MAULIDI A MAHANGAR MUSULUNCI 3

*MAULIDI A MAHANGAR MUSULUNCI [ 3 ]*

_(Kashi na Uku)_

Akwai shubuhohin da masu shar’anta Idin maulidi 

ambatawa a matsayin hujjojin da ke wajabta Idin maulidi ko
halatta shi, saboda haka In sha Allahu Ta’ala za mu ambaci
uku daga cikinsu a wannan rubutu namu (kashi na 2) sannan
mu ba da amsarsu, saboda burin da muke da shi na tsarkake
addinin Musulunci daga wannan bidi’ah mai kama da bidi’ar
Kirsimeti wacce Kiristoci ke yi cikin ko wace shekara, haka
nan saboda burinmu na dukkanmu al’ummar Musulmi mu gudu
tare mu tsira tare.
(( ﻻ ﻳﺆﻣﻦ ﺍﺣﺪﻛﻢ ﺣﺘﻰ ﻳﺤﺐ ﻻﺧﻴﻪ ﻣﺎ ﻳﺤﺐ ﻟﻨﻔﺴﻪ )).


★ SHUBUHA TA FARKO:

Shubuha ta farko: Suka ce: Allah ne da kansa Ya yi umurni
da yin bukin Idin maulidi cikin Suratu Yunus aya ta 58 a inda
ya ce:-
{ ﻗﻞ ﺑﻔﻀﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺑﺮﺣﻤﺘﻪ ﻓﺒﺬﻟﻚ ﻓﻠﻴﻔﺮﺣﻮﺍ ﻫﻮ ﺧﻴﺮ ﻣﻤﺎ ﻳﺠﻤﻌﻮﻥ }.
Ma’ana: {Ka ce: Ku yi farin ciki da falalar Allah da
rahamarSa shi ne mafi alheri daga abin da suke tarawa}.
Suka ce: Annabi shi ne falalar Allah da rahamarSa, Allah
kuwa Ya ce a yi farin ciki da falalarSa da kuma rahamarSa,
farin cikin kuwa yana nufin shirya bukin maulidinsa ne ahi
Annabi mai tsira da amincin Allah, ke nan shirya bukin
maulidi ko wace shekara bin wani umurni ne na musamman
Wanda ya fito daga Allah madaukakin Sarki, rashin bin
wannan umurni kuwa lalle saba wa Shi Allah Madaukakin Sarki
ne!!!
Amsa a kan wannan shubuha tana da rassa da yawa:-


Na farko: sai a ce da su: Fassara wannan ayar da cewa tana
umurni ne da yin bukin maulidi fassara ce da take Kama da
fassarar Baatiniyyah da gulaatus suufiyyah da suke yi wa wasu
nassoshin Alkur’ani mai girma, kamar yadda suka fassara
ayah ta 25 cikin Suratu Nuuhin inda Allah Yake magana game
da mutanen Annabi Nuhu Ya ce:-
{ ﻣﻤﺎ ﺧﻄﻴﺌﺎﺗﻬﻢ ﺃﻏﺮﻗﻮﺍ ﻓﺄﺩﺧﻠﻮﺍ ﻧﺎﺭﺍ ﻓﻠﻢ ﻳﺠﺪﻭﺍ ﻟﻬﻢ ﻣﻦ ﺩﻭﻥ ﺍﻟﻠﻪ
ﺃﻧﺼﺎﺭﺍ }.
Ma’ana: {Saboda laifukansu na ganganci aka nitsar da su
(cikin ruwa) sannan aka sanya su a Wuta. Saboda haka ba su
sama wa kansu wanin Allah a matsayin Mai taimako ba}.
Sai suka ce: ma’anar ayar ita ce: Allah Yana nufin cewa
abin nan da suka yi wa Annabi Nuhu na saba wa umurnin da
Allah ya aiko shi da shi shi ne ya Kai su ga yin nitso cikin
tekunan sanin Allah! Watau dai abin nan da suka yi na saba
wa Annabi Nuhu babu wani zunubi a cikinsa kamar yadda wasu
ke tsammani!!
Suka kuma fassara inda Allah Ya ce cikin Suratul Israa’i aya
ta 23:-
{ ﻭﻗﻀﻰ ﺭﺑﻚ ﺍﻻ ﺗﻌﺒﺪﻭﺍ ﺍﻻ ﺇﻳﺎﻩ }.
Ma’ana: {UbangijinKa Ya hukunta cewa kada ku bauta wa
kowa sai Shi}.
Sai suka ce: Ma’anar ayar ita ce: “Ubangijinka Ya riga ya
kaddara muku cewa ba za ku yi wata bauta ba face Allahn ne
dai kuka bautawa! saboda haka babu wani abu a duniyan da za
ku bautawa face a hakikanin lamari Allah ne Shi kadanSa kuka
bautawa!!


