MATAR KA TANA BUƘATAR KULAWA

http://sirinrikemiji.blogspot.com/2018/10/matarka-tana-bukatar-kulawa.html



Idan tayi fushi jawota jikinka ka rarrasheta. Mata suna son rarrashi matuka. 

Idan kaga tayi shiru tambayeta meye matsalarta cikin murya mai sanyi bawai da fada ba. al'adan mace ne ko anyi mata abu sai tace ba komai, sabodd ita komai sai tasa shagwaba kuma tana son mai rarrashinta. 

Idan tayi kwalliya ka yabawa kwalliyarta
Idan tayi girki kaci kana santi koda dadinsa baikai ayi santi ba.

Idan kukayi kwanciyar aure da ita ka nuna mata qololuwar jindadinka da ita, haka kuma da rana ka dauko zancen kana zuzuta ta kana yabawa da irin ni'imarta wannan shi zaisa ta qara qaimi wurin kula da kanta.

Kana yabon kyawawan halinta kuma kana tausayawa mata da yimata uzuri idan tayi ba daidai ba. 

Duk sanda ka samu lokaci kana shiga kitchen kana tayata ayyukan gida ko ba yawa ne. mata suna son su gansu tareda mazajensu suna tayasu aiki kai koda zuwa kawai kayi ka zauna bakayi komai ba zataji dadi a ranka.

Idan tace zata matsa daga kusa da kai riqeta kace baka yarda ba. 

Idan kaga tana kuka sa bakinka ka tsotse hawayenta

Idan kaga tana kishinka kyaleta kar ka kyareta. So kesa ayi kishi wanda baya sonka bazaiyi kishinki ba.

Idan bata da lafiya ka fita damuwa da halin da take ciki.

Idan kayimata laifi ka nuna rashin jin dadinka da hakan kuma ka bata hakuri.

Duk sanda zaka fita ka sumbace ta agoshinta. 

Kana kasuwa ko office makaranta kirata ta awaya kace kana kewarta...

Kada kalmar (ina sonki ta dinga yiwa harshenka nisa)

   Maza ku gane wani abu ba ci da sha da sutura ne kawai zakayi ka burge mace ba . Wata zakaga ba abinda ta rasa na nau'in jin dadi amma tana cike da damuwa me yasa? Saboda ta rasa abubuwanda na lissafo a sama. Wlh akwai wanda sunfi shekara nawa suna samun matsala da iyalinsa sai kaji yana tutiyar bai rageta da ci ko sha ba sutura ma yanayi kawai halinta ne. Ba halinta bane ta rasa muhimman abubuwane a rayuwarta. Sau da yawa anbar mazan hausawa a baya wurin kula da matansu kuma sune mafi dacewa da su kula da matansu idan mukayi duba da yanda Manzo SAW yake tafiyar da ryuwan iyalinsa. Mata basa buqatar wasu muhimman abubuwa domin samun farin ciki. Wallahi da duk namiji zai yi kokari yayi aiki da abubuwan nan dana lissafo to tabbas zaiga canji harma yasamin albarka. 

  A turawa yan uwa maza domin suma su qaru su gyara mu'amalansu da matansu. Allah yasa mu dace ameen......


Post a Comment (0)