MAULIDI A MAHANGAR MUSULUNCI 1

*≈≈ MAULIDI A MAHANGAR MUSULUNCI [1]*

_(Kashi na Daya)_

 kamar yadda aka sani ne cewa wannan rana ta 12/3/
ita ce ranar da wasu ke bukin ranar haifuwar Annabi
Muhammad mai tsira da amincin Allah, saboda neman lada da
falala a wurin Allah, duk kuwa da cewa rikon wannan rana a
matsayin Idi bidi’a ce wurin dukkan Maluman Musulunci!



Haka dai Shaidan yake batar da mutane ta hanyar kawata musu
wani abin da ba Shari’ah ba ne har su rika ganin shi tamkar
abin da yake Shari’ah ne! Allah yana cewa cikin Suratu
Faatir aya ta 8:-
(( ﺃﻓﻤﻦ ﺯﻳﻦ ﻟﻪ ﺳﻮﺀ ﻋﻤﻠﻪ ﻓﺮﺍﻩ ﺣﺴﻨﺎ ﻓﺎﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﻀﻞ ﻣﻦ ﻳﺸﺎﺀ ﻭﻳﻬﺪﻱ
ﻣﻦ ﻳﺸﺎﺀ ﻓﻼ ﺗﺬﻫﺐ ﻧﻔﺴﻚ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﺣﺴﺮﺍﺕ ﺍﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻢ ﺑﻤﺎ
ﻳﺼﻨﻌﻮﻥ)).
Ma’ana: ((yanzu wanda aka kawata masa mummunan aikinsa
har ya gan shi wani abu Mai kyau “yana daidai da
waninsa?” saboda haka lalle Allah yana batar da wanda yake
so, kuma ya shiryar da wanda yake so, kada ranka ya halaka
a kansu saboda bakin ciki. Lalle Allah Masani ne ga abin da
suke sana’antawa)).
Mu a nan, a bisa dogara da ayah ta 104 a cikin Suratu Aali
inda Allah Ya ce:-
(( ﻭﻟﺘﻜﻦ ﻣﻨﻜﻢ ﺃﻣﺔ ﻳﺪﻋﻮﻥ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﺨﻴﺮ ﻭﻳﺄﻣﺮﻭﻥ ﺑﺎﻟﻤﻌﺮﻭﻑ ﻭﻳﻨﻬﻮﻥ ﻋﻦ
ﺍﻟﻤﻨﻜﺮ ﻭﺃﻭﻟﺌﻚ ﻫﻢ ﺍﻟﻤﻔﻠﺤﻮﻥ )).
Ma’ana: ((A samu wata al’umma daga cikinku da za ta
yi kira zuwa ga alheri, sannan ta umurni da abin da
Shari’ah ta sani, kuma ta yi hani ga abin da Shari’ah bata
sani ba.



