TAMBAYA MABUƊIN ILIMI

*SHIRIN TAMBAYA MABUD'IN ILIMI*
19/10/2018

DAGA 
_Sirrin 'ya mace group WhatsApp_


*TAMBAYA*
*Dan Allah yau ai mana bayani akan abunda ya shafi wankan tsarki Kuma akwai bambanci tsakanin wankan haila da wankan janaba?*


*WANKAN TSARKI*

*Kamar yanda muka sani abubuwan dake wajabta wankan tsarki guda Uku ne.*

*1.JANABA* 
*2.HAILA*
*3.BIKI*

Da farko dai mu sani shi wannan wanka amana ce daga cikin tarin Amanar dake tsakanin bawa da Mahaliccinsa. Saboda haka ya zama wajibi ka kiyaye wannan Amanar, kuma mu san hukunce-hukuncen sa. 

Domin mu gabatar dashi a yanda musulunci ya tsara mana, abinda ya rikice maka saika yi tambaya ka nima sani akansa, kar ka sanya kunya a ciki domin wannan abune da musulunci ya yarda a nima sani akan sa.

*Menene JANABA-* JANABA shine fitar Manniyi ta hanyar jin dadi ko aka samu dadin, wato ta haryar saduwa ko kuma mafarki. Kuma Farilla ne ayi masa wanka. koda ace Maniyya bai fita ba yayin saduwa to indai al'auran Namiji ya shiga cikin Al'auran Mace tofa sai sunyi wannan wankan tsarki.


*HAILA-* shi jini ne dake fita ma Mace ta al'auranta yayin balaga, wanda wasu suke yinsa wata-wata ko lokaci zuwa lokaci. a dadin kwanakinsa kwana sha Biyar (15) ne, inya wuce haka to wannan jinin ya zama jinin ciwo sai mace tayi wanka ta cigaba da ibada kuma ta nima magani. Bayan jini haila ya dauke sai ayi wankan tsarki, wankansa Farilla ne.


*BIK'I-* shine jinin haihuwa, da Mace ke fitarwa bayan ta haihu, adadin kwanakinsa kwana sittin ne (60) inya wuce haka ya zama jinin ciwo, sai ayi wanka a nima acigaba da ibada a nima Magani. Yayin da jinin biki ya dauke sai ayi wanka tsarki. Wannan wankan shima farilla ne

*Dan haka Ku sani babu banbanci yayin yin wannan wanka, banbancin su shine Niyyah.*👌


*WANKA YA KASU SIFFA GUDA BIYU*

Akwai:

*1. SIFFATUL KAMALA*
*2. SIFFATUL IJZA*


*SIFFARUL KAMALA-* Shine siffa wanda ake yinsa daki-daki, mutum ya daura Niyyah, ya jero farilla, sullah, mustahabbi, ayi Alwala , wato za ayi shi cikin natsuwa da kamala. Wannan shine wankan tsarkin da zanyi bayani nan gaba kadan.


*SIFFATUL IJZA-* Shine wanda mutum zai daura Niyyah, saiya shige shawa ya cuda jikinsa ya gaggauta ya gama ya fito, ba tare da yin wankan daki-daki ba, ko mutum ya daura Niyya ya fada teku ku swimming pool ya gabatar da wankansa.


*YANDA AKE YIN WANKAN TSARKI*

wato _*SIFFATUL KAMALA*_

Da farko z'a tanadi ruwa mai tsarki. Shin ya zamu fahimci ruwan mu yana da kyau da tsarki?.


*MENENE RUWA MAI TSARKI?-* shine ruwa mai tsarki mai tsarkakewa, wanda launinsa bai jirkita ba, kamahinsa bai sauya ba, kuma dan danonsa bai sauya ba, wato ruwan ya zama baibu maiko, ko ruwan ya zama bai hadu da najasa ba, ko kuma ruwan ya zama ba mai wari ba, ya zama tsafta taccen ruwa.

Sannan a tabbatar da inda za a sanya ruwan wankakke ne yanada tsafta.

