*≈≈ MAULIDI A MAHANGAR MUSULUNCI [2]*
_(kashi na Biyu)_
★_MALUMAN MUSULUNCI DABAN DABAN SUN HANA YIN BUKIN
MAULIDI
Yan’uwa Musulmi! Lalle da yawa daga cikin maluman
Musulunci sun gargadi Al’umma sun hana su yin bukin
maulidi da rikon shi a matsayin wata ibadah da za a nemi
lada wurin Allah da ita, kuma sun bayyanar da cewa yin
bukin maulidi bidi’a ce kuma bata.
Daga cikin wadannan malamai akwai manya manyan
malumanmu na mazhabar Malikiyyah, kamar Ibnul Hajj wanda
ya rasu a shekarar hijira ta 732 watau yau da rasuwarsa
shekaru 702 ke nan da suka wuce, da kuma Umarul
Faakihaanii wanda ya rasu a shekarar hijira ta 734 watau yau
da mutuwarsa shekara 700 ke nan da suka wuce, da kuma
Ibraahimush Shaatibii wanda ya rasu a shekarar hijira ta 690
watau yau da rasuwarsa shekara 744 ke nan da suka wuce,
da kuma uwa-uba Sheik Uthmanu Dan Fodiyo wanda ya rasu
a shekarar hijira ta 1234 watau yau shekara 201 ke nan da
rasuwarsa.
Amma Sheik Ibnul Hajj ga abin da yake cewa cikin littafin
Almudkhal 2/2, da 2/10-11 :-
(( ﻭﻣﻦ ﺟﻤﻠﺔ ﻣﺎ ﺍﺣﺪﺛﻮﻩ ﻣﻦ ﺍﻟﺒﺪﻉ ﻣﻊ ﺍﻋﺘﻘﺎﺩﻫﻢ ﺍﻥ ﺫﻟﻚ ﻣﻦ ﺍﻛﺒﺮ
ﺍﻟﻌﺒﺎﺩﺍﺕ ﻭﺍﻇﻬﺮ ﺍﻟﺸﻌﺎﺋﺮ ﻣﺎ ﻳﻔﻌﻠﻮﻧﻪ ﻓﻲ ﺷﻬﺮ ﺭﺑﻴﻊ ﺍﻻﻭﻝ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﻭﻗﺪ
ﺍﺣﺘﻮﻯ ﻋﻠﻰ ﺑﺪﻉ ﻭﻣﺤﺮﻣﺎﺕ ﺟﻤﻠﺔ ﻓﻤﻦ ﺫﻟﻚ ﺍﺳﺘﻌﻤﺎﻟﻬﻢ ﺍﻟﻤﻐﺎﻧﻲ ﻭﻣﻌﻬﻢ
ﺁﻻﺕ ﺍﻟﻄﺮﺏ (( ﺍﻟﻰ ﺍﻥ ﻗﺎﻝ: )) ﻭﺍﻥ ﺧﻼ ﻣﻨﻪ ﻭﻋﻤﻞ ﻃﻌﺎﻣﺎ ﻓﻘﻂ ﻭﻧﻮﻯ
ﺑﻪ ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﻭﺩﻋﺎ ﺍﻟﻴﻪ ﺍﻻﺧﻮﺍﻥ ﻭﺳﻠﻢ ﻣﻦ ﻛﻞ ﻣﺎ ﺗﻘﺪﻡ ﺫﻛﺮﻩ ﻓﻬﻮ ﺑﺪﻋﺔ
ﺑﻨﻔﺲ ﻧﻴﺘﻪ ﻓﻘﻂ ﺇﺫ ﺍﻥ ﺫﻟﻚ ﺯﻳﺎﺩﺓ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﻭﻟﻴﺲ ﻣﻦ ﻋﻤﻞ ﺍﻟﺴﻠﻒ
ﺍﻟﻤﺎﺿﻴﻦ ﻭﺍﺗﺒﺎﻉ ﺍﻟﺴﻠﻒ ﺍﻭﻟﻰ ﺑﻞ ﺃﻭﺟﺐ ﻣﻦ ﺍﻥ ﻳﺰﻳﺪ ﻧﻴﺔ ﻣﺨﺎﻟﻔﺔ ﻟﻤﺎ