 To su wadannan Al’umma sune masu rabauta)). Da
kuma dogara kan aya ta 78, da 79 cikin Suratul Maa’idah
inda Allah Madaukaki ya yi maga a kan Banuu Isaraa’iil ya
ce:-
(( ﻟﻌﻦ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻛﻔﺮﻭﺍ ﻣﻦ ﺑﻨﻲ ﺍﺳﺮﺍﺋﻴﻞ ﻋﻠﻰ ﻟﺴﺎﻥ ﺩﺍﻭﺩ ﻭﻋﻴﺴﻰ ﺍﺑﻦ
ﻣﺮﻳﻢ ﺫﻟﻚ ﺑﻤﺎ ﻋﺼﻮﺍ ﻭﻛﺎﻧﻮﺍ ﻳﻌﺘﺪﻭﻥ . ﻛﺎﻧﻮﺍ ﻻ ﻳﺘﻨﺎﻫﻮﻥ ﻋﻦ ﻣﻨﻜﺮ ﻓﻌﻠﻮﻩ
ﻟﺒﺌﺲ ﻣﺎ ﻛﺎﻧﻮﺍ ﻳﻔﻌﻠﻮﻥ )).
Ma’ana: ((An la’anci wadanda suka kafirta daga Banu
Isaa’iil a bisa harshen Daawuuda da Isa Dan Maryam, saboda
irin yadda suka yi sabo, suka kasance suna ketare iyaka. Suka
kasance ba sa hana juna yin mummunan aikin da suke
aikatawa. Wallahi abin da suka kasance suna aikatawa ya yi
muni)). Da kuma dogara kan hadithin da Imam Muslim ya
ruwaito hadithi na 49 inda Annabi mai tsira da amincin Allah
yake cewa:-
(( ﻣﻦ ﺭﺃﻯ ﻣﻨﻜﻢ ﻣﻨﻜﺮﺍ ﻓﻠﻴﻐﻴﺮﻩ ﺑﻴﺪﻩ ﻓﺎﻥ ﻟﻢ ﻳﺴﺘﻄﻊ ﻓﺒﻠﺴﺎﻧﻪ ﻓﺎﻥ ﻟﻢ
ﻳﺴﺘﻄﻊ ﻓﺒﻘﻠﺒﻪ ﻭﺫﻟﻚ ﺍﺿﻌﻒ ﺍﻻﻳﻤﺎﻥ )).
Ma’ana: ((Wanda duk ya ga munkari daga cikinku sai ya
jirkita shi da hannunsa, in kuma ba zai iya ba, sai ya jirkita
shi da harshensa, in kuma ba zai iya ba sai ya jirkita shi da
zuciyarsa, wannan shi ne mafi raunin Imani)). Da kuma
dogara kan maganar Sahabin Annabi Abdullahi Dan Mas’ud
Allah ya kara masa yarda, wacce ta zo cikin littafin Ibnu
Wadh,dhah shafi na 11 da littafin Ali’itisaam na Imamush
Shaatibii 1/107 inda ya ce:-
(( ﺍﺗﺒﻌﻮﺍ ﻭﻻ ﺗﺒﺘﺪﻋﻮﺍ ﻓﻘﺪ ﻛﻔﻴﺘﻢ )).
Ma’ana: ((Ku bi -abin da Annabi ya zo da shi- kada ku
kirkiri bidi’ah, domin an gama muku kome -na addini-)).



