa.
  Wato wannan shima wani Babi ne guda a ilimin Usuul da ake cewa SADDUZZARI'AH, Kautar da wani Abu koda kuwa halattacce ne, sabida kar mutane su fada kuskure.
Domin akwai batattun malamai suna yin rubutun Alqur'ani da jinin haila sabida yiwa mata sihitri akan mazajensu ko wani abin da yayi kama da haka.

Allah shine masani


ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Post a Comment (0)