ABDULKADIR SALADIN 20

20. ABDULKADIR SALADIN
Na Alhaji Nuhu Bamalli
www.bukarmada.wordpress.com
...
Amma ciwon da ya kama Mahadi, ba na wasa ba ne. Zazzabi ne mai zafin gasken gaske, ya kuwa yi masa mummunan kamu. ’Yanuwansa duka sun karai, sun fara fid da rai ga rayuwa tasa. Ubangidana, Halifa kuwa, shi na tabbata a karkashin ransa murna ya ke, ko da ya ke a fuska yana nuna matukar bakin ciki. Dare da rana yana tare da Mahadi a gadonsa na jiyya. Mu kuma yaransa sai mu zauna kofar gida zugudum, babu komawa gida. Muka dai tare a can.
A rana ta shida daga kama ciwon, da maraice, abin ya yi tsanani har bayan an kare salla aka ce jama’a su yi addu’a don a roka wa Mahadi lafiya. Sai ran nan ne kowa da kowa ya yarda lalle yana ciwo. Kashegari, aka ce bai san inda kansa ya ke ba, har ba ya sanin kowa. Aka hana kowa ya shiga daga Halifa. sai Ma’aji Ahmed Wad Sulaiman, sai Osman Wad Ahmed, wani shenun malami. Ana nan zaune shiru, sai aka ce Mahadi ya suma. Zuwa can ya farfado. Amma shi Mahadi ya san karshe ya zo. Sai ya yi wasiyya ya ce, “Annabi ya nada Abdullahi shi ne magajina, watau halifana. Da ni da shi duka daya ne. Wanda duk ke bi na da gaskiya, ya bi shi. Ni kam tawa ta kare, ina rokon gafarar Ubangiji.” Yana kare wannan magana, sai ya yi kalmar shahada, ya mike jikinsa sham, ya dibiya hannunsa bisa kirjinsa, rai ya yi halinsa. Allahu Akbar, duniya gidan bara wani! Yau Mahadi da shi da wanda ba a halitta ba duk daya. Ya tafi lahira!
Yana cikawa, sai wadanda ke wurin suka yi wa Halifa Addullahi mubaya’a, suka dauki alkawarin za su bi shi. Kafin a jima, labarin mutuwar Mahadi ya watsu ko ina cikin Kahartum. Amma aka ce ko ihu kada a ji wani ya yi, balle kururuwar mutuwa irin ta mata. Uwargidan Mahadi, Sittina A’isha, wadda a ke kira ‘Umul Muminu,’ watau uwar muminai, tana dakin lokacin da mijinta ya cika. Ta tashi ta shiga cikin gida ta fada wa sauran mata, amma ta ce kada wanda ya yi kuka. Ko ba ta yi wahalar hana su ba, ban yi zaton ransu zai baci ba, tun da ya ke galibinsu duk bayi ne aka kamo da karfi, aka kuga a daka. Da ma can a karkashin zuciya tasu suna kara ne gun babban Alkali Allah, shi kuwa ya ji kararsu, ya kira wannan babban azzalumi zuwa Babban Dakin Shari’a. A kan ce amfanin zunubi romo, amma Mahadi kayan zunubin kurum ya yi zuwa lahira, bai rayu har ya sha romon ba.
Ko da ya ke an hana kuka, amma nan da nan gari duk ya kaure, ba ka jin kunne. Wadansu jahilan, dalilin kukansu, wai laifinsu da suka cika yi, shi ya sa Mahadi ya ga kazanta ta yi yawa a wannan duniya, sabo da haka ya zabi ya tafi wuri mai tsarki! Nan da nan dai aka chiga hidimar jana’izar Mahadi. Aka haka kabari a cikin dakin da ya mutu, aka yi masa wanka. Makusantan nan nasa, su Halifa Abdullahi, da Ahmed Wad Sulaiman suka yi masa salla, suka saka shi cikin kushewa suka rufe. Bayan sun yi addu’a sun shafa sai suka fita gun taron mutane a waje suna ba su magana, su daina kuka.
