ALEWAN GIDAN AURE

*💏ALEWAN GIDAN AURE💏*

💏Soyayyar da za ku bama juna a duniya tana da farillai, sunnoni da mustahabbai, akwai kuma halal da haramun duka tattare a cikinsa.

💏Farillan soyayya sune sauke dukkanin abun da Allah Ya ɗaura a kanka na kasancewar ka tare da abokin zaman ka. Ke ki yi masa ladabi da biyayya ta hanyar jin maganar sa, mutunta sa da kiyaye masa da bashi farin ciki. Shi kuma ya ciyar da ke, ya ba ki muhalli, ya biya miki buƙatun ki, da baki kariya a matsayinsa na mijinki dss.

💏Sunnonin ta shine koyo dukkanin abubuwan farantawa na Annabawan Allah da salihan bayi don kyautata wannan zama, domin waɗannan sune zasu sanya a ji daɗin gidan kuma a cigaba da son juna.

💏Mustahabban ta sune koyo dukkanin soyayyan tattali, ƙarin kyautatawa da farantawa wanda kake rayuwa da shi domin ƙarfafa farillanta da sunnoninta. 

💏Haramun a soyayya shine yin abun da Allah Ya haramta domin farantawa abokin rayuwar ka da sunan wayewa ko jin daɗi, da ƙuntatawa da gangar saboda samun wata dama a kansa. 

💏Cikakkiyar halaliyar soyayya mai zaƙin alewa ga masoyin ka shine ka sauke muhimman haƙƙoƙin sa, ka kare dukkanin baƙin ciki da damuwa samunsa, ka sanya shi farin cikin zaben ka a matsayin abokin rayuwarsa na har abada. 

💏Shi fa wannan zaman fata ake yi a yi sa a duniya da lahira, a dunƙule dai wannan mijin naki ko wannan matar taka so kake yi ku rayu a cikin jannah in kun gama da duniya, ashe sai mutum yayi addu'a, ya cire son zuciya domin dacewa da farin ciki a duniya da lahira.

💏Amma menene amfanin soyayyar da ba a faranta ma juna? Menene jin daɗin gidan auren da ba a sauke haƙƙin juna? Menene amfanin zamantakewa mai takura zuciya da jefa ta cikin ƙunci?

💏Kada mu zata yawan kalmar "I love you" da yawan soyayya kafin aure sune alewan cikin gidan aure, a'a mu nemi waɗanda suka san haƙƙin zama, daɗin zama, masu son samun rayuwa mai daɗi a duniya da lahira ko da kuwa soyayyar su ba ta da yawa to wata rana sai an yi alfaharin auren su.

🤲🏼Ya Allah mun bar maka zaɓi, Ka haɗa kowa da mutanen kirki.

*🖎Sadeeya Lawal Abubakar.*

*🕌SAUTUS SUNNAH*

*📞08033942932*
Post a Comment (0)