JINI YANA ZUWA MIN A YAYYANKE!!

JINI YANA ZUWA MIN A YAYYANKE!!


                          *Tambaya*
Assalamu Alaiykum, Malam matata ta haihu sati biyu kenan, to Malam yanzu takan wuni Jini bai zoba sai da Daddare in ta kwanta sai Jinin yazo. To shin Malam za ta iya yin wanka/tsarki da safe tayi sallolin Azahar zuwa Isha'i? Kokuma yaya zatayi? Nagode Allah Yaqara illimi mai albarka.


                             *Amsa:*
To dan'uwa a zance mafi inganci duk yinin da ta ga jini to yana daukar hukuncin jinin biki ne, haka ma tsarki yana daukar hukunce-hukuncen tsarki, ta yadda za ta yi wanka duk yinin da ba ta ga jini ba, Saidai idan yana yayyankewa kusa-kusa, to tana iya jinkirta wankan, sai ta hada sallolin da ba ta ga jini ba a lokutansu, saboda yin wanka a kowanne lokaci akwai wahala a ciki, kuma Allah yana cewa: "Bai sanya muku kunci a cikin addini ba" Suratu Hajj 78.

Allah ne mafi sani.

Don neman Karin bayani duba Almugni na Ibnu Khudaamah 1\214.

22\2\2015

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_____________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

 ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.
Post a Comment (0)