Dankuma dogara har yanzu a kan maganar shi Sahabi Abdullahi
Dan Mas’uud wacce ta zo cikin littafin Ibnu Wadh’dhah
shafi na 11 da kuma Sunanud Daarami 1/68-69 a inda ya ce
lokacin da ya wuce wani mai wa’azi a cikin masallaci yana
ce wa mutane: ku yi Subhanallah kafa goma, ku yi la’laha
illalah kafa goma, sai ya ce da su:-
(( ﻭﻳﺤﻜﻢ ﻳﺎ ﺃﻣﺔ ﻣﺤﻤﺪ ﻣﺎ ﺍﺳﺮﻉ ﻫﻠﻜﺘﻜﻢ ! ﻫﺆﻻﺀ ﺻﺤﺎﺑﺔ ﻧﺒﻴﻜﻢ ﺻﻠﻰ
ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻣﺘﻮﺍﻓﺮﻭﻥ ﻭﻫﺬﻩ ﺛﻴﺎﺑﻪ ﻟﻢ ﺗﺒﻞ ﻭﺃﺗﻴﺘﻪ ﻟﻢ ﺗﻜﺴﺮ ﻭﺍﻟﺬﻱ
ﻧﻔﺴﻲ ﺑﻴﺪﻩ ﺍﻧﻜﻢ ﻟﻌﻠﻰ ﻣﻠﺔ ﻫﻲ ﺃﻫﺪﻯ ﻣﻦ ﻣﻠﺔ ﻣﺤﻤﺪ ﺍﻭ ﻣﻔﺘﺘﺤﻮﺍ ﺑﺎﺏ
ﺿﻼﻟﺔ . ﻗﺎﻟﻮﺍ ﻳﺎ ﺃﺑﺎ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﻣﺎ ﺍﺭﺩﻧﺎ ﺍﻻ ﺍﻟﺨﻴﺮ ﻗﺎﻝ ﻭﻛﻢ ﻣﺮﻳﺪ
ﻟﻠﺨﻴﺮ ﻟﻦ ﻳﺼﻴﺒﻪ ﺍﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺍﻥ ﻗﻮﻣﺎ
ﻳﻘﺮﺀﻭﻥ ﺍﻟﻘﺮﺍﻥ ﻻ ﻳﺠﺎﻭﺯ ﺗﺮﺍﻗﻴﻬﻢ ﻭﺍﻳﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﺎ ﺍﺩﺭﻱ ﻟﻌﻞ ﺍﻛﺜﺮﻫﻢ ﻣﻨﻜﻢ
ﺛﻢ ﻭﻟﻰ ﻋﻨﻬﻢ )).
Ma’ana: ((kaitonku ya ku al’ummar Muhammad mamakin
saurin halakarku! Wadannan Sahabban annabinku ne mai tsira da
amincin Allah ga su nan da yawa, wadannan tufafinsa ne ba
su gama yagewa ba, wadannan butocinsa ne ba su gama
fashewa ba. Ina rantsuwa da Wanda raina yake hannunsa lalle
ne ku ko dai kuna kan wani addini ne da ya fi addinin
Muhammad shiriya ko kuwa ku masu bude kofar bata ne. Sai
suka ce wallahi baban Abdurrahman babu abin da muke nufi
sai alheri. Sai ya ce ai da yawa mai son alheri ba zai taba
samun sa ba. Lalle Manzon Allah mai tsira da amincin Allah
ya gaya mana cewa akwai wasu mutane da za su rika karanta
Alkur’ani amma kuma ba zai wuce makogoronsu ba, Ina
rantsuwa da Allah watakila mafi yawansu daga cikinku suke.
Daga nan sai ya juya ya bar su)).



 Intaha. Da kuma dogara
kan maganar babban Taabi’ii Hasanul Basarii wacce ta zo
cikin littafin Ibnu Wadh’dhah, da littafin Alitisam na
Shaatibii 1/111 inda ya ce: ((Mai yin bidi’ah ba zai Kara
kokari cikin azuminsa na bidi’ah ba, ko sallarsa ta bidi’ah
ba, face hakan ya nisantar da shi daga Allah)).
Dogara kan wadannan ayoyi da hadithai da maganganun
Sahabbai da Taabi’ai da kuka ji su yanzu ne ya sa muke
gargadin Al’ummar Musulmi, muke hana su rikon ranar
haihuwar Manzon Allah Mai tsira da amincin Allah a matsayin
ranar Idi, muke musu gargadin rikon bukin maulidi a matsayin
wani abu na addini da ake neman lada da shi a wurin Allah
Madaukakin Sarki!
Saboda abu ne tabbatacce wurin Maluman Musulunci cewa
Annabi Mai tsira da amincin Allah bai yi bukin maulidi ba,
Sahabbai ba su yi bukin maulidi ba, Taabi’ai ba su yi bukin
maulidi ba, Taabi’ut Taabi’in ba su yi bukin maulidi ba.