ﻛﺎﻧﻮﺍ ﻋﻠﻴﻪ ﻷﻧﻬﻢ ﺍﺷﺪ ﺍﺗﺒﺎﻋﺎ ﻟﺴﻨﺔ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ﻭﺗﻌﻈﻴﻤﺎ ﻟﻪ ﻭﺳﻨﺘﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﻟﻬﻢ ﻗﺪﻡ ﺍﻟﺴﺒﻖ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺒﺎﺩﺭﺓ
ﺍﻟﻰ ﺫﻟﻚ ﻭﻟﻢ ﻳﻨﻘﻞ ﻋﻦ ﺍﺣﺪ ﻣﻨﻬﻢ ﺍﻧﻪ ﻧﻮﻯ ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﻭﻧﺤﻦ ﻟﻬﻢ ﺗﺒﻊ
ﻓﻴﺴﻌﻨﺎ ﻣﺎ ﻭﺳﻌﻬﻢ )).
Ma’ana: ((Yana daga cikin jumlar abin da suka kirkira na
bidi’o’i tare da akidar cewa hakan yana daga cikin manyan
ibadodi, kuma yana daga cikin alamomin Musulunci mafi fita
fili: abin nan da suke aikatawa cikin watan Rabii’ul Awwal
na bukin maulidi. Shi dai maulidi ya tattari abubuwan haramun
da yawa a dunkule, daga cikinsu akwai wake-wake da suke
yi tare da Kayan kade-kade …. To amma idan yin maulidi
ya wifinta daga yin wake-wake tare da kayan kade-kade mai
yin maulidin ya yi abinci kawai ya yi nufin maulidi da shi
ya kira yan’uwa zuwa cin abincin, to, yin hakan ya zama
bidi’ah saboda niyyar maulidin da ya yi, domin niyyar
maulidin kari ne a cikin Addini ba ya kuma daga cikin
ayyukan Salaf Magabata ba, bin Magabata kuwa shi ne ya fi
dacewa, kai shi ne ma wajibi da a ce mutum zai kara wani
abu sabanin abin da suka kasance a kansa, domin su Magabata
su ne suka fi kowa yin koyi da Manzon Allah, kuma su ne
suka fi kowa girmama shi da girmama sunnarsa, kuma su suke
da kafar rigaya wajen takawa zuwa ga abin da yake alheri ne,
babu kuma mutum daya da ya ciro yin niyyar maulidi daga
dayansu, mu kuwa sauran Musulmi mabiya ne gare su, dukkan
abin da ya wadatar da su na addini shi ne zai wadatar da
mu)).