Mu barorin Halifa, mu aka fara ba mu rantsuwar biyayya, muka yi. Sai aka ce mu fita da mumbarin Mahadi mu ajiye a kofar masallaci. Da muka ajiye, aka ce jama’a su yi shiru, Halifan Mahadi yana fitowa yanzu zai yi musu jawabi. Zuwa can ya fito. Jikinsa duk na rawa, sai hawaye ke zuba a idonsa shar, shar! Ya ce, “Ya jama’ar Mahadi, kaddarar Ubangiji ba ta da magani. Yau Mahadi ya riga mu gidan gaskiya. Ya bar gidan duniya, gidan karya, gidan hargitsi, gidan tashin hankali, ya tafi gidan aljanna, gidan ni'ima, madauwamiya. Shi dadin duniya ba mai dorewa ba ne. Amma yanzu sai mu gode wa Allah, wanda cikin rahamarsa ya sa mu a karkashin tutar Mahadi. Mu bi hanyar da ya nuna mana, kada mu ratse. Ku jama’ar Mahadi ne, ni kuma a yau na zama halifansa. To, ina so ku rantse za ku yi biyayya ta tsakani da Allah gare ni.”
Yana rufe baki, sai mutane suka dauka, “Bayana Allahu, wa Rasulahu. wa Mahadi, wa bayanaka ala tauhidillahi.” Ma’anar wannan, watau, “Mun yi biyayya ga Allah, da Annabinsa, da Mahadi, mun kuma yi biyayya gare ka." Mutane suka shiga zuwa gabansa suna daukar wannan alkawari da dai dai. Suka dinga, tun safe har magariba, sa’an nan ne ya daga daga kan mumbarin nan. Ni dai gajiya ba a ko maganarta gare ni. Nan wurin na shinkida bayan an tashi. Da barci ya kwashe ni, ban farka ba sai safe.
Yanzu kafin mu ci gaba da labarin shugabancin Halifa Abdullahi, bari mu duba baya mu yi tunani, mu ga aikin da Mahadi ya yi. Ya ce shi mujaddadi ne na addinin Musulunci. To, me ya gyara ? Sai mu duba mu gani. Mun san kullum a cikin wa’azinsa, yana cewa a kula da lahira, a bar shagala da duniya. Mun san kuma ya kan ce duk mutum daya ne, da mai sarauta da talaka, da mai arziki da matalauci. Ya kawo samfurin sa tufa, watau sa jabba da wando iyaka kwauri, da tagiya dankwara a zagaya mata rawani kamu uku. Ya hana shan giya, ya rage yawan kudin aure. Ya hana rawa da kida da waka, ya ce wadannan duk ayyukan Shaidan ne. Ya hana mugun baki, wanda duk ya zagi wani, bulala tamanin. Ya hana shan taba. Ya ce a yanke hannun barawo. Ya hana barin suma a kai, sai kowa ya rika aski. Ya hana kukan mutuwa. Ya hana duk mutanen da ke cikin kasar Sudan fita su je hajji a Makka.
Da ya ke Mahadi ya san galibin odojin nan nasa ba bisa kan shari'ar Musulunci su ke ba, sai ya ce daga yau kada wanda ya sake koyon ilmin shari'a. Ya ce wa malamai masu koyad da shari’a su rufe makarantunsu. Ya sa aka tattaro duk littattafan shari’ar musulunci. Da aka kawo, ya sa aka kona wadansu, aka zuba wadansu cikin Kogin Nil!
Irin abubuwan da Mahadi ya kawo ke nan, irin wankin da ya yi wa addinin musulunci ke nan, ya hana zuwa yin hajji a Makka, ya kona littattafan shari'a. Wai kuwa ya cc shi mujaddadi ne.
Mahadi, a waje kam, da ganinsa ka ga Musulmi tamman. Duk irin abin da ya hana yi, shi ke fara bari, wanda ya ki bari kuwa, kisa ne ko bulala. Amma a cikin gidansa, in ka ga irin bidi'ar da a ke yi, ai sai gidan dan daudu ko gidan magajiya. Da shi da 'yanuwansa da halifansa, duk haka su ke. Irin gyaran da ya yi wa Sudan ke nan, ya halaka rayuka dubbai don ya sami ikon hana shan giya, da hana zuwa hajji, da kona littattafan shari’a !
...
(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
BBM: D61EAFAE
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada
Post a Comment (0)