*DAURA NIYYAH-* 
Daura Niyyah tana farawa ne tun daga lokacin da ka dauko ruwan wankan ka mai tsarki. Abinda nake nufi shine ki kudurta Niyyah a zuciyarki.

Misali- daya daga cikin wankan JANABA za kiyi ko kuma wankan Al'ada ko biki shine zaki aiyana shi a zuciya. wannan itace niyya, ba wasu abubuwan ake karantawa ba, mu sami niyya tanada matukar mahimmanci, domin ko wani aiki saida Niyyah.


A ajiye ruwan a hannun dama in a bokiti ne, wato in a budadden abu ne, in kuma buta ne wato mazubin rufaffe ne a ajiye shi a hannun hagu.


Sai a fara da BISIMILLAH (a cikin zuciya). Sai a wanke hannu sau uku, awanke da kyau. sannan yanada kyau a sake daura Niyyah a zuciya (niyyar wankar da ya kama mutum, janaba ko haila ko biki). Wasu kuma sukan ce a zuciyarsu NAYI NIYYAN YIN WANKAN JANABA FARILLAH a zuciya.


*Sai a wanke daga cibiya zuwa cinyoyi, sannan a wanke al'aura sosai a cuda, hatta wurin dubura a wanke.*

*Sai mutum ya wanke gabobin Alwala sau d'ai-d'ai. Mutum zai iya jinkirta wanke kafafu har sai ya kare wankan sai ya wanke kafan. Amma anfiso a gabatar da sunnah alokacin. abin nufi shine a cike Alwalan gaba daya.*

*Sai a wanke kai sau uku, mutum zai diba ruwa a tafin hannsa ya cuda kansa, zaiyi diba ruwan har sau uku ya wanke kansa. Kofofin gashi a bude suke, ruwan zai shiga a hankali da kyau.* 

Sannan kuma hakan bazai haifar wa mutum da ciwon kai ba, saboda ba kwara ruwa mutum yaba. A cuda kunnuwa da da wiya, a tsudasu sosai yayin wanke kai. 
(Ina tunasar damu mu mata zuba ruwa sau uku baya gamsar d kanmu Sbd yawan Gashi yana da kyau ki zuba ruwa sosai yadda gashin ko ina ze samu in da kitso ki bubbuga kan yadda ruwan ze shiga kasa. Kuma yawan cin malamai suna nunawa mata wankan haila anfi so a tsefe kai sbd shi ana so ruwa ya game ko ina har kasan gashi)


*Sannan a wanke b'arin jiki na dama sau uku a tsuda sosai*

*Sannan barin jiki na hagu sau uku a cuda sosai.*

*Sannan a game jiki da ruwa, a tsuda a gaggauta sosai da sosai, tun daga sama har kafa, k'asan nono duk wani matse matsi a tabbatar ko ina ya samu ruwa.* 

*Sai mutum ya wanke k'afan sa wanda ya barshi sai ya ida wankan, ya cuda ya wanke da kyau*


*Shikenan wannan wanka ya kammala*👌


_*Karin bayani*_
*Ana so a rika, kula da tab'a Al'aura yayin gabatar da wanka bayan mutum ya gabatar da Alwalan sa, saboda gudun alwalan kar ta karye. Dan wannan Alwala da mutum yayi zai iya yin Sallah da ita n Farilla ko Sunnah.*

*Amma idan Mutum ya taba al'auransa tofa wannan Alwalan ta karye, bayan Mutum ya gama wanka sai ya sake wata Alwalan in zaka yi Sallah.*

*Sannan ayi kokari kar abar lam'a a jiki (lam'a shine barin dan karami wuri wanda ruwa bai sameshi ba) domin barin lam'a tofa wanka ya samu wani nakasu, sai a kiyaye.*


_Allah shine mafi sani_
Ameen.


Daga Alkamin 
*Admin*
(Sirrin 'ya mace group) WhatsApp.


Post a Comment (0)