Sannan Imamul Faakihaanii ya ce cikin Risalarsa ta maulidi
mai suna Almurid fil Kalaami alaa Hukmil Maulid :-
(( ﻻ ﺍﻋﻠﻢ ﻟﻬﺬﺍ ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﺍﺻﻼ ﻓﻲ ﻛﺘﺎﺏ ﻭﻻ ﺳﻨﺔ ﻭﻻ ﻳﻨﻘﻞ ﻋﻤﻠﻪ ﻋﻦ ﺍﺣﺪ
ﻣﻦ ﻋﻠﻤﺎﺀ ﺍﻻﻣﺔ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻫﻢ ﺍﻟﻘﺪﻭﺓ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﺍﻟﻤﺘﻤﺴﻜﻮﻥ ﺑﺂﺛﺎﺭ ﺍﻟﻤﺘﻘﺪﻣﻴﻦ
ﺑﻞ ﻫﻮ ﺑﺪﻋﺔ ﺍﺣﺪﺛﻬﺎ ﺍﻟﺒﻄﺎﻟﻮﻥ ﻭﺷﻬﻮﺓ ﻧﻔﺲ ﺍﻋﺘﻨﻰ ﺑﻬﺎ ﺍﻻﻛﺎﻟﻮﻥ ﺑﺪﻟﻴﻞ
ﺍﻧﺎ ﺍﺫﺍ ﺃﺩﺭﻧﺎ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻷﺣﻜﺎﻡ ﺍﻟﺨﻤﺴﺔ ﻗﻠﻨﺎ ﺍﻣﺎ ﺍﻥ ﻳﻜﻮﻥ ﻭﺍﺟﺒﺎ ﺍﻭ ﻣﻨﺪﻭﺑﺎ
ﺍﻭ ﻣﺒﺎﺣﺎ ﺍﻭ ﻣﻜﺮﻭﻫﺎ ﺍﻭ ﻣﺤﺮﻣﺎ ﻭﻫﻮ ﻟﻴﺲ ﺑﻮﺍﺟﺐ ﺇﺟﻤﺎﻋﺎ ﻭﻻ ﺑﻤﻨﺪﻭﺏ
ﻻﻥ ﺣﻘﻴﻘﺔ ﺍﻟﻤﻨﺪﻭﺏ ﻣﺎ ﻃﻠﺒﻪ ﺍﻟﺸﺮﻉ ﻣﻦ ﻏﻴﺮ ﺫﻡ ﻋﻠﻰ ﺗﺮﻛﻪ ﻭﻫﺬﺍ ﻟﻢ
ﻳﺄﺫﻥ ﻓﻴﻪ ﺍﻟﺸﺮﻉ ﻭﻻ ﻓﻌﻠﻪ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ ﻭﻻ ﺍﻟﺘﺎﺑﻌﻮﻥ ﻭﻻ ﺍﻟﻌﻠﻤﺎﺀ ﺍﻟﻤﺘﺪﻳﻨﻮﻥ
ﻓﻴﻤﺎ ﻋﻠﻤﺖ ﻭﻫﺬﺍ ﺟﻮﺍﺑﻲ ﻋﻨﻪ ﺑﻴﻦ ﻳﺪﻱ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻥ ﻋﻨﻪ ﺳﺌﻠﺖ ﻭﻻ ﺟﺎﺋﺰ
ﺍﻥ ﻳﻜﻮﻥ ﻣﺒﺎﺣﺎ ﻻﻥ ﺍﻻﺑﺘﺪﺍﻉ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﻟﻴﺲ ﻣﺒﺎﺣﺎ ﺑﺈﺟﻤﺎﻉ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ
ﻓﻠﻢ ﻳﺒﻖ ﺍﻻ ﺍﻥ ﻳﻜﻮﻥ ﻣﻜﺮﻭﻫﺎ ﺍﻭ ﺣﺮﺍﻣﺎ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Ban san wata hujja da za ta halatta yin maulidi
ba a cikin Alkur’ani da Sunnah, kuma ba a nakalto yin bukin
maulidi koda daga mutum daya ba cikin maluman Al’umma
wadanda su ne abin koyi a cikin Addini , kuma su ne ke
riko da maganganun magabata, kai, abin da dai yake ciki shi
ne: shi dai maulidi wata biri’ah ce da marasa aikin yi suka
kirkira kuma sha’awar son rai ce da masu cin dukiyar mutane
cikin karya suka runguma, saboda shi dai bukin maulidi idan
muka shimfida shi a kan hukunce-hukuncin nan guda biyar sai
mu ce: ko dai ya zama wajibi, ko kuwa ya zama
mustahabbi, ko kuwa ya zama mubaahi, ko kuwa ya zama
makruuhi, ko kuwa ya zama haraamun, to in mun yi hakan za
mu ga cewa shi dai ba wajibi ba ne bisa Ijmaa’in Malamai,
shi kuwa ba mustahabbi ba ne domin abin da ake nufi da
mustahabbi shi ne abin da Shari’ah ta ce a yi ba tare da an
zargi Wanda ya ki yi ba, shi kuwa maulidi Shari’ah ba ta
ce a yi shi ba, kuma ni a sanina Sahabbai, da Taabi’ai, da
malamai masu riko da Addini ba su yi shi ba, wannan shi
ne jawabina a gaban Allah a kan bukin maulidi in har aka
tambaye ni. Kuma ba zai halatta ba a ce Maulidi ya zama
mubaahi saboda kirkiran wani abu cikin addini ba zai zama
mubaahi ba a bisa Ijmaa’in Musulmi, saboda haka babu abin
da ya rage face maulidi ya zama makruuhi ko kuwa
haramun)). Intaha.
