Eznah 19

*_EZNAH_*🌹
         _wattpad@mamuhgee_




*19*
'dakin asabe ta fa'da Kai tsaye ta shige toilet ta rufo qofar tareda jingina jikin kofa tana sauke numfashi da qarfi.

Yawu ta ha'diye daqyar akaro na ba adadi kafin tafara tattaro 'yar nutsuwa ta cusawa kanta...

Jikinta tafara 'daurayewa kafin ta fito ta zauna bakin gadon asabe tana tunani.

Meyene manufar Kamal akanta da 'danta dayake fa'da?
Dama tun farko ba son gskia yakeminba kenan,
Idan sunason su kashe saheeb Dan suci dukiyarsa to ita meyene nata da 'danta,,,,,
Tabbas idan sukasan naji Nima kasheni zasuyi kamar yanda sukace sun kashe maman saheeb ta hanyar Bata guba da Mai aikin gidan itama ta hanyar ka'deta hakama matar gidan sun kaita daji sun kasheta........

Miqewa tsaye tayi gabanta yayi muguwar yankewa sbd wani irin tunani daya shiga zuciyarta..

Fitowa tayi jikinta na qara karbar rawa tabi ta qofar kicin tabar sashen ta Isa gurin gwaggo gabanta na tsananta fa'duwa.

Tattaro 'yar nutsuwa tayi Dan tanason ta fahimci amsar tambayar dazatayi wa gwaggon.

A darare ta zauna tareda bawa gwaggon baya Dan batason ta fahimci halinda take ciki murya a sarqe tace,

Gwaggo..

Abinci gwggo kebawa abdulshakur batareda ta juyoba tace,

Ya akayi?
Kun sake fa'dan ne keda kamalu tunda ke bakida aiki Sai saiyiwa wahalalliyar soyayya kuka.

Batama damu da abinda gwaggon taceba tace,

Yaushene matar gidannan ta rasu?

Watanni bakwai kenan yanxu.

Mummunan bugawa gabanta yasakeyi sbd watanni bakwai kenan da faruwar komai na haihuwar abdulshakur.
Meyene sunan saheeb na gaskiya?

Abdulshakur..... gwaggo tabata amsa Kai tsaye..

Yani irin yawu ta ha'diye tareda miqewa tana girgixa Kai Dan Sam Bata fatar banxan tunaninta yazamo gskia sbd ganin irin mugayen mutane marasa imani dasuke shirye da kawar da kowa akan abun duniya takosan abdulshakur dinta Dan qaramin alhakine gurin kashewa.

Daki ta shige da sauri tareda kawar da tunin cikin ranta Dan batamason yinsa.

Kaya ta canxa ta fito tareda 'daukar abdulshakur suka fito ta kar6i kudi gurin gwaggo suka fito siyan pad.

A layin bayansu taje siyan pad din sbd can ne kawai da shago tasiyo sun juyo kenan motar sojojin saheeb ta shigo layin da mugun gudu kafin ta Ankara sunyi sama da ita.

Abdulshakur dake hannunta saidayayi sama ya daki saman motar kafin ya fa'do qasa cikin jini.

Qara ta qwalla ganin ko numfashi bayayi duk da itama taji ciwo a hannu da gefen fuska haka ta miqe jikinta na rawa tayo kansa tana Kiran sunansa da qarfi.

Rintse idanu yayi cikin wani irin yanayi kafin ya fito motar sbd shine yake tuqi da kansa Sai  zayyan dake gefensa tukuna motar sojojinsa a bayansu.

Zayyan ma fitowa yayi ya qarasa gabanta da sauri tareda durqusawa yana ganin halinda yaron ke ciki ya 'dago da sauri yakalli saheeb dayake tsaye yace,

We need to take him to hospital now...

Tanajin haka ta miqe da sauri tana qoqarin 'daukarsa Amma batasan sanda tasaki qaraba tareda sabbin hawaye sbd azabar dataji ahannunta.

