TAMBAYA TA 349

Tambaya ta (349)
:
Meye hukuncin azumin Mutumin da yayi Istimna'i da rana acikin Ramadan Shin azuminsa yana nan ko ya lalace??
:
Amsa:
:
Da farkodai yana dakyau musan cewa Istimna'i (Masturbation) wato Mutum yafitar da Maniyyinsa ta kowacce irin hanyane koda kuwa ba da hannunsa yayi amfaniba indai Sha'awace tasa yafitar dashi, to mafi yawa daga cikin Malamai Ahlul-Imi suntafi akan cewa aikata Istimna'i (Masturbation) haramunne Ƙaulan-Wahidan, to amma haramcin yinsa yafi ƙarfi dakuma tsanani idan yakasance acikin watan azumine akayi, amma dangane da abinda yashafi azumin wanda yayi Istima'i (Masturbation) da rana, mafi yawan Malamai cikinsu kuwa harda Mazahibul-Arba'a da'ake dasu, wato
:
→(1)--HANABILA,
→(2)--MALIKIYYA,
→(3)--SHAFI'IYYA,
→(4)--HANAFIYYA,
:
Duk suntafine akan cewa Istimna'i (Masturbation) yana lalata azumi, danhaka kenan duk wanda yayi Istimna'i, (Masturbation) ko yayi wasa da Matarsa, ko ya rungumeta ya Shash-Shafata, kokuma ya Sumbaceta (Kiss), kokuma ita Mace tayi wasa da Mijinta wanda har hakan yakai ga Mutum yafitar da Maniyyinsa Malamai sukace azuminsa ya lalace, danhaka wajibine yatuba zuwaga Aʟʟαн(ﷻ) sakamakon wannan Ɗanyen-Aiki da yayi, sannan kuma zaici gaba da kame bakin sane harzuwa faɗuwar rana, bayan Sallah kuma sai ya rama wannan azumin amma bazaiyi Kaffara ba, amma MALIKIYYA suntafine akan cewa wajibine Sai yayi Kaffara, Saidai Nassin Kaffara yazone akan wanda yayi Jima'i da Matarsa a watan Ramadan da rana koda kuwa bai kawo Maniyyiba Sai yayi Kaffara, amma Mazhabin ZAHIRIYYA suna ganin cewa wanda yayi Istimna'i ko yayi wasa da Matarsa har yakai ga yafitar da Maniyyi sukace azuminsa yana nan bai lalace ba, kamar yadda
Al-Imam-Ibn-Hazm-Azzahiriy yakawo acikin littafinsa
Al-Muhalla-Bil-Asar, sukace babu wani Dalili daga Al-Ƙur'ani ko Hadisi dayake nuna cewa azuminsa ya lalace, hakanan shima_
Shaikh-Nasiruddin-Albany akan haka yatafi kamar yadda yayi bayanin hakan acikin Littafin
(تمام المنة في التعليق على فقه السنة)
To Saidai kuma galibi mafi yawan Malamai suntafine akan cewa azuminsa ya lalace, sakamakon dogaro da sukayi akan waɗansu Dalilai kamar haka,
:
Abu nafarko Sukace Nassi ya tabbata daga Mαиzoи Aʟʟαн(ﷺ) acikin Hadisul-Ƙudsiy inda Aʟʟαн(ﷻ) Yake magana akan Mai-Azumi Yake cewa:
:
"يدع طعامه وشرابه وشهوته من أجلي"
MA'ANA:
(Bawa na) yakan bar abincinsa da abin shansa da sha'awarsa asaboda Ni:
:
Anan sai Malamai sukace yin Istimna'i Sha'awace, domin kuwa ko Shakka babu cewa Sha'awace takesa afitar da Maniyyi ta hanyar yin Istimna'i da gangan kokuma wasa tsakanin Ma'aurata, Sannan sukace Dalilinsu na cewa Istimna'i Sha'awace, saboda faɗin Aηηαвι(ﷺ) inda Yake cewa:
:
"وفي بضع أحدكم صدقة، قالوا يا رسول الله(ﷺ) أيأتي أحدنا شهوته ويكون له أجر؟....إلخ"
MA'ANA:
Acikin tsokar ɗayankuma akwai Sadaƙa, Sai (Sahabbai) sukace Ya Ma'aikin-Aʟʟαн(ﷺ) yanzu ɗayanmu yaje (yabiya buƙatar) Sha'awarsa kuma yakasance anbashi lada?…… hardai zuwa ƙarshen Hadisin
:
Danhaka magana mafi inganci itace, fitar da Maniyyi da gangan ta hanyar Istimna'i ko wasa da Mace yana lalata azumi, amma idan Maniyyi bai fitaba shikenan azuminsan yana nan lafiya ƙalau, akan haka mafi yawan Malamai na da can dakuma na yanzu suke bada Fatawa, kamar irin su:
:
Ibn-Baz,
Ibn-Usaimin,
Ibn-Taimiyya,
Fatawal-Lajnat,
:
Dadai sauransu:
:
※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※
ωαηαη sнιηε gωαяgωαdoη ɗαη αвιηdα ιʟιмιη мυ dαкυмα вιηcιкεηмυ үαкαι zυωα gαяεsнι, dαηнαкα ιdαη αηgα ωαηι кυsкυяε αcιкιη αвιηdα мυкα яυвυтα тo αηα'ιүα ғαɗαкαя dαмυ мυgүαяα, тαяεdα кαωo нυננα мαι ƙαяғι:
:
Doмυп пεмαп ƙαяıп вαчαпı sαı αdυвα шαɗαппαп ʟıтαттαғαı καмαя нακα:
↓↓↓
:
"بداية المجتهد" (1/382)
:
"المجموع للنووي" (6/349)
:
"المغني لإبن قدامة" (4/363)
:
"الإستذكار لإبن عبد البر" (3/296)
""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""
Daga Zaυren
Fιƙ-нυl-Iвadaт
""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""
→AMSAWA←
Mυѕтαρнα Uѕмαи
08032531505
""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""
Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾
:
https://m.facebook.com/f

Post a Comment (0)