ƘARIN BAYANI DANGANE DA WANKAN JANABA

TAMBAYA
=========
👇
Assalamu Alaikum mlm don Allah inaso ayimin karin bayani dangane da wankan janaba sbd naji wani mlm yace idan anxo Alwala yayin wankan janaba kowane guri da,ake wankewa sau uku sau daya xa a wanke,amma naji wani mlm yace kamar yadda mutum yake alwala idan zaiyi sallah haka zaiyi shine nakeso ayimin karin bayani wace ruwaye ce mafi inganci. 



AMSA 
======
👇
Ruwayar da tazo akan wankan janaba ta na da yawa, amma dai duka sau daya ake wanke kowanne gabar Alwala. Duk da kinji wani malami yace irin yadda manzon Allah saw yake yin alwala, ae manzon Allah saw yana yin Alwala cudi dai-dai, wani Lokacin kuma cudi biyu-biyu, wani Lokacin kuma cudi Ukku-ukku. 
 Amma dai a batun Alwala idan yazo yin wankan janaba, to anan sau dai-dai yakeyi. 
  Wannan haka hadisin Ummuna Aisha Allah ya kara mata yarda cikin siffar wankan manzon Allah saw tace sai manzon Allah saw Yayi Alwala sau daidai irin Alwalarsa ta sallah. 

Allah shine masani. 


ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876


Post a Comment (0)