Jawota taji anyi da qarfi tareda juyo da ita taga kamal,

Cikin hasala yace,
So nawa Zan fa'da Miki ki daina fita da wannan bastard son din naki sbd badluck ne agareki Amma kinqi
Gashi kin karya hannunki sbd shi and still kinason 'daukarsa sbd hannun ya qarasa karyewa let me tell you something karkiga Ina sonki duk da nasan kin haifi shege kiyi tunanin idan kin karye ko kin nakasa Zan cigaba da sonki sbd Sam bazan yarda ki 6atamin shirina.....

Fixgewa tayi da qarfi hawaye na ciko idanunta sbd baqin ciki da kunya daya sata Dan kuwa tuni zayyan ya waro idanuwansa Yana sake kallonta Jin ankira abdulshakur da 'danta shege Mara uba.

Saheeb kallo 'daya yama yaransa suka koma mota da gudu suna sorry sir yashige motarsa tareda janta cikin wani mugun speed yabar gurin motar sojojin ta Mara Masa baya Dan idan da akwai abinda yafi tsana da qyama to zinace saigashi wannan yarinyar Ashe bayan ganin dayake yimata da Kamal cikin wani irin yanayi har lasisin iskanci ne da ita tunda ta haife shaida....wata tsanar yarinyar da qyamarta yaji tana shigarsa harma da 'dan yaja qaramin tsaki Dan kuwa badan yana ganin qimar gwaggo ba da har ita har shegen 'danta bazasu qara kwana cikin gidanba.

Hawayen dasuka gangaro matane yasa Kamal Jan tsaki tareda riqo hannunta ta qwace zatabar gurin taga zayyan daukeda abdulshakur cikin sanyi yace Mata,

Muje akaisa asibitin.

A Motar Kamal suka nufi asibitin zuciyarta Sai tsananin quna take da abinda Kamal yayi Mata Kuma ga halinda Abdul 'dinta yake ciki.

Suna Isa akai gaggawar kar6arsa emergency itama daqyar ta yarda Kamal yakaita akai dressing din hannunta tareda gefen fuskarta da aka shafa mata ointment.

Ganin yanda ranta yayi tsananin 6acine yasa yafara lallashinta Yana Bata hkr Dan wani 6angare na zuciyarsa na tsananin sonta Amma burinsa nason dukiyane yake danne hakan.

Kallonsa tayi idanuwanta na kawo hawaye zuciyarta na karyewa sbd maganar gaskiya har lokacin akwai sonsa maqale aranta saidai zata biyar dashi ta yanda yakeso harsaita gano manufarsa akanta.

Cikin sanyin murya tace,

Ya wuce Amma karka sake.

Murmushi yasaki tareda riqo hannunta Yana cewa,

Bazan sakeba my love.

Zame hannunta tayi tareda kallon gefenda zayyan yake zaune Yana waya.

Zayyan baibar asibitinba Saida aka gama komai aka kwantarda abdulshakur din a aminity,.

Magungunan da'aka rubuta dakomai ya biya kafin ya kalleta cikin sakewar fuska yace,

Tom Zan tafi tunda komai yafara daidaita zuwa gobe insha Allah zamu zo tareda saheeb saimu qara dubasa Allah ya basa lafiya yakuma tsare gaba.

Amin nagode....tafada cikin sanyin murya.

Kallon Kamal yayi yace,

Kamal kozaka saukeni gida tunda kaga yanda mukazo.

Kallonta Kamal yayi tareda sakar Mata murmushi yace,

Ok baby Zan dawo zuwa goben Nima ok?

Kai ta 'daga Masa ya wuce Yana murmushin mugunta itama binsa tayi da wani mugun kallo aranta tana cewa,

Zakai mamakin halinda zaka tsinci kanka kaida 'yar ta'addar uwarka ranar Dana gama sanin manufarku na  wargaza muku komai.

Koda Kamal ya sanarda gwaggo abinda yafaru hankali ya tashi da daddare haka ta shirya ta nufi babban  palon saheeb cikin sallama.

News yake kallo Amma Rabin hankalinsa nakan wayarsa da mum asee keta Kira.

Amsa sallamar yayi cikin maqoshi tareda yiwa gwaggon kallo 'daya ya 'dauke.

Cikin jimami tai Masa maganar tanason yasa akaita asibitin sbd Anano bazata iya da sha'anin yaro ita kadaiba musamman da akace taji rauni itama a hannu.

