SHARHIN FIM ƊIN IRON MAN
* Bada Umarni - Jon Favreau
* Ɗaukar Nauyi - Avi Arad/Kevin Feige
* Rubutawa Da Tsarawa - Mark Fergus/Hawk Ostby/Art Marcum/Matt Holloway
* Taken Fim - Ramin Djawadi
Iron Man Fim ɗin jarumta ne da aka fitar da shi a cikin shekara ta 2008 a Ƙasar Amurka. Labarin fim ɗin ya samo asali ne daga littattafan almara mai suna Iron Man wanda Stan Lee, Larry Leiber, Don Heck da Jack Kirby suka Wallafa a ƙarƙashin kamfanin Marvel Comics. Kamfanin Marvel Studios ne ya ɗauki nauyin shirin, yayin da Kamfanin Paramount Pictures suka rarraba shi.
Iron Man shi ne Fim na farko daga cikin Fina Finan duniyar Marvel mai suna Marvel Cinematic Universe (MCU).
An fara ɗaukar wannan Fim ne a cikin watan Maris 2007, kuma aka kammala a cikin watan Yuni.
An saki Iron Man a Sydney ranar 14 ga watan Afrilu 2008, sannan kuma an sake shi a ko'ina ranar 2 ga watan Mayu 2008. An kashewa fim ɗin kuɗi Dala miliyan $140, Fim ɗin ya kawo maƙudan kuɗaɗe kimanin Dala Miliyan $585 a harkar Kasuwancin Fina Finan duniya baki ɗaya. Bugu da ƙari, fim ɗin ya samu yabawa sosai daga wajen ƴan kallo da kuma masana a harkar Fina-Finai na duniya musamman a ɓangaren ƙoƙarin jarumin fim ɗin da kuma kayan aikin da aka yi amfani da su a cikin sa.
Ƙungiyar American Film Institute ta zaɓi fim ɗin a matsayin ɗaya daga cikin fitattun Fina-Finai goma Goma na wannan shekarar. An Yi na biyu da na ukun fim ɗin.
Shahararren Biloniya, Hamshaƙin Masani a harkar ƙere-ƙere kuma ƙasurgumin ɗan shagali Wato Tony Stark ya gaji Kamfanin ƙera makamai na Stark Industries wanda Mahaifin sa ya mutu ya bar masa.
Saboda haka ne ma ya tafi Afghanistan tare da abokin sa Laftanal Kanal James Rhodes domin su gwada wani sabon makami da ya ƙera mai suna Makamin Jericho. Bayan an gama gwajin, sai aka kaiwa motocin da ke ɗauke da Stark hari da irin makaman da Kamfanin sa suke ƙerawa. Stark ya samu mummunan rauni a wannan harin, sannan sai wasu gungun mahara da ake kira da Ten Rings suka kama shi suka kulle a cikin wani kogo tare da wani likita mai suna Yinsen.
Yinsen shi ne ya taimakawa Stark wajen sanya masa wata Na'ura a ƙirjinsa domin ta hana guntattakin ƙarafunan da suka ji masa ciwo kaiwa ga zuciyar sa, wanda in hakan ya faru zai mutu nan take.
Shugaban waɗannan Mahara mai suna Raza ya yiwa Stark alƙawarin sakin shi idan har ya ƙera masa irin wannan makami na Jericho, amma Stark da Yinsen sun san cewa ƙarya yake yi.
Stark da Yinsen sai suka ƙera wani ɗan ƙaramin janareta mai ƙarfin gaske domin ya baiwa wannan Na'ura da ke jikin Stark ƙarfin da ya kamata, sannan kuma ya baiwa rigar ƙarfen da suka ƙera a ɓoye wutar da zai basu damar guduwa daga wannan waje. Duk da cewa sunyi aikin su a sirrance har suka kusan gamawa, wannan ƙungiya ta mahara sun gano nufin su, don haka sai suka kai musu hari a wajen aikin nasu. Yinsen sai ya sadaukar da Rayuwarsa ta hanyar jan hankalin su zuwa wani waje can daban domin Stark ya samu ya kammala Haɗa wannan riga.
Tony Stark sai ya fito cikin wannan rigar ƙarfe tasa inda sukayi ba-ta-kashi a tsakanin sa da waɗannan mahara, ganin Yinsen a mace yasa shi fusata har ya farfasa makaman waɗannan mahara sannan ya tashi sama yayi tafiyar sa, amma baiyi nisa ba ya faɗo a cikin Sahara ya fasa rigar a sanadiyyar haka. Bayan Rhodes ya ceci a jirgi ya maida shi gida, sai ya sanar cewa daga yanzu kamfanin sa ba zasu ƙara Sana'anta makamai ba.
Obadiah Stane , wanda tsohon abokin aikin Mahaifin Tony ne kuma Manajan Kamfanin a yanzu, ya faɗa masa cewa wannan hukunci da Stark ya yanke zai iya kawo ma Kamfanin tsaiko, kuma tamkar cin fuska ne ga wasiyyar Mahaifin sa. Da Stark ya samu nutsuwa, sai ya sake ƙera wata Ingantacciyar rigar ƙarfe wacce tafi wancan komai sannan ya sake ƙera wani sabon janaretan da zai saka a ƙirjinsa wanda ya fi wancan ƙarfi da inganci. Mataimakiyarsa ta musamman Pepper Potts sai ta ajiye na asalin ƙaramin janaretan a wani gidan gilashi. Duk da cewa Stane ya nemi Stark yayi masa ƙarin bayani dangane da abubuwan da yake ƙerawa, Stark yayi Mirsisi saboda ya fara zargin Kamfanin nasa.
