MAULIDI A MAHANGAR MUSULUNCI 04

*≈≈ MAULIDI A MAHANGAR MUSULUNCI [4]*

_(Kashi na Hudu)_

★SHUBUHA TA BIYU:

Shubuha ta biyu suka ce: Duk wata ni’ima da Allah Ya yi
wa mutum, to dole ne ya gode aw Allah a kanta, saboda
lokacin da Annabi ya dawo Madinah ya ga Yahudawa suna
azumi a ranar goma ga watan Muharram sai shi Annabi mai
tsira da amincin Allah ya tambaye su ya ce: Me ya sa kuke
azumin wannan rana? Sai suka ce masa: Wannan rana ce da
Allah Ya tsirar da Annabi Musa tare da jama’arsa, kuma Ya
halakar da Fir’auna tare da mutanensa cikin teku, shi ya sa
Annabi Musa yake azumin wannan rana saboda gode wa Allah
mu ma shi ya sa muke yin azuminsa, sai Annabi mai tsira
da amincin Allah Ya ce: Mun fi ku cancantar yin abin da
Annabi Musa ya yi, saboda haka ya yi azumin wannan ranar
kuma ya umurci Musulmi da su yi azuminsa. A nan muna
ganin babu wata ni’ima da ta kai haihuwar Annabi
Muhammad mai tsira da amincin Allah, kuma ko shakka babu
wannan ni’ima za ta wajabta mana gode aw Allah, wannan
kuwa shi ya sa muke yin bukin maulidi saboda nuna godiya ga
Allah Madaukakin Sarki.
Amsa a kan wannan shubuha tasu sai a ce da su: Lalle
gaskiya ne ni’imomin Allah suna wajabta godiyar Allah a
kan bayinSa, to amma hakika ni’ima mafi girma a cikin
Musulunci ita ce:Ni’imar ba wa Annabi mai tsira da amincin
Allah Manzanci, ba.


 Wai ni’imar haihuwar sa ba, domin
Alkur’ani mai girma bai yi nuni da ishara zuwa haihuwarsa
koda sau daya ba, to amma ya yi nuni da ishara zuwa ga
manzancinsa ba sau daya ba ba sau biyu ba! Allahl
Madaukakin Sarki Ya ce cikin Suratu Aa’li Imraan aya ta
164:-
{ ﻟﻘﺪ ﻣﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ﺇﺫ ﺑﻌﺚ ﻓﻴﻬﻢ ﺭﺳﻮﻻ ﻣﻦ ﺍﻧﻔﺴﻬﻢ ﻳﺘﻠﻮ
ﻋﻠﻴﻬﻢ ﺁﻳﺎﺗﻪ ﻭﻳﺰﻛﻴﻬﻢ ﻭﻳﻌﻠﻤﻬﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺤﻜﻤﺔ }.
Ma’ana: {Hakika Allah Ya yi babbar falala ga muminai
domin Ya aika da Manzo daga ainihinsu yana karanta musu
ayoyinSa Yana tsarkake su yana karantar da su Littafi da
Hikima}. A nan Allah bai ce: domin an haifi wani Manzo
daga cikinsu ba, a’a sai Ya ce: Domin an aiko wani
manzo. Wannan shi ne halin da za ku tarar game da ko wane
Manzo daga cikin manzannin Allah Madaukakin Sarki, watau
abin himmantuwa game da shi shi ne aiko shi ba wai ranar
haihuwarsa ba, kamar dai yadda Allah Madaukakin Sarki ya ce
cikin Suratul Bakara aya ta 213:-
{ ﻛﺎﻥ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺃﻣﺔ ﻭﺍﺣﺪﺓ ﻓﺒﻌﺚ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻨﺒﻴﻴﻦ ﻣﺒﺸﺮﻳﻦ ﻭﻣﻨﺬﺭﻳﻦ ﻭﺍﻧﺰﻝ
ﻣﻌﻬﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﺑﺎﻟﺤﻖ ﻟﻴﺤﻜﻢ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﻴﻤﺎ ﺍﺧﺘﻠﻔﻮﺍ ﻓﻴﻪ }.
Ma’ana: {A da mutane sun kasance al’umm ce guda daya,
sai Allah Ya aiko Annabawa suna masu bishara suna masu
gargadi, kuma Ya saukar da Littafi da gaskiya tare da su’
domin ya yi hukunci tsakanin mutane cikin abin da suka Saba
aw juna cikinsa}. Kun gani a nan’ da dai mayar da wata
rana Idi da sunan addini halal ne cikin addinin Musulunci, to
da kuwa marar da aka aiko Manzon Allah mai tsira da
amincin Allah Idi shi ne ya fi.


