TUN KAFIN AURE 11

TUN KAFIN AURE💐 11
Da gaske Simy ta shiga neman yarinyar hoto don Juni dubu dari da hamsin ya saka mata a account yace cikon sai bukata ya biya. Hoton ta fara turawa groups uku da take tsammanin daga nan aka turo don ta manta inda ya fito. Sai bayan kwana hudu ya kebbi tayi magana tace ai saurayin yayan kawarta ne a kano suke. Jin haka Simy tayi saurin cewa ai yarinyar da makotansu ne sun dade basu hadu ba tana neman address dinta ne. Nan dai ba wani dogon bincike yar kebbi ta turo da number din Zainab. Mata mu rage tallata sirrinmu a social media don Allah.
Kamar akan kaya yake a lagos din sai dai kuma dole ya tsaya don Imi yana nan Simy ba tafiya zata yi ba. Yana cikin restaurant din hotel din da yayi masauki tayi masa waya ta shigo. Nan yayi mata kwatance suka hadu. Sai da ta cika cikinta da abinci wanda ya kasa ci don dokin jin abinda zata fada masa. ta sanar dashi yadda suka yi da yar kebbi cikin tsananin farinciki ya kankameta sannan ta bashi number din Zainab. Tana ta dariya Juni lallai yarinyar nan ta tafi da imaninka idan akwai saura. Ke me kike nufi? Ya daure fuska...ni duk iskanci na bana hadawa da izgilanci ga addini fa. Ga wayarki ya mika mata..zan ciko miki kudinki anjima. It was nice doing business with you Juni. The pleasure was all mine ya bata amsa.
Dakinsa ya koma ya hada kayansa. Bayan ya gama ya kira number din Zainab. Kamar gaske sallama ya fara yi mata ta amsa duk da taji bakuwar murya.
Dan gyaran murya yayi( Zainab ce ko)
(Eh, wa ke magana)
Shiru yayi yana tunanin karyar da zaiyi ( ina yayanki ango to be?)
( ya Saif ya fita)ta bashi amsa.
( suna ta shirye shiryen biki ko)
Mamaki ta fara yi dai amma tayi shiru (eh amma fa still bangane ka ba)
( ina printing din cards na biki ne a nan kusa da unguwarku shine nake son nuna masa sample don kiran kasuwa).
Sai a lokacin ta dan saki rai tayi masa kwatancen gisansu kamar yadda ya bukata ba tare da ta kawo komai a ranta ba. Yarinyar kamar mara wayo ya fada shi kadai, ba wani bincike ta turo da address.
Scrolling waya yayi ya nemi sunan Oldman ya kira. Senator Rufai yayi mamakin ganin sunan Junaid yaron da number dinsa da suke da ita gaba daya basa samu sama da sati biyu. Hakuri Junaid ya bashi tare da sanar dashi zai tafi kano wurin Hajiyan Dangi itama ya bata hakuri.  Senator Rufai murna yayi sosai. Yana matukar son dansa lalacewar yaron kawai ke damunsa.
******************
Kano ta dabo tumbin giwa yau tayi babban bako. Junaid Rufai Bukar ne yake tafiya cikin nutsuwa don yau manyan kaya ya saka tare da aski wanda gashin na zuba zuciyarsa na kuna. Hatta faratansa yaje wani salon a lagos  'yan mata sun gyare shi. Shadda yasa light blue anyi mata dinki mai kyau kansa harda hula. Idan ka ganshi sai kasa shi cikin mazan kwarai sai dai abin ba a fuska yake ba.
Yana tafiya maaikatan airport na binsa a baya ganin sunansa yan maula sun rude. Motar da babansa ya turo ce ta karaso gabansa aka saka masa kayansa a cikin booth. Kudin ya basu masu yawa tunda bai san zafin nema ba. Kowa sai murna...Tilly dake bayansa wadda baisan ma jirgi daya suka biyo ba tayi murmushi tasan ba a banza yayi wannan shigar yazo kano ba. Sai ta rama wulakancin da yayi mata a lagos. Wayar Rosie ta nema ta sanar da ita ta shigo gari.
Gyadi gyadi yace da driver din ya kaishi . Dreba ya shafa kai yallabai ai Alhaji ya gina ma Hajiyar gida a hotoro ai kusan shekararta biyu a can. Shima Juni kai ya shafa don yaji kunya. Rabonsa da zuwa sada zumunci 'yan uwansu na kano ya kwana biyu.
Batul Mamman💖



Post a Comment (0)