Sannan Imamush Shaatibii ya ce -a lokacin da yake yin
bayanin ma’anar bidi’ah- cikin littafinsa mai suna Alitisam
1/50,53 :-
(( ﻋﺒﺎﺭﺓ ﻋﻦ ﻃﺮﻳﻘﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﻣﺨﺘﺮﻋﺔ ﺗﻀﺎﻫﻲ ﺍﻟﺸﺮﻋﻴﺔ ﻳﻘﺼﺪ ﺑﺎﻟﺴﻠﻮﻙ
ﻋﻠﻴﻬﺎ ﺍﻟﻤﺒﺎﻟﻐﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﺘﻌﺒﺪ ﻟﻠﻪ ﺳﺒﺤﺎﻧﻪ .… ﻳﻌﻨﻲ ﺍﻧﻬﺎ ﺗﺸﺎﺑﻪ ﺍﻟﻄﺮﻳﻘﺔ
ﺍﻟﺸﺮﻋﻴﺔ ﻣﻦ ﻏﻴﺮ ﺍﻥ ﺗﻜﻮﻥ ﻓﻲ ﺍﻟﺤﻘﻴﻘﺔ ﻛﺬﻟﻚ ﺑﻞ ﻫﻲ ﻣﻀﺎﺩﺓ ﻟﻬﺎ ﻣﻦ
ﺃﻭﺟﻪ ﻣﺘﻌﺪﺩﺓ .… ﻣﻨﻬﺎ ﺍﻟﺘﺰﺍﻡ ﺍﻟﻜﻴﻔﻴﺎﺕ ﻭﺍﻟﻬﻴﺌﺎﺕ ﺍﻟﻤﻌﻴﻨﺔ ﻛﺎﻟﺬﻛﺮ ﺑﻬﻴﺌﺔ
ﺍﻻﺟﺘﻤﺎﻉ ﻋﻠﻰ ﺻﻮﺕ ﻭﺍﺣﺪ ﻭﺍﺗﺨﺎﺫ ﻳﻮﻡ ﻭﻻﺩﺓ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ ﻋﻴﺪﺍ ﻭﻣﺎ ﺃﺷﺒﻪ ﺫﻟﻚ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Bidi’ah wata kirkirarriyar hanya ce cikin addini
mai kama da addinin gaskiya ana nufin kaiwa matuka matuka
cikin bautar Allah da yin ta .., ina nufin ita bidi’ah tana
kama da hanyar Shari’ah ba tare da ta kasance hanyar
Shari’ah ta hakika ba, kai a gaskiya ma tana karo ne da
hanyar Shari’ah ta fiskoki da yawa … Daga cikinsu akwai
lazimtar wasu irin siffofi ayyanannu, kamar zikirin da ake yi
a bisa tsarin haduwa a kan sauti daya’ da kuma rikon ranar
haihuwar Manzon Allah mai tsira da amincin Allah a matsayin
idi, da abin da yake Kama da haka)).
