WACCE MIJIN TA YAKE SAURIN INZALI

*TAMBAYA: - Wacce mijinta yake saurin inzali kafin buqatarta ta biya mai yakamata suyi don maganin matsalar.*

AMSA: - Gaskiya wannan ba qaramar matsala ba ce domin kuwa ita take sa rashin zaman lafiya a tsakani yawanci ma'aurata kuma akwai cutarwa mai yawa kususan ga matar, domin ita mace akwai wani ruwa da ke fesowa a gabanta kafin tayi inzali shi kuma wannan rowan asit ne domin zafi ne da shi idan tayi inzali wannan rowan maniyi shin e yake sanyaya shi to idan har ba tai inzali ba wannan rowan zai sabbaba mata ciwon mara da tsatstsagewarta da matsala a farjinta, kuma zai sa ta tsani miji, don haka Manzon Allah (SAW) ya ce:- "Idan xayanku ya sadu da matarsa to kada ya tashi har sai ta biya buqatarta kamar yadda yake so ya biya buqatar sa".

Abin da akafi so ga kowanne miji da mata kowanne yayi iya yinsa don ya gamsar da xan uwansa, ba wai kowa ya dinga qoqarin biyawa kansa buqataba wanna shi ne abinda yake haifar da matsalar.

Mafita shi ne, a biyo hanyoyi da muka yi bayani a baya kafin jima'i wato xan saqo kamar yadda Manzon Allah yayi bayani.

(abu na biyu) kasancewar sha'awar mace tana kaiwa minti goma 10 ta namiji minti biyar 5 to sai ya sami kanwa ya sa a bakinsa ya dinga tsotsa kamar alawa a lokacin jima'in wannan zai sa sha'awarsa shima takai har minti goman 10 ta inda zasu yi dai dai idan aka yi haka za'a sami mafita.

*TAMBAYA: - Tazarar kwana nawa yakamata a dinga samu kafin saduwa don kolawa da lafiya.*

AMSA: - Ya danganta da lafiyar mutum da kuma qarfin sha'awarsa da irin abincin da yake ci amma ba a so mutum yayi jima'i sau biyu a rana domin hakan zai cutar da lafiyarsa kuma indai ka fiya yawan jima'i to zaka tsufa da wuri.

*☞ SHARE DON MU KARU DA JUNA*

Copyright BY: Sirrin rike miji
FACEBOOK GROUP: sirrin rike miji

FACEBOOK PAGE LIKE: sirrin rike miji
WhatsApp: ☏+2348141712330

Post a Comment (0)