A yayin wani taron taimakawa gajiyayyu da Kamfanin Stark Industries suka shirya, ƴar Jarida Christine Everhart ta sanarwa da Stark cewa makaman da Kamfanin sa ya ƙera, ciki har da makamin Jericho sun isa hannun maharan TEN RINGS kuma suna can suna yaƙar mutanen ƙauyen su Yinsen wato Gulmira. Daga nan ne sai Stark ya gano cewa ashe Stane yana ta saidawa ƴan ta'adda makaman sa ne a koi'ina cikin duniya kuma yana masa zagon ƙasa don yaga ya zama shugaban Kamfanin Stark Industries.
Stark sai ya sanya wannan sabuwar riga tasa ya nufi Afghanistan inda ya ceci mutanen ƙauyen. A kan hanyar sa ta dawowa ne wasu jiragen yaƙi guda biyu suka kai masa hari, har sai da ya kira Rhodes a waya ya sanar mishi da cewa shi ne a cikin rigar kafin su ka ƙyale shi.
Can kuma a gefe, mharan Ten Rings Sai suka tattaro wannan riga da Stark ya fara ƙerawa har ta fashe suka kawowa Stane, nan take Stane yayi maganin Raza sannan yasa aka kashe sauran maharan. Daga nan sai shima Stane yayi amfani da wannan damar ya ƙera wata Jibgegiyar riga tasa ta kansa. Shi kuma Stark saboda ya gano inda makaman da ake siya daga Kamfanin sa suke zuwa sai ya aika Potts domin ta datse Kundin bayanan da ke ofishin Stane. A nan ne ta gano cewa Stane ya yo hayan waɗannan maharan ne domin su kashe Stark, amma sai suka ƙi.
Daga nan sai Potts ta gana da Jami'i Phil Coulson daga Ƙungiyar asiri ta S.H.I.E.L.D. In da ta sanar masa da abin da Stane yake aikatawa. Kasancewar malaman Kimiyyar Stane ba zasu iya ƙera wannan ɗan ƙaramin janareta ba, sai Stane ya kaiwa Stark hari a gidan sa, bayan ya Sanƙamar da shi, sai ya cire Janaretan nasa daga ƙirjin sa ya tafi. Da ƙyar da siɗin goshi Stark ya kai ga asalin Janaretan sa da ke ajiye, ita kuma Potts tare da wasu jami'ai daga Ƙungiyar S.H.I.E.L.D. Sai suka yi ƙoƙarin kama Stane amma tuni ya sanya wannan riga tasa inda ya fara kai musu hari.
An cikin hakane Stark yazo, amma saboda wannan Janaretan ba zai iya baiwa sabuwar rigar tasa wutar da ta kamata ba sai ya zamana Stane ya fi ƙarfin sa. Nan fa faɗan da suke yi ya ɗauke su har izuwa hasumiyar Kamfanin Stark. A can ne Stark ya sa Potts ta kunna asalin babban Janaretan da ke baiwa gidan wuta baki ɗaya, hakan ya haifar da wanzuwar zunzurutun ƙarfin wutar lantarki wanda ya kado da Stane da rigar sa ya mutu.
Washegari, Yayinda ya ziyarci wani taron ƴan jarida, Stark ƙiri da muzu yaƙi ɗaukar kowace shawara daga Ƙungiyar S.H.I.E.L.D. Sannan ya bayyanawa duniya cewa shi ne jarumin da suka sani da sunan Iron Man.
A wata fitowa ta ƙarshe, an nuno Daraktan Ƙungiyar S.H.I.E.L.D.
Nick Fury ya kawo wa Stark ziyara, inda yake bayyana masa cewa ba fa shi kaɗai bane Jarumi a cikin duniyar nan. Tare kuma da yi masa bayani dangane da himmar haɗa tawagar Avengers.
JARUMAN FIM ƊIN DA MATSAYIN DA SUKA FITO A CIKIN SA.
* Robert Downey Jr. - Tony Stark / Iron Man
* Terrence Howard - James "Rhodey" Rhodes
* Jeff Bridges - Obadiah Stane
* Shaun Toub - Yinsen
* Gwyneth Paltrow - Pepper Potts
* Faran Tahir - Raza
* Paul Bettany - J.A.R.V.I.S.
* Leslie Bibb - Christine Everhart
* Clark Gregg - Phil Coulson
* Jon Favreau - Happy Hogan
* Samuel L. Jackson - Nick Fury
Source: Wikipedia
<><><><><><>>><><><><><><>
___________________________________
●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●
<••••••••••••••••••••••••••••>
👳🏻♂ *_Haiman Raees_* <••••••••••••••••••••••••••••>
*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
08185819176
*_"""""""""""""""""""""""_*
🌐 _*Web:*_ www.haiman.com.ng
*_"""""""""""""""""""""""_*
🖥 _*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees
*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees
*_"""""""""""""""""""""""_*
🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees
*_"""""""""""""""""""""""_*
📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*
Miyan Bhai Ki Daring...