Sannan Shehu Uthmanu Dan Fodiyo ya ce cikin littafinsa mai
suna Ihyaaus Sunnah wa Iqmaadul Bid’ah shafi na 104 :-
(( ﻓﺎﻥ ﻗﻠﺖ ﻣﺎ ﺣﻜﻢ ﻣﺎ ﻳﻔﻌﻞ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﻲ ﺷﻬﺮ ﺭﺑﻴﻊ ﺍﻻﻭﻝ ﻓﻲ ﻳﻮﻡ
ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﺍﻭ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﺍﻟﺴﺎﺑﻊ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﻣﻦ ﺍﺟﺘﻤﺎﻉ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻟﻠﺬﻛﺮ ﻭﺍﻟﻄﻌﺎﻡ ﺍﻟﺬﻱ
ﻳﻌﻤﻠﻮﻧﻪ ﻟﺬﻟﻚ؟ ﻗﻠﺖ: ﺍﻧﻪ ﺑﺪﻋﺔ ﻣﻜﺮﻭﻫﺔ ﺍﻥ ﺧﻼ ﻋﻦ ﻛﻞ ﻣﻌﺼﻴﺔ .
ﻭﻗﻴﻞ : ﺍﻥ ﺍﻟﺼﻮﺍﺏ ﺍﻥ ﻋﻤﻞ ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﺍﻟﺸﺮﻳﻒ ﺍﻟﻨﺒﻮﻱ ﻣﻦ ﺍﻟﺒﺪﻉ ﺍﻟﺤﺴﻨﺔ
ﺍﻟﻤﻨﺪﻭﺑﺔ ﺍﺫﺍ ﺧﻼ ﻋﻦ ﻣﻌﺼﻴﺔ . ﻭﺃﻣﺎ ﻣﺎ ﻳﻌﺘﺎﺩﻩ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﻲ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﺰﻣﺎﻥ
ﻓﻲ ﺫﻟﻚ ﻣﻦ ﺍﺧﺘﻼﻁ ﺍﻟﺮﺟﺎﻝ ﻭﺍﻟﻨﺴﺎﺀ ﻓﻤﻌﺎﺫ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻥ ﻳﻘﻮﻝ ﺍﺣﺪ
ﺑﺠﻮﺍﺯﻩ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Idan ka ce: Mene ne hukuncin abin da mutane
suke yi a cikin watan Rabii’ul Awwal a ranar maulidi ko
kuwa a ranar bakwai ga maulidi na taruwar jama’a saboda
yin zikiri da cin abincin da aka yi tanadinsa saboda hakan?
Sai in ce: Wannan bidi’ah ce makruuhiyah in yin maulidin
ya wofinta daga dukkan sabon Allah. Amma kuma wasu sun
ce: Abin da yake daidai shi ne shi bukin maulidin Annabi
yana daga cikin bidi’o’i masu kyau matukar dai ya wofinta
daga ko wane sabon Allah. To amma abin da mutane suka
Saba yin shi a maulidi a wannan zamani na cakuda tsakanin
maza da mata a’uuzu billahi da wani mutum zai ce halal
ne)).
Wannan shi ne abin da malumanmu na mazhabar Malikiyyah
suka fada game da bukin maulidi.
