MACEN DA MIJINTA YA MUTU DA SATI ƊAYA BAYAN YA SAKE TA ZATA YI TAKABA?

Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu, 

Tambaya

Idan Mijinka yasakeka da sati 1:kuma yarasu, to yahalatta tayimishi takaba ko baki halattaba????

*Amsa:*

_Wa'alaikumussalam Warahmatullah wabarakatuhu._

_Idan ya kasance saki ɗayane ko biyu, wato sakin da akwai damar yin kome a cikinsa, to za ta dawo ne ta yi masa takaba tunda ba ta gama iddarta ba. Amma idan saki ne wanda babu kome a cikinsa, to a wannan halin ba za ta yi masa takaba ba tunda ta tashi daga matsayin matarsa._

_Matuƙar mutun ya rabu da mai ɗakinshi da saki ɗaya ko biyu, sannan ya rasu kafin ta kammala iddar saki, shikenan sai ta koma takaba, matarshi ce yana da dama ya dawo da ita a ko yaushe muddin bata kammala idda ba_ .
.
Wallahu A'lamu.
.

Daga Zauren:
*🕌ISLAMIC POST WHATSAPP.*

_Ku turo da cikakken suna da address zuwa wannan number *08166650256* a WhatsApp don shiga group dinmu._

Post a Comment (0)