MENENE HUKUNCIN MATAR DA JININ AL'ADA KO JININ BIKI YA DAUKE MATA KO WANKAN JANABA YA SAMETA KAFIN KETOWAR ALFIJIR, ZATA IYA DAUKAR AZUMI KO KUWA???

MENENE HUKUNCIN MATAR DA JININ AL'ADA KO JININ BIKI YA DAUKE MATA KO WANKAN JANABA YA SAMETA KAFIN KETOWAR ALFIJIR, ZATA IYA DAUKAR AZUMI KO KUWA???


                                 *Tambaya:*
Minene Hukuncin Matar da Jinin Al'ada ko Jinin Biki yadauke mata ko wankan Janaba ya sameta kafin ketowar Alfijir, zata iya daukar Azumi ko kuwa???


                                      *Amsa*
Zata tashi da azumi, daga baya sai tayi wanka. Saboda hadisi ya tabbata daga nana Aisha (R.A) tace:‎ "Manzon Allah (S.A.W) yakan wayi gari da janaba a jikinsa a sababin jima'I da yayi, ba mafarki ba a cikin ramadhan, kuma sai yaci gaba dayin‎ a zuminsa.

Ma'ana zai iya samun janaba da dare, ya wayi gari da ita kuma yaci gaba da azuminsa babu komai".

Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

 ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.


Post a Comment (0)