Sannan Shaikhul Islam Ibnu Taimiyah wanda ya rasu a shekarar
hijira ta 728 watau shekaru 706 ke nan da suka wuce shi ya
yi maganar maulidi ya kuma tabbatar da cewa maulidi bidi’ah
ce, ya rubuta cikin littafinsa mai suna Iqtidhaa’us Siraa’til
Mustaqiim 2/123-124 :-
(( ﻭﻛﺬﻟﻚ ﻣﺎ ﻳﺤﺪﺛﻪ ﺑﻌﺾ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺍﻣﺎ ﻣﻀﺎﻫﺎﺓ ﻟﻠﻨﺼﺎﺭﻯ ﻓﻲ ﻣﻴﻼﺩ
ﻋﻴﺴﻰ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻭﺍﻣﺎ ﻣﺤﺒﺔ ﻟﻠﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﺗﻌﻈﻴﻤﺎ
ﻭﺍﻟﻠﻪ ﻗﺪ ﻳﺜﻴﺒﻬﻢ ﻋﻠﻰ ﻫﺬﻩ ﺍﻟﻤﺤﺒﺔ ﻭﺍﻻﺟﺘﻬﺎﺩ ﻻ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺒﺪﻉ ﻣﻦ ﺍﺗﺨﺎﺫ
ﻣﻮﻟﺪ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻋﻴﺪﺍ ﻣﻊ ﺍﺧﺘﻼﻑ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﻲ ﻣﻮﻟﺪﻩ
ﻓﺎﻥ ﻫﺬﺍ ﻟﻢ ﻳﻔﻌﻠﻪ ﺍﻟﺴﻠﻒ ﻣﻊ ﻗﻴﺎﻡ ﺍﻟﻤﻘﺘﻀﻲ ﻟﻪ ﻭﻋﺪﻡ ﺍﻟﻤﺎﻧﻊ ﻣﻨﻪ ﻟﻮ
ﻛﺎﻥ ﺧﻴﺮﺍ ﻭﻟﻮ ﻛﺎﻥ ﻫﺬﺍ ﺧﻴﺮﺍ ﻣﺤﻀﺎ ﺍﻭ ﺭﺍﺟﺤﺎ ﻟﻜﺎﻥ ﺍﻟﺴﻠﻒ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻨﻬﻢ ﺍﺣﻖ ﺑﻪ ﻣﻨﺎ ﻓﺎﻧﻬﻢ ﻛﺎﻧﻮﺍ ﺍﺷﺪ ﻣﺤﺒﺔ ﻟﺮﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ ﻭﺗﻌﻈﻴﻤﺎ ﻟﻪ ﻣﻨﺎ ﻭﻫﻢ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺨﻴﺮ ﺍﺣﺮﺹ ﻭﺍﻧﻤﺎ ﻛﻤﺎﻝ ﻣﺤﺒﺘﻪ
ﻭﺗﻌﻈﻴﻤﻪ ﻓﻲ ﻣﺘﺎﺑﻌﺘﻪ ﻭﻃﺎﻋﺘﻪ ﻭﺍﺗﺒﺎﻉ ﺃﻣﺮﻩ ﻭﺇﺣﻴﺎﺀ ﺳﻨﺘﻪ ﺑﺎﻃﻨﺎ ﻭﻇﺎﻫﺮﺍ
ﻭﻧﺸﺮ ﻣﺎ ﺑﻌﺚ . ﺑﻪ ﻭﺍﻟﺠﻬﺎﺩ ﻋﻠﻰ ﺫﻟﻚ ﺑﺎﻟﻘﻠﺐ ﻭﺍﻟﻴﺪ ﻭﺍﻟﻠﺴﺎﻥ ﻓﺎﻥ ﻫﺬﻩ
ﻃﺮﻳﻘﺔ ﺍﻟﺴﺎﺑﻘﻴﻦ ﺍﻷﻭﻟﻴﻦ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻬﺎﺟﺮﻳﻦ ﻭﺍﻷﻧﺼﺎﺭ ﻭﺍﻟﺬﻳﻦ ﺍﺗﺒﻌﻮﻫﻢ
ﺑﺈﺣﺴﺎﻥ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Haka nan abin da sashin mutane ke kirkira ko dai
saboda koyi da Kiristoci cikin bukin Kirsimeti’ ko kuwa
saboda son Annabi mai tsira da amincin Allah da girmama
shi, zai yiwu Allah ya ba su lada a kan nuna kokari da
soyayya’ amma ba zai ba su lada a kan bidi’o’in rikon
maulidin Annabi mai tsira da amincin Allah a matsayin idi ba
duk da yake ma masu tarihi sun yi sabani a kan wace rana
ce da wani wata ne aka haife shi! Shi dai bukin maulidi babu
wani daga cikin magabata da ya yi shi duk kuwa da cewa
dukkan dalilan da ake bayarwa na yin bukin a yanzu akwai su
a wancan lokacin ma, kuma babu wani abu da zai hana su
yin bukin inda yin shi alheri ne.