Duk kuwa abin da ba zama addini ba a zamanin Sahabbai, da
Taabi’ai, da Taabi’ut Taabi’in tare da kasancewar sababin
yin sa a lokacin nasu’ da kuma ikon yin sa daga gare su
yana nan’ amma kuma babu Wanda ya yi shi daga cikinsu,
to lalle wannan abin babu ta yadda za a yi ya zamanto
addini karbabbe a wurin na bayansu har zuwa tashin Kiyama.
Yan’uwa Musulmi! Lalle shi rikon ranar maulidi a matsayin
Idi, da maida shi ranar buki, ba a fara yin shi ba cikin
wannan Al’umma sai cikin karni na hudu na hijirar Annabi
Mai tsira da amincin Allah’ watau sai a cikin shekara ta
dari uku da settin da biyu (362). Sannan mutumin da ya fara
yin wannan buki na maulidi shi ne wani sarki dan Shi’ah
Fadimiyyah Mai suna Almu’izzu li Dininl Lah a garin
Alkahira’ kamar yadda yake rubuce cikin littattafan Musulunci
da tarihi, da wasunsu, kuna iya duba wadannan littattafan:-
ﺍﻟﻤﻮﺍﻋﻆ ﻭﺍﻻﻋﺘﺒﺎﺭ ﺑﺬﻛﺮ ﺍﻟﺨﻄﻂ ﻭﺍﻻﺛﺎﺭ ﻟﻠﻤﻘﺮﻳﺰﻱ ١ / ٤٩٠، ﻭﺻﺒﺢ
ﺍﻷﻋﺸﻰ ﻓﻲ ﺻﻨﺎﻋﺔ ﺍﻹﻧﺸﺎﺀ ﻟﻠﻘﻠﻘﺸﻨﺪﻱ ٣ / ٤٩٨، ﻭﺗﺎﺭﻳﺦ ﺍﻻﺣﺘﻔﺎﻝ
ﺑﺎﻟﻤﻮﻟﺪ ﺍﻟﻨﺒﻮﻱ ﻟﻠﺴﻨﺪﻭﺑﻲ ﺹ٦٩، ﻭﺃﺣﺴﻦ ﺍﻟﻜﻼﻡ ﻓﻴﻤﺎ ﻳﺘﻌﻠﻖ ﺑﺎﻟﺴﻨﺔ
ﻭﺍﻟﺒﺪﻋﺔ ﻣﻦ ﺍﻷﺣﻜﺎﻡ ﻟﻤﺤﻤﺪ ﺑﺨﻴﺖ ﺹ٤٤، ٤٥، ﻭﺍﻟﻤﺤﺎﺿﺮﺍﺕ ﺍﻟﻔﻜﺮﻳﺔ
ﻟﻠﺸﻴﺦ ﻋﻠﻲ ﻓﻜﺮﻱ ﺹ٨٤، ﻭﺍﻹﺑﺪﺍﻉ ﻓﻲ ﻣﻀﺎﺭ ﺍﻻﺑﺘﺪﺍﻉ ﻟﻠﺸﻴﺦ ﻋﻠﻲ
ﻣﺤﻔﻮﻅ ﺹ١٢٦، ﻭﺍﻟﺘﺎﺭﻳﺦ ﺍﻟﻌﺒﺎﺳﻲ ﻭﺍﻟﻔﺎﻃﻤﻲ ﻟﻠﺸﻴﺦ ﺍﺣﻤﺪ ﻣﺨﺘﺎﺭ ﺍﻟﻌﺒﺎﺩﻱ
ﺹ٢٦١، ٢٦٢ .
Almawaa’izu wa Litibaar na Maqriizii 1/490, da Subhul
A’ashaa na Qalqashandii 3/498, da Taariikhu Lihtifaali Bil
Maulidin Nabawii na Sanduubii shafi na 69, da Ahsanul Kalam
fi ma yataallaqu bis Sunnati wal Bidi’ati minal Ahkam na
Muhammad Bakhiit shafi na 44,45, da Almuhadharaatul
Fikriyyah na Ali Fikrii shafi na 84, da Al’ibdaa fi Madharri
Libtidaa na Ali Mahfuuz shafi na 126, da Taarikhul Abbaasii
wal Faatimii na Ahmad Mukhtaar Al’abbadii shafi na
261,262.

_#DR,JALO JALINGO_l

*_Gabatarwa_*:- Yusuf Ja'afar Kura 

*MIFTAHUL Ilmi*
WhatsApp

→ ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren *MIFTAHUL ILMI* whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu *(07036073248)* ta ‎whatsApp.
Post a Comment (0)