Suka kuma fassara inda Allah ya ce cikin Suratul Hijri aya ta
99 :-
{ ﻭﺍﻋﺒﺪ ﺭﺑﻚ ﺣﺘﻰ ﻳﺄﺗﻴﻚ ﺍﻟﻴﻘﻴﻦ }.
Ma’ana: {Kuma ka bauta wa Ubangijinka har mutuwa ta zo
maka}. Sai suka ce: ma’anarsa shi ne: shi Dan Adam ana
umurtansa da yin ibada ne har zuwa lokacin da ya kai
matsayin Yakini da sanin Allah, da zarar ya kai wannan
matsayi ayyukan ibada sun fadi ke nan a Kansa!!
Reshe na biyu: Sai a ce da su: Wani malami ne cikin
maluman tafsiiri daga magabata Salafus Salih ya fassara wannan
ayar da irin wannan fassara taku ta cewa: Ana nufin yin bukin
maulidi ne da wannan ayah? 


Lalle muna tabbatar wa masu
karatun wannan rubutu namu cewa: har abada yan bidi’ar
maulidi ba za su iya kawo koda malamin tafsiiri daya ba daga
cikin Salafus Salih da ya fassara wannan ayar da cewa tana
nufin umurni ne da yin bukin maulidi.
Rashe na uku: Sai a ce da su: In dai har wannan ayar tana
nufin yin bukin maulidi ne to kuwa lazimin hakan shi ne:



Sahabbai da sauran shugabannin Al’ummah kamar su Abu
Hanifah, da Mali, da Shafi’ii da Ahmad, da sauransu
dukkansu ke nan sun nuna kiyayya da rashin kauna ga Manzon
Allah Mai tsira da amincin Allah, sannan dukkansu ke nan sun
saba wa umurnin Allah da ya zo cikin wannan aya ta 58 da
ta zo cikin Suratu Yunus, domin har suka gama rayuwarsu
babu wani daga cikinsu da ya taba yin bukin maulidi! Duk
kuwa wanda ya ce: Sahabbai, da Taabi’ai da sauran
shugabannin Al’ummah ba sa kaunar Manzon Allah ko ba sa
girmama shi, ba sa bin umurnin Allah da ya zo cikin
Alkur’ani na girmama shi to lalle wannan ya bace bata
bayyananniya! Lazimin wannan kuwa shi ne: Yan bukin
maulidi su ne batattu saboda lazimin maganarsu ta tabbatar da
cewa Sahabban Manzon Allah da Taabi’ai, da
Taabi’utttaabi’ina da sauran Sugabannin Al’ummah batattu
ne, saboda ba su yi aiki da wannan aya ba:-
{ ﻗﻞ ﺑﻔﻀﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺑﺮﺣﻤﺘﻪ ﻓﺒﺬﻟﻚ ﻓﻠﻴﻔﺮﺣﻮﺍ ﻫﻮ ﺧﻴﺮ ﻣﻤﺎ ﻳﺠﻤﻌﻮﻥ }.
Reshe na hudu: Sai a ce da su: Dukkan abin da bai zama
nuna soyayya ba ne ga Manzon Allah a zamanin Shabbai da
Taabi’ai da sauran Shugabanni kamar Imam Malik, da Abu
Hanifah, da Shaa’i’ii, da Ahmad, to ba zai zama nuna
soyayya ga Manzon Allah ba a wannan zamani namu.
Idan kuma wani daga cikin yan bukin maulidi ya fidda
jahilcinsa a fili ya ce: Ai Suyuutii ya halatta yin bukin
maulidi ! Sai a ce da shi: 



Ai shi Suyuutii ba ya daga cikin
wadanda ake kira Magabata cikin Musulunci, a’a yana cikin
jerin yan baya ne, domin ya mutu ne a shekara ta 911 na
hijira watau yau shekara 523 ke nan da suka wuce. Kuma shi
Suyuutii a wurin Malamai mutum ne da yake kama da mai
tara kirare cikin dare, ya kan dauki kirare sannan ya kan dauki
macizai da kunamu, saboda wannan idan har ya halatta
bidi’ar bukin maulidi ba wani abin mamaki ba ne a gurin
Malamai, domin ya yi ma abin da ya fi hakan muni da ban
mamaki, saboda Mai littafin Rimaahu Hizbir Rahiim ya ce a
cikin wannan littafi nasa wanda aka buga tare da littafin
Jawaahirul Ma’aa’nii 1/199 ya ce shi Suyuutii ya ce cikin
littafinsa mai suna :-
ﺗﻨﻮﻳﺮ ﺍﻟﺤﻠﻚ ﻓﻲ ﺇﻣﻜﺎﻥ ﺭﺅﻳﺔ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﻭﺍﻟﻤﻠﻚ
“Ya ga Annabi kuma ya yi taro da shi a farke har sau
saba’in da wani abu”! Mai irin wannan magana mara tushe
don ya ce bukin maulidi halal ne mene abin mamaki a cikin
maganarsa? Allah Ya tsare daga fadawa cikin ko wace irin
halaka. Ameen.....

_#DR,JALO JALINGO_

*_Gabatarwa_*:- Yusuf Ja'afar Kura 

Daga
*MIFTAHUL Ilmi*
WhatsApp

→ ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren *MIFTAHUL ILMI* whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu *(07036073248)* ta ‎whatsApp.
Post a Comment (0)