Lalle ne da yin bukin
maulidi tsantsar alheri ne to da Salaf Magabata su suka fi
cancantar yin sa a kanmu, saboda sun fi mu son Manzon
Allah mai tsira da amincin Allah da girmama shi, kuma sun
fi kowa son aikata alheri. Lalle cikar soyayya da girmamawa
ga Annabi tana cikin bin shi ne da yi masa da’ah da bin
umurnin shi, da raya sunnar shi ciki da waje, da yada abin
da aka aiko da shi, da yin jihadi da zuciya, da hannu, da
harshe a kan hakan wannan ita ce hanyar Magabata na farko
daga cikin Muhajirai da Ansarawa da wadanda suka bi su da
kyautayi)).
Yan’uwa Musulmi! Wannan shi ne matsayin bukin maulidi
daga bakunan wadannan gagga-gaggan maluman Musulunci, tare
ma kuma da cewa Maluman tarihi da siiirah sun yi sabani
game da ranar haihuwar shi Annabi mai tsira da amincin
Allah, a inda wasu suka ce:
1- An haife shi ne a ran biyu ga watan Rabii’ul Awwal.
2- Wasu kuwa suka ce an haife shi ne a ran takwas ga
watan Rabii’ul Awwal.
3- Wasu kuwa suka ce an haife shi ne a ran goma ga watan
Rabii’ul Awwal.
4- Wasu kuwa suka ce an haife shi ne a ran goma sha
biyumga watan Rabii’ul Awwal.
5- wasu kuwa suka ce an haife shi ne a ran goma sha
bakwai ga watan Rabii’ul Awwal.
6- Wasu kuwa suka ce an haife shi ne a ran ashrin ga watan
Rabii’ul Awwal.
7- Wasu kuwa suka ce an haife shi ne a ran goma sha biyu
ga watan Ramadhan.
Domin ganin wannan sabanin sai ku dubi littafin Taariikhul
Islam na Imamuz Zahbii a Juz’in Siirah shafi na 25-27, da
kuma littafin Albidaayatu wan Nihaayatu na Alhaafiz Ibnu
Katheer 2/662.
Yan’uwa Musulmi! Kauli daidai har bakwai a kan ranar
haihuwar Annabi mai tsira da amincin Allah babu kuma wani
wanda ya isa ya ce: wannan kauli shi ne hakikanin gaskiya
wancan kaulin kuma ba gaskiy ba ne, saboda abu ne da ya
faru kafin zuwan Musulunci kuma bayan shi Musulunci ya zo
bai tabbatar da ranar haihuwar ba ta hanyar wahayi saboda
rashin muhimmancin yin hakan a cikin Addini.
Ke nan ware wata rana daga cikin ranakun nan da aka ambata
da riyawar cewa ita ce ranar da aka haifi Manzon Allah mai
tsira da amincin Allah akwai nau’i na karya da shedan zur a
cikin yin hakan. Allah ya tsare mu da son zuciya.
Wannan shi ne kashi na farko game da bayananmu a kan bukin
maulidi, kashi biyu na tafe in sha Allahu Ta’ala, kuma zai
yi bayani ne game da shubuhohin da yan bidi’ah ke
ambatawa domin tabbatar da bidi’ar maulidi.
Allah Ya nuna mana gaskiya gaskiya ce ya ba mu ikon bin ta
Ya kuma nuna mana karya karya ce Ya ba mu ikon kin ta.
Ameen.
_#DR,JALO JALINGO_
*_Gabatarwa_*:- Yusuf Ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL Ilmi*
WhatsApp
→ Ga ma su sha'awar shiga Zauren *MIFTAHUL ILMI* whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu *(07036073248)* ta whatsApp.