««« TARWATSA MAZA-1
Littafe Na daya.
Na Abdul Aziz Sani Madakin Gini..
TYPING... Suleiman zidane kd...
Facebook.Suleiman zidane kd...
Whatsapp phone number... 09064179602:
.................................................................
A wani zamani can baya mai tsawo da ya shude, lokacin da ake rayuwa ta zalunci, kafirci da fasikanci, anyi wata babbar daula dake karkashiin wani shahararren sarki mai suna HASANUL MAUZUR.
Sarki hasanul mauzur ya kasance gawurtaccen mayaki mai tarwatsa maza afilin daga, wanda atarihin jarumtakarsa bai taba zuwa kasa ba,kuma ba a taba jimasa rauniba komai girman kato kuma komai karfinsa indai yakara da sarki hasanul mauzur sai yayi na dama baya ga wannan sadaukan taka da allah ya bashi, ya kasance mashahurin attajirin da babu kamarsa a duk fadin nashiyar dayake domin shi kansa bai san iyakar. Dukiyar da ya mallakaba.
Birnin sharas shine sunan kasar sarki hasanul mauzur kuma a karkashin birnin a kwai manyan birane kimanin guda bakwai amma duk birnin sharas inda fadar sarki hasanul mauzur take ya fi sauran kyau girma da daukaka. Gaba daya mutanen daular suna bautar wani karamin Gunkine mai siffar kyanwa wanda ake wa lakabi da hurzas.
Shidai wannan gunki an a jiyeshi ne a cikin wani kasaitaccen gida wanda babu mai shiga cikinsa face mutum biyu kacal.
Daga sarki sai bokansa mai suna SURAB IBIN KAIZAR, sai kuma wanda yayi gagarumin abin bajinta ko kuma wanda ya farantawa sarki rai, sai ayi masa izinini ya shiga dakin bautar ta gana da gunki hurzaas.
Duk mutumin daya gana da gunki hurzas tofa kakarsa ta yanke saka domin duk irin bukatar da ya yake da ita ta duniya, sai ta biya bisa wannan daliline fa dawan sarki ke ta yimasa shishshigi da neman yarda don kawai a lamince musu ganawa da gunki hurzas. A shekara guda mutum daya kacal akan samu wanda sarki ke lamincewa.
Sarki hasanul mauzur na da kyakykyawar 'ya guda daya jal, wata budurwa mai suna SHULAIRA kyawun shulaira yafi gaban kwatance sai abin da idanu ya gani. Ko kadan shulaira bata gado mahaifintaba a wajen jarumta da halaiya domin ita ta kasance mai tausayi son jama'a da taimako, sabanin mahaifinta wanda ko yaushe ba shi da aikin yi face cin zali da kai harin sumame don samo dukiya da bayi ko taimako sarki hasanul mauzur zaiyi sai dai ya yiwa attajiri ko babban basarake amma ba talakan gari ba. A rayuwar duniya babu abin da sarki hasanul mauzur ya tsana sama da talaka.
Gimbiya shulaira ta tsani halayen mahaifinta, amma tunda babu yarda zata yi ta hanashi yi, dole ta ke hakuri. Sai dai a duk sa'adda zai yi zalunci in dai tana wajen tana hana shi kuma sai ya hakura dole saboda tsananin son ta da yake don baya son yayi abin da zai sosa mata zuciya tunda mahaifiyar shulaira ta mutu sarki hasanul mauzur bai sake yin aure ba, kuma yayi alkawarin har abada bazai kara yin aureba saboda dama ya dauki wannan alkawari ga mahaifiyar shulaira. Sa'adda ta kwanta cutar ajali, tsawon shekaru uku a wannan lokaci shulaira bata fi sheekara takwas a duniya ba lokacin da imila mahaifiyar shulaira ta tabbatar da cewa cutarta bata tashi bace sai ta dubi sarki hasanul mauzur tace, "ya kai mijina yanzu idan na mutu wacce mace zaka auro ta kaunaci shulaira kamar yadda nake kaunarta?l
Koda jin haka sai imila ta fashe da kuka sannan tace, "kayi sani cewa na sha yin mafarki ana nuna mini shulaira a cikin wahala bayan raina bisa haka ne nake tsoron cewa zata sha wahala ne a wajen matar da zaka auro".
Koda jin wannan batu sai sarki hasanul mauzur yace, "AIkuwa tunda haka ne, nayi miki alkawarin in dai mutuwa ta daukeki har abada bazan sake sha'awar wata 'ya mace ba bare ma na aureta sai dai na zauna da barori da kuyangina kawai".
Sa'adda Imila taji haka sai ta cika da farin ciki tace, "Hakika yanzu ne ka nuna mini soyayyarka ta gaskiya, ina yi maka fatan jurewa bisa wannan alkawari da ka dauka".
