LABARIN WANI MASUNCI

Akwai wani mutum mai sana'ar kama kifi, ko da
yaushe kifi ne abincinsa da iyalinsa
wata rana ya fita ya kamo kifi ya kawo gida a
soya kamar yanda ya saba, bayan uwar gida ta
yanka kifin nan sai ta ga abin mamaki a cikin
kifin. Ba wani abu ba ne face Dunkulallen Gwal
mai kyau,
nan da nan ta sanar da mai gida, shi kuwa yai
murna domin talauci ya kare.
Ya dauki wannan gwal ya kaiwa wani
hamshakin mai kudi domin ya siya amma ya ce
"ai in da zan baka kaf dukiya ta to ban biya ka
kudin wannan gwal din ba" don haka ka kaiwa
mai gari.
Ya tafi wajen mai gari shi ma ya ce gaba daya
dukiyarsa da kadararsa ba za su sayi wannan
gwal ba, sai dai a kaiwa sarki.
Mutumin nan ya kaiwa sarki, shi ma sarki ya ce
ba zai iya biya ba, amma abin da za a yi za a
budewa mai kifin nan taskar sarki, a bashi awa
10 yai ta diban duk abin da yake so.
Mutumin ya ce Ranka ya dade awa 10 ai ta yi
yawa, ai ko awa 1 ma ya isa, sarki ya ce a a ka
dai yi awa 10.
Aka budewa mai Su taskar sarki ya shiga,
shigarsa ke da wuya sai ya ga duk wani abu da
yake bukata na rayuwa akwai shi a ciki
ya duba gefe sai ya ga wani abinci mai rai da
lafiya, sai ya zauna ya kwashi girki,
bayan ya ci ya koshi, sai ya ga wani gado mai
laushi wanda bai taba ganin irinsa ba tunda
yake, sai ya ce
Bari na dan kwanta na huta sai in tashi in debi
abin da nake so.
(KASH!, INDA YA SAN MAI ZAI FARU DA BAI
KWANTA BA)
Yana cikin barcin ne ya ji fadawa suna buga
kofa suna cewa ka fito awa 10 ta cika.
Ya tashi a firgice ya ce don Allah a taimaka
masa, wallahi bai dau komai ba
fadawa suka ce lallai sai ya fita lokacin sa ya
kare,
Haka ya fita, ba gwal kuma bai debo komai ba.
*To wannan mutumin shi ne DAN ADAM, gwal
din nan kuwa shi ne RAI, ita kuma wannan
taskar ita ce DUNIYA, awa 10 nan kuwa shi ne
lokacin da aka debarwa mutum a rayuwarsa ta
duniya.
Don haka 'yan uwa mu dage mu yi abin da ya
kawo mu duniya (Bautawa Allah), kada mu
kwanta bacci har lokacin mutuwa ya yi bamu
aikata komai ba.
Allah ya sa mu dace,
 Yan'uwa mu yaweita addua dan neman sauqi ga musibar da ta
buwayi qasar mu Nigeria. Don Allah ku aika wanan sako ga
duk muslimin da ke contact list dinku. Allah ya sa mudace-
ameen ya rabbi 👏👏


1 Comments

Post a Comment