TAMBAYA TA 345

Tambaya ta (345)
:
Shin ko ya halatta Mace ta dauki wani abu a dukiyar Mijinta tayi sadaka dashi ba tare da izininsa Mijinba??
:
Amsa
:
Dangane da hukuncin cewa Mace taɗauki wani abu daga cikin dukiyar Mijinta tayi tasarrufinta cikin wani aikin alkhairi kamar Sadaƙa, Kyauta, Taimakon Mabuƙaci, dadai sauransu, Malamai sukace hukuncin yin tasarrufi da dukiyar Mai-Gida ya kasune cikin halayene kamar guda uku:
:
→(1)--Hali na Ɗaya shine, idan ya kasance dama Miji yayiwa Matarsa izini abayyane cewa tayi tasarrafi acikin dukiyarsa gwargwadon yadda yadace, to anan babu wani Ishkali (Rikitarwa) acikinsa, danhaka kai tsaye ya halatta ta iyayin sadaka daga cikin dukiyarsa, domin Mαиzoи Aʟʟαн(ﷺ) Yace:
:
"لا يجوز لإمرأة عطية إلا بإذن زوجها"
MA'ANA:
Baya halatta ga Mace tayi kyauta (da dukiyar mijinta) Sai in da izinin Mijin nata:
:
→(2)--Hali na Biyu shine, ya kasance abayyane dama Miji ya hana Matarsa tayi tasarrufi acikin dukiyarsa, to shima wannan babu wani Ishkali (Rikitarwa) acikinsa gameda cewa kai tsaye haramunne Mace taɗauki wani abu acikin dukiyar Mijinta tayi Sadaƙa ko Kyauta dashi tunda ya hanata, saboda Aηηαвι(ﷺ) Yace:
:
"لا يحل مال إمرئ إلا بطيب نفسه"
MA'ANA:
Baya halatta (ayi tasarrufi da) dukiyar Mutum sai in da daɗin ransa (yardarsa):
:
→(3)--Hali na uku kuma shine, ya kasance abayyane Miji bai bawa Matarsa izinin tayi tasarrufi cikin dukiyarsa ba, haka kuma azahiri baifito fili ya hanata ba, wato shidai bai hana ba Sannan kuma baice ayiba, to dangane da wannan hali na uku sai Malamai sukayi Saɓani akansa,
:
Wani Sashe daga cikin Malamai sukauafi akan cewa ya halatta Mace tayi tasarrufi acikin dukiyar Mijinta, zata iya bada Sadaƙa ko Kyauta daga ciki gwargwadon abinda bazai zama ɓarna da dukiyarba ko ya tozartar da'ita, danhaka zatayine daidai gwargwadon (Urfi) bisaga yanayin yadda koda Mijinta yaji labari bazai damuba, Misali kamar idan yakasance abisa ga al'adar yanayin yadda akasaba gani a garinsu idan wani Almajiri ko Mabuƙaci yazo yana neman taimako galibi akan bashi daga ₦1,000 zuwa ƙasa da haka a Misali, to babu laifi tabayar da hakan, amma idan taɗauki ₦10,000 ko ₦100,000 tabayar ko shakka babu tawuce gona da iri, amma idan tayine daidai yadda yadace to shikenan babu laifi, saidai in dama tasan halayyar Mijinta Mutum ne da bayason atabamasa dukiya danhaka koda ta bayar idan yaji labari zai nuna damuwarsa, to anan haramunne Mace tadauki wani abu nasa komai kankantarsa tayi sadaka dashi, daga cikin Dalilan Malaman da sukace ya halatta Mace tayi tasarrufi batare da izinin Mijintaba sunkafa Hujja da wannan Hadisi na Mαиzoи Aʟʟαн(ﷺ) da yake cewa:
:
"إذا أطعمت المرأة من بيت زوجها غير مفسدة، كان لها أجرها وله مثله،"
:
"وفي رواية"
:
"كان لها مثل أجره، لها ما نوت حسنا، وللخازن مثل ذالك"
:
MA'ANA:
Idan Mace ta ciyar daga ɗakin (dukiyar) Mijinta batare da tayi ɓarnaba to tana da lada shima kuma yana da lada,
:
Awata ruwayar akace:
:
"Ta kasance tana da lada saboda kyakkyawar niyyarta, haka nan mai dukiyar shima yana lada misalin haka"
:
Saidai wasu daga cikin Malamai suntafine akan cewa idan yakasance Miji baifito fili yace tayiba haka kuma baifito fili ya hanataba, sukace to bai halatta ba ta dauka ta bayar dole sai in tanemi izininsa, idankuma tadauka to ta aikata haramun kuma sai tabiyashi aranar Kiyama, daga cikin Dalilansu sunkafa Hujja da wannan Hadisi na Aηηαвι(ﷺ) da yake cewa:
:
"لا تنفق إمرأة شيئا من بيت زوجها إلا بإذن زوجها، قيل يا رسول الله(ﷺ) ولا الطعام؟ قال ذاگ أفضل أموالنا"
MA'ANA:
Kada Mace taciyar da wani abu daga ɗakin (dukiya) Mijinta sai da izinin Mijinta, sai akace Ya Ma'aikin Aʟʟαн(ﷺ) koda abincine tabayar? Sai Yace to ai wannan (abincin) shine mafi falala acikin dukiyoyinmu,
:
Amma magana mafi rinjaye acikin zantukan da Malamai sukayi itace, idan yakasance Miji bai hanaba kuma baice ayiba, to ya halatta Mace tayi Sadaka da daidai gwargwadon abinda zuciya bazatayi ƙyashin abayar dashiba,
:
※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※
:
ωαηαη sнιηε gωαяgωαdoη ɗαη αвιηdα ιℓιмιη мυ dαкυмα вιηcιкεηмυ үαкαι zυωα gαяεsнι, dαηнαк

Post a Comment (0)