Hasanul mauzur yace, "Tabbas zan kasance mai jaddada wannan alkawarin, har izuwa ranar da nima nawa wa'adin ya cika"
Ai kuwa tun daga ranar da Imila ta rasu sarki hasanul mauzur bai kara sha'awar yin aure ba, koda kuwa yaga macen da ta burgenshi, don kada ya karya alkawarin da ma a gaban shulaira ya yiwa imila wannan alkawarin.
Lokacin da shulaira ta cika shekara sha takwas a duniya, sai 'ya'yan sarakai da 'ya'yan attajirai suka yi caa akan neman aurenta. Ita kuwa shulaira sai ta nuna sam bata da ra ayin aure. Al'amarin daya dugunzuma hankalin sarki hasanul mauzur kenan ya kirata yace, "yake 'yata ke kuwa menene dalilin ki na kin yin aure ayanzu, alhalin dukkanin masoyanki babu na banza?"
Sa'adda shulaira taji wannan tambaya sai tayi murmushi, tace, "Ya kai abbana kayi sani a matsayinka na shahararren sarki , mai karfin mulki da karfin arziki, da kuma gagarumar jarumta bai kamata a auri 'yarka cikin sauki ba. Dolene ya zamana cewa wanda zai aureni yayi babbar bajimta, wadda zata zamo abin tarihi a duniya, gaba daYa. Bisa wannan daliline na yankewa kaina sadaki, kuma na shirya mataki da sharadi wanda dole sai anbisu sannan za a sami ikon aurena kosa gimbiya shulaira tazo nan a zancenta, sai sarki hasanul mauzur ya cika da tsananin farin ciki, ya dubeta cikin murmushi, yace, "yake 'yata hakika kin zomini da shawara mai kyau, wadda ta faranta mini raina , saboda haka yanzu saiki yi mini bayanin mataki da sharadin da kika gindaya bisa neman auren naki".
Cikin murna shulaira tayi gyaran murya, sannan tace, "mataki na farko shine, duk sauraayin dake son aurena dole ne yabiya sadaki na kudi adadin dinare miliyan dubu daya mataki na biyu ina son a zabo manyan sadaukai guda dari wadanda babu kamarsu a na shiyarnan dole ne manemin aurena ya fafata dasu ya tarwatsasu mataki na uku dolene manemin aurena ya gwabza yaki dakai, ya kaika kasa sharadi kuwa duk wanda ya aureni bazai yi mini kishiyaba, kuma idan na rigashi mutuwa bazai kara aureba har abada".
Yayinda shulaira ta zo nan a jawabinta sai idanun sarki suka ciko da kwalla har hawaye ya zubo masa ya dubeta yana mai yaken, yace, "yake 'yata hakika kin burgeni matuka bisa wannan mataki da sharadi da kika kirkiro, domin kin nuna min cewa kema kina matukar kaunar mahaifiyarki, kuma kina cikin begenta, dare da rana. Na amince da wannan matakai da sharadi da kika gindaya, amma abin da nake so da ke shine kada a furta sharadin sai sai bayan anci wannan gasa kuma za'a sanar da hakan.
Yake 'yata kiyi sani kin kirkiro gasa mai matukar wahala wadda bana zaton za a sami mahalukin da zai iya haye wadannan matakai uku koda mutum ya haye guda biyun, tofa bazai iya haye na ukun ba, dalili kuwa shine a kwai wani sirri mai karfi wanda ban taba gaya miki shiba amma a yanzu zan sanar dake, tunda wannan al'amari ya bijiro".
Sarki hasanul mauzur ya kyara zama gami da gyaran murya, sannan ya fara bayani kamar haka.....
"Na kasance sadaukin gaske, amma bokana ya tabbatar mini da cewa, akwai sadaukai uku a duniya wadanda su kadai ne zasu iya kaini kas idan muka yi gaba-da -gaba dasu. Lokacin da boka surub ibini kaizar yayi mini wannan jawabi sai hankalina ya dugunzuma na rasa abinda ke min dadi a duniya, don haka sai na dubeshi nace, "ya kai babban boka yanzu me zanyi na kare kimata ya zamana cewa koda na hadu da wadannan sadaukai uku ba zasu iya kaini kasba? Kuma ina son kasarar dani inda wadannan sadaukai suke da kuma suffofinsu domin na kiyaye karona dasu kafin na sami kariya". Koda jin wannan batu sai boka surub yai shiru kuma ya sunkui da kansa kas. Yana mai rintse idanunsa gami da karanta wadansu dalasiman tsafi, daga can sai ya dago kai ya kalleni kawai sai ya bushe dadariya, yace, "ya kai wannan sarki mai daraja kayi sani cewa, bukatarka zata biya idan har zaka iya jure yin a bubuwan da zamu umarceka dayi.