Sannan kuma game da azumin da shi Annabi mai tsira da
amincin Allah ya yi na ranar Aashuuraaa to fa dole ne mu
sani cewa: Shi fa Annabi mai tsira da amincin Allah shi ne
mai shar’antawa kuma mai isar da sako daga Ubangijinsa
zuwa ga sauran mutane, saboda haka ba ya halatta a gare mu
mu yi kiyasin wani mutum a kan shi, har na mu fada cikin
wata bidi’a, domin abin da ake bukata ga dukkan al’ummar
Musulmi shi ne: Su zama masu bi a koda yaushe ba wai
masu kirkiro bidi’o’i ba. Sannan kuma shi azumi ai
kishiyar bukin Idi ne saboda azumi yana nufin hana sa kai cin
abinci shi kuwa bukin Idi yana nufin ciyar da kai abinci ne,
saboda haka ta kaka za a kira yin azumi bukin Idi?

★ SHUBUHA TA UKU:

Shubuha ta uku: suka ce: Annabi mai tsira da amincin Allah
ya kasance yana azumi a ko wane ran litinin, a lokacin da
Sahabbai suka tambaye shi: Don me yake azumi a wannan
rana? Sai ya ce: yana azumtar ko wace litinin ne saboda a
ran litinin ne aka haife shi.


Yan maulidi suka ce wannan yana nufin ke nan Annabi mai
tsira da amincin Allah shi ma yana bukin maulidi watau yana
bukin ranar haihuwarsa.
Amsa a kan wannan shubuha ta yan maulidi sai a ce da su:-
Na daya: Musulmi ba sa musun halaccin azumin ranar litinin
da kuma falalarsa, haka ma azumin ranar alhamis da falalarsa,
to amma shi wannan azumin aka yi shi ne cikin dukkan
kwanakin litinin da alhamis na shekara, ba wai sau daya ne
ba kawai ake yin shi cikin shekara, kamar yadda masu yin
bidi’ar maulidi suke yin shi sau daya cikin shekara.
Na biyu: lalle kiyasta bukin maulidi a kan azumin ranar litinin
da ake yi cikin ko wane mako, kiyasin abin da yake bidi’ah
ne a kan bin da yake Sunnah, wannan kuwa Kiyasi ne
batacce.


Na uku: lalle inda su masu bukin maulidi suna son koyi ne
da Annabi mai tsira da amincin Allah cikin abin da shi
Annabin ya yi a ranar haihuwarsa, to da sai su wadatu da
abin da shi Annabi mai tsira da amincin Allah ya wadatu da
shi, watau sai su rika yin azumi cikin ko wace ranar litinin,
ba wai su rika bukin maulidi cikin ko wace ranar gama sha
biyu ga watan Rabi’ul Awwal ba, saboda shi Manzon Allah
mai tsira da amincin Allah bai yi maulidi a ranar goma sha
biyu ga watan Rabi’ul Awwal ba duk kuwa da cewa yana
damar yin hakan in da yin hakan ya dace da Shari’ar
Musulunci, to amma da yake hakan bai dace da Shari’ar
Musulunci sam bai yi hakan ba, abin kawai aka sani ya yi
shi ne: Azumin ranar litinin cikin ko wane mako. Ke nan
wannan zai wajabta wa yan bukin maulidi in har dai suna son
Annabi suna kuma girmama shi suna kaunar bin hanyar da ya
bi, su bar yin bukin maulidi a ranar goma sha biyu ga watan
Rabi’ul Awwal su koma yin azumin ranar litinin ko wane
mako, da kuma ranar alhamis ko wane mako.
Muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya taimake mu Ya nuna
mana gaskiya gaskiya ce Ya ba mu ikon bin ta, Ya nuna
mana karya karya karya ce Ya ba mu ikon kin ta. Ameen.

_#DR,JALO JALINGO_

*_Gabatarwa_*:- Yusuf Ja'afar Kura 

Daga
*MIFTAHUL Ilmi*
WhatsApp

→ ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren *MIFTAHUL ILMI* whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu *(07036073248)* ta ‎whatsApp.


Post a Comment (0)