Tsuke fuska yayi batareda yakalli gwaggon ba yace,

Bazata iya 'dawainiyarsaba ta haifesa
Kije kiyi kwanciyarki idanma bazata iya 'dawainiyarsa da wahalarsaba ta koya yanxu ko ta nemi ubansa ta miqa masashi.

Kallonsa tayi taga yanda fuskarsa take a ha'de saita miqe takoma daki ta zauna cikeda tausayin ananon Dan kuwa tasan raguwa ce sosai ta wannan fannin.

Har dare yayi Anano bataga gwaggo ba hankalinta yaso tashi Amma ganin har lokacin abdulshakur bai farkaba saita maida hankalinta kansa har bacci ya dauketa a zaune.

Da safe gwaggo tayi musu abin Kari tasa a kwando ta shirya Dan niyarta Yana fita aiki tabi Kamal ta tafi asibitin.

Qarfe goma saura yafito cikin shirinsa na qananun Kaya black trouser da dark blue shirt Sai black shade na warby parker dayayi matuqar yiwa farar fuskarsa kyau ya nufi palon mum asee.

Tana ganinsa wani Abu ya danne numfashinta daqyar ta tattaro numfashinta tasakar Masa murmushi tana cewa,

Gud morning my son.

Morning mum''''yace Yana Zama kusada ita tareda gaida Abba daya shigo palon lokacin.

Kallonsa Abba yayi yace,

Anjima idan kadawo inason ganinka akan wasu takardu danakeson kasa hannu.

Ok insha Allah Zan dawo around 6.

Wani 'dadi mum asee taji Dan kuwa tasan yau Abba zai fito da duk takardun kadarorinsu kafin saheeb din yadawo abban ya tashi aiki ta 6oye takardun.

Miqewa yayi ya fice a bakin motarsa ya tararda gwaggo zayyan dayazo yasa ankirata.

Shiga yayi suka bar gidan Yana ganin sun 'dau hanyar asibitin ya qara tsuke fuska zaytan na luredashi yasaki murmushi kawai.

Sbd gwaggo ya fito motar suka shiga.

Zaune take bakin gadon da Abdul yake kwance Kamal na zaune gabanta Yana shafa Mata ointment a gefen fuskarta Sai murmushin yaudara take sakar Masa shikuwa ji yake kamar yacire Mata ciwon.

Ji sukai anbude qofa atare suka kalli qofar cikin idanuwansa idonta yafara sauka tayi saurin 'dauke Kai gabanta na fa'duwa da mugun kallon tsana da qyama dataga ya jefota dashi.

Kallon hannun Kamal dake fuskarta tayi tai saurin janyewa tareda miqewa tana gaida zayyan da gwaggo Dan shi ko fuskar gaidasa Bata ganiba Dan ba qaramar qyamarta ta hango a idanunsa ba.

Cikin sakewa zayyan ya matso Yana duba Abdul din daya tashi lokacin Yana cewa,

Lallai yaron Nan soldier ne Dan gashinan yatashi da qarfinsa.

Dariya gwaggo tayi tace,

Ina wani soja anan gashinan kwana daya duk yasa ananota ramewa qilama kwana tayi tana kuka.

Murmushi Anano tasaki tace,

Kai gwaggo duk ciwon Nan dayake ciki bazaki raga masaba jifa Yan.......

Ha'diye sauran maganar tayi sbd idanuwansu dasuka shiga cikin na juna taga yanda fuskarsa ke qara tsuke saita waske tareda miqewa tashige toilet kamar munafuka Dan dai itakam Sam Bata iya Zama indai Yana guri sbd zuciyarta ke bugawa da qarfi.

Shima juyawa yayi yabar 'dakin zuciyarsa takaicin zuwansa,,,,
Ko acikin marasa tarbiya da mutumci wannan uwarsu ce,,,
Hartanada bakin Kare 'dan shege agaban gwaggonta she's unbelievable......

Mota Yakoma saidata zayyan ya tsaya 6ata Masa lokaci kafin yafito suka tafi.



# vote
# comment
# share


Post a Comment (0)