Da farko dole ka samo abubuwa uku domin na hada maka wani magani wanda zaka shafe gaba dayan jikinka da shi, wadannan abubuwa sune, kwakwalwar rikakken Gaggon biri,wanda ya shekara tamanin a duniya sai kuma kitsen zakanya wacce ke dauke da tsohonciki, haihuwa yau ko gobe.
Abu na uku shine harshen giwa wacce ta haura shekara hamsin. Za a hada wadannan abubuwa a cikin tukunya a rufe sannan akwanna tara ana dafasu. A daren kwana na taranne zakayi tsirara ka shafe jikinka da waddannan abubuwa uku sannan ka tafi makabartar a cikin tsirara batare da kasa tufafiba idan ka isa makabar tar sai ka nemi kabari wanda ya kai shekara tamanin bai bajeba kuma ba'a taba hake shiba ka zauna agaban kabarin ka soka hannayenka cikin kabarin ba zaka zareba sai bayan kwana uku. Duk bukatarka da zakayi sai dai ka yi ta a wajen, amma babu tashi kuma babu waiwaye.
Ya kai wannan sarki idan har ka sami nasarar kammala wannan aiki ba tare daka yi kuskureba to har abada babu wani sadauki da zai iya samun nasarar kaika kasa komai karfinsa kuma kuma harka mutu baza a taba samun galabar yaki a kankaba kuma babu wani kato dazaka yiwa naushi daya batare da ya baje a kasaba kai ko giwa ka nausa sai ta je kas"
Yayin da boka surub yazo nan a jawabinsa sai na kawo gwauron numfashi na a jiye, sannan na dubeshi nace "yakai babban boka hakika kazo mini da babban al'amari mai wuyar gaske to amma fani a rayuwata ban taba karaya ba, bisa duk a bin da nasa a gabana. Tunda ga kuruciya kawo izuwa girmana duk abinda na aiyana ina son nayi sai nayi shi, ban taba samun rashin nasaraba saboda haka ni yanzu na amince zan tafi neman wadannan abubuwa uku tai makon da zaka yimini kawai shine, ka fada mini dajin da zanje na samo wadannan abubuwa uku ba tare da na sha wahalar nema ba"
Koda jin haka sai boka surub yayi murmushi yace, "A yamma da kasarka akwai wadansu dazuzzuka guda uku wadanda suka yi iyaka da kasar hairuf. Daji na farko ana kiransa da suna Darul-shazar acikinsa ne zaka sadu da rikakken goggon biri, wanda ya shekara tamanin. A duniya shidai wannan biri a halin yanzu babu wani biri mai karfi da girma tamkarsa saboda tsananin karfinsa ma da faratan hannayensa ya kwakule wani katon dutse yayi gidansa a ciki inda ya ke kwana tare da matarsa da kuma 'ya'yan sa guda bakwai.
Wannan biri tare da 'ya'yansa sun hana fatake da matafiya ratsawa ta cikin dajin darul-sharzas, domin komai yawan runduna suna iya tarwatsata saboda karfisu da kuma tsagwaron dabararsu ta iya yaki makaminsu shine faratansu idan kuwa suka daka tsalle daga kasa suna iya hawa kan bishiya mai tsawon zira'I dari da hamsin, sannan suna da zafin nama na gaban kwatance, sai dai kawai mutum yaga sun gilma ta gabansa sun bace tamkar kiftawar ido. Ya zama dole ka yi yaki da 'ya'yan wannan goggon biri, ka kashesu suduka bakwan, sannan zaka sami damar kashe ubansu.
Kasani cewa karfinka ko karfin sihirinka bazai kwaceka ba, a hannun goggon birin face dabara da hikimar iya yaki da zarar ka kashe birin matarsa zata gudu to a sannanne zaka fafe kansa ka debo kwakwalwarsa ka adanata, sannan ka wuce izuwa daji na gaba wanda ake kira shajaral mausuba. A cikin dajin shajarul mausuba ne zaka riski zakanya mai dauke da tsohon ciki, haihuwa yau ko gobe. Ita dai. Wannan zakanya tana cikin wani kogon dutse ne dake bisa dogon tsauni. Dole ka hanzarta nan da kwana goma shahudu karisketa in ba haka ba kuwa zaka iya tararwa ta haife abin dake cikinta ka ga kenan kitsenta bazai yi aiki ba.
Ita dai wannan zakanya tunda cikinta ya tsufa sai ta daina fita ko ina kullum tana cikin wannan kogon dutse mijinta ke gadinta yana kula da lafiyarta, 'ya'yanta kuwa guda uku suke tafiya sunemo mata abin da zataci. Kada ka je kogon dutsen sai da hantsi a sannan ne 'ya'yan nata ke tafiya neman abinci kaga kenan daga