* Bada Umarni - Louis Leterrier
* Ɗaukar Nauyi - Avi Arad /Gale Anne Hurd/Kevin Feige
* Rubutawa da Tsarawa - Zak Penn
* Taken Fim - Craig Armstrong
* Tacewa - John Wright/Rick Shain
The Incredible Hulk Fim ɗin jarumta ne da aka fitar da shi a cikin shekara ta 2008 a Ƙasar Amurka. Labarin fim ɗin ya samo asali ne daga littattafan almara mai suna Hulk wanda Stan Lee da Jack Kirby suka wallafa a ƙarƙashin Kamfanin Marvel Comics. Kamfanin Marvel Studios ne ya ɗauki nauyin shirya shi, yayin da Universal Pictures ya rarrabashi. Incredible Hulk shi ne Fim na biyu daga cikin Fina Finan duniyar Marvel mai suna Marvel Cinematic Universe (MCU).
Mafi yawancin Fim ɗin an ɗauke shi ne a Toronto ,
Ontario, daga Yuli zuwa Nuwamba 2007. An saki fim ɗin ne a ranar 8 ga watan Yuni 2008 a gidan kallo na Gibson Amphitheatre dake Universal City, California, sannan aka sake shi a ko'ina ranar 13 ga watan Yuni 2008. Fim ɗin ya samu yabo sosai daga ƴan kallo da masu sharhi baki ɗaya, musamman a fannin kayan aiki, faɗa da kuma yadda aka tafi da jarumin Fim ɗin. Bugu da ƙari, fim ɗin ya kawo kuɗi kimanin Dala miliyan $263 a harkar Kasuwancin Fina Finan duniya baki ɗaya.
LABARIN FIM ƊIN
Janar Thunderbolt Ross ya gana da Dr. Bruce Banner a Culver University da ke Virginia. Bruce Saurayin ƴar wannan Janar ɗin ce mai suna Betty kuma abokin aikin ta. A wannan zama sun tattauna ne akan wani gwaji wanda shi Janar Ross ya haƙiƙance cewa zai baiwa ƙwayoyin halittun ɗan adam kariya daga Sinadarin Gamma Radiation.
Shi wannan gwaji, wanda wani shiri ne na ganin an Samar da wasu zaratan jarumai domin yaƙin duniya na biyu, Janar Ross so yayi ya sake ƙirƙirar sa, amma sai abin bai yiwu ba. Wannan yunƙuri da akayi sai ya zama sanadin haɗewar jinin Banner da wannan sinadari na Gamma Radiation, hakan yasa yake rikiɗa izuwa Hulk lokaci bayan lokaci duk sa'ilin da bugun zuciyarsa ya wuce matakin 200 a kowace daƙiƙa.
Daga nan sai Hulk ya ruguza ɗakin gwaje-gwajen ya kuma kashe wasu tare da raunata wasu daga cikin mutanen da ke ɗakin sannan ya tsere. Daga nan fa sai ya zama ɗan gudun Hijira wa hukumar soji ta Amurka da kuma Janar Ross a keɓe, saboda so yake yi ya maida shi makamin sa.
Shekaru biyar bayan faruwar haka, yanzu Banner yana aiki ne a wani Kamfanin haɗa kwalabai Rocinha , Rio de Janeiro da ke Brazil, Yayinda yake ci gaba da binciken maganin da zai warkar da shi.
A garin haka ne ya haɗu da wani masanin kimiyya da ke amfani da sunan "Mr. Blue", shi kuma yasan Banner da sunan "Mr. Green". Sannan kuma yana koyon Yoga domin ya koyi kulawa da kansa, har ma ya samu sa'a inda ya ɗauki tsawon Watanni biyar bai rikiɗa ba.
Watarana suna aiki sai yanke yatsar sa, ɗigon jinin sa sai ya ɗiga a wata kwalba wacce wani tsoho ya sha Lemon da ke cikin, aikuwa tsohon na sha nan take ya kamu da cutar gamma. Ross sai yayi amfani da wannan kwalba wajen gano inda Banner yake tare da tura manyan dakaru domin su kama shi. Jagoran waɗannan dakaru kuwa shi ne Shararren Sojan ruwa ɗan Birtaniya - haifaffen Rasha Emil Blonsky. Ai kuwa sai Banner ya rikiɗa ya koma Hulk yayi fatali da tawagar dakarun.
Yayinda Ross ya bayyanawa Blonsky yadda akayi Banner ya koma Hulk, sai ya amince shi ma ayi masa irin wannan allura da sinadarai kaɗan. Hakan ya bashi ƙarfin gudu na musamman, ƙarfin damtse, juriya da kuma saurin warkewa, amma kuma sai allurar ta fara canja masa Kamanni tare da canja masa Ra'ayin sa.
Banner sai ya dawo Culver University Inda suka haɗu da Betty wacce yanzu ta koma soyayya da likitan hauka Leonard Samson. Ross da Blonsky sai suka ƙara kawowa Banner hari, ashe Samson ne ya sanar da su abin da ake ciki. Hakan yasa shi ya ƙara rikiɗa izuwa Hulk. Fafatawar da akayi dai ya tabbatar da cewa mayaƙan Ross babu abin da zasu iya yiwa Hulk, amma shi Blonsky wanda hankalin sa ya fara gujewa sai ya ci gaba da tsokanar Hulk Yayinda sauran mayaƙan suka ja da baya.
A nan ne Hulk ya yiwa Blonsky mugun duka inda kowa yayi tunanin ya mutu, sannan sai ya ɗauki Betty ya gudu da ita. Bayan ya rikiɗa izuwa Banner, sai shi da banner suka ci gaba da guduwa Yayinda Banner ya tuntuɓi Mr. Blue, sai ya ce masa su haɗu a birnin New York.
Mr. Blue dai ba kowa bane face likitan halittu Dr. Samuel Sterns , kuma ya faɗawa Banner cewa ya samar masa da wani magani. Bayan anyi wani gwaji, sai Sterns ya gargaɗi Banner da cewa maganin zai magance kowace rikiɗa ce kawai. Ya kuma gaya masa cewa yayi amfani da jinin da ya taɓa aiko masa wajen ƙirƙirar wasu misalan Jinannakin domin ayi amfani da jinin nan gaba wajen ƙirƙirar magunguna. Saboda jin tsoron kada wannan samfuri na jini nasa ya faɗa hannun sojin Amurka, sai Banner ya yanke hukuncin tarwatsa komai gaba ɗaya.
Blonsky ya rayu daga wannan mugun duka da Hulk yayi masa a Culver University Kuma ya warke tsngaras! Don haka sai ya ƙara shiga cikin dakarun Ross a karo na uku domin su kama Banner. Bayan sun kama Banner shi da Betty, sai aka ɗauke su a jirgin sama. Shi kuma Blonsky sai ya tsaya ya baiwa Dr. Sterns umurnin yayi masa alluran jinin Banner duk da ya gargaɗe shi da cewa wanzuwar allurar da akayi masa da jinin Banner a jikin sa zai iya haifar masa da Illah, Blonsky sai yayi kunnen uwar shegu. Aikuwa bayan an masa allurar sai ya zama wani jibgegen halitta wanda ya fi Hulk girma da ƙarfi, sai dai kuma hakan ya haukatar da shi.
Daga nan sai ya kaiwa Sterns hari wanda jinin Banner ya fallatsa masa a cikin wani ciwo da ke goshin sa, shi ma dai nan ya fara rikiɗan. Blonsky kawai sai ya fara ta'adi a cikin garin Harlem. Ganin cewa Hulk ne kaɗai zai iya tsaida Blonsky, sai Ross ya sake shi inda yayi tsalle daga wannan jirgi kuma ya rikiɗa bayan ya faɗo ƙasa. Bayan sun ɗauki tsawon lokaci suna ɗauki ba daɗi, Hulk yayi nasara akan Blonsky. Bayan sun ɗan gana da Betty, sai Hulk ya tashi sama ya gudu.
Bayan wata ɗaya, Banner yana Bella Coola, British Columbia. A Nan ne ya rikiɗa a nutse maimakon da da sai anyi hargitsi.
A wata fitowa ta ƙarshe, an nuno Ross a wata mashaya inda Tony Stark ya ziyarce shi, kuma ya sanar masa da cewa ana shirin haɗa wata tawaga.
JARUMAN FIM ƊIN DA MATSAYIN DA SUKA FITO A CIKIN SA
* Edward Norton - Bruce Banner / Hulk
* Liv Tyler - Betty Ross
* Tim Roth - Emil Blonsky / Abomination
* Tim Blake Nelson - Samuel Sterns
*VTy Burrell - Leonard Samson
* William Hurt - Thaddeus "Thunderbolt" Ross
* Robert Downey Jr. - Tony Stark
<><><><><><>>><><><><><><>
___________________________________
●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●
<••••••••••••••••••••••••••••>
👳🏻♂ *_Haiman Raees_* <••••••••••••••••••••••••••••>
*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
08185819176
*_"""""""""""""""""""""""_*
🌐 _*Web:*_ www.haiman.com.ng
*_"""""""""""""""""""""""_*
🖥 _*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees
*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees
*_"""""""""""""""""""""""_*
🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees
*_"""""""""""""""""""""""_*
📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*
Miyan Bhai Ki Daring...