_*π°π€΅ MUHIMMANCIN YIN ADDU'A YAYIN SADUWA DA IYALI π°π€΅*_
Ψ¨Ψ³Ω Ψ§ΩΩΩ Ψ±ΨΩ Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ .
_*πΉ Ya ku Ma'aurata, ku dinga yin “Addu'ar Saduwa da Iyali” kafin fara Yin Jima'i don ku tsare 'ya'yanku daga fadawa cikin fitina da bala'i πΉ*_
_πΉ Da farko ina mai bada haquri na yin posting akan wannan darasi. Amma abin yana ci min tuwo a kwarya sosai wlh, domin kuwa sai bayan iyaye sun haifi kangararrun yara, sai su zo suna neman Addu'ar mutane wanda tun farko sune ya ka mata su yi addu'ar don tsare 'ya'yan su daga fadawa halaka._
_πΉ Sau dayawa Ma'aurata wadanda suka jima suna Buqatar juna (sababbin ma'aurata) sukan fadawa juna ne kawai kai tsaye, ko suyi kan gado, ba tare da tuna yin “Addu'ar saduwa da iyali ba” saboda wancen rudun na buqata dake cikin zukatansu. A wannan lokacin ne kuma Shaidan πΊ yake samun dama don ya cutar da yaran da zaku haifa._
_πΉ To amma Dan Da aka haifa matuqar anyi wannan addu'ar kafin saduwa Shaidan πΊ ba zai taba cutar dashi ba har abada bisa nassi na hadisin Manzon Allah (SAW) wanda Bukhari ya bude masa babi guda a cikin babban littafinsa mai albarka, hadisin abbas da ya ke cewa: π_
_ΨΉΩ Ψ§Ψ¨Ω ΨΉΨ¨Ψ§Ψ³ Ψ±ΨΆΩ Ψ§ΩΩΩ ΨΉΩΩΩ Ψ§ ΩΨ§Ω: ΩΨ§Ω Ψ§ΩΩΨ¨Ω Ψ΅ΩΩ Ψ§ΩΩΩ ΨΉΩΩΩ ΩΨ³ΩΩ : *(ΩΩ Ψ£Ω Ψ£ΨΨ―ΩΩ Ψ₯Ψ°Ψ§ Ψ£Ψ±Ψ§Ψ― Ψ£Ω ΩΨ£ΨͺΩ Ψ£ΩΩΩ ΩΨ§Ω: Ψ¨Ψ§Ψ³Ω Ψ§ΩΩΩ، Ψ§ΩΩΩΩ Ψ¬ΩΨ¨ΩΨ§ Ψ§ΩΨ΄ΩΨ·Ψ§Ω، ΩΨ¬ΩΨ¨ Ψ§ΩΨ΄ΩΨ·Ψ§Ω Ω Ψ§ Ψ±Ψ²ΩΨͺΩΨ§، ΩΨ₯ΩΩ Ψ₯Ω ΩΩΨ―Ψ± Ψ¨ΩΩΩΩ Ψ§ ΩΩΨ― ΩΩ Ψ°ΩΩ ΩΩ ΩΨΆΨ±Ω Ψ΄ΩΨ·Ψ§Ω Ψ£Ψ¨Ψ―Ψ§ً)* [Ψ±:141]_
_πΉ Daga ibn Abbas (RA) Ya ce: Manzon Allah (SAW) ya ce: *"Idan dayan ku yaso ya je wa iyalinsa to yace: Da Sunan Allah, Ya Allah! Ka nisantar da shaidan daga gare mu, kuma ka nisantar da shaidan daga abin da Ka azurta mu da shi."* Manzon Allah yace: Duk wanda yayi wannan addu'ar kuma matar ta dauki ciki a wannan daren, to shaidan ba zai taba cutar da abin da suka samu ba. Muslim ma ya fitar dashi a hadisi mai lamba ta 2/1028._
_πΉ *NOTE:* Idan ba'a karanta wannan addu'ar ba, to Lokacin da maniyyin namijin yake shiga cikin matar yana haduwa da maniyyin shaidan πΊ ne. Shiyasa sai ku haifi yaro shedani, ashe iyayensa biyu ne, da shaidan da babansa na ainihi, sai yayi ta fita yar ya zamewa mutane bala'i da annoba!_
_πΉ Shiyasa Manzon Allah (Sallallahu alayhi wa sallam) ya ce: *“Duk wanda ya karanta wannan addu'ar sannan matarsa ta samu ciki a wannan daren, to Shaidan πΊ ba zai taba cutar da wannan yaron ba.”*_
_πΉ Idan kuna yawan yin wannan addu'ar to Alhamdulilah kun tsare kanku da 'Ya'yanku, sai ku haifi hafizan Qur'ani, amma idan bakwa yi to, ku dena zuwa kuna cewa malamai su yi muku addu'a, ko a baku rubutu ko basu, domin kuwa Babansu Shaidan πΊ yana nan. Amma sai a kiyaye a dinga yi daga yau don a kare masu zuwa gaba._
_*πΉ Allah ya sa mu dace, ya tsare mu da 'Ya'yan mu baki daya daga fitinar Shaidan πΉ*_
✍ *πΉ Abdullah A Abdullah Abu Khadija Assalafeey (Ψ£ΩΨ΅Ψ§Ψ± Ψ§ΩΨ³ΩΨ©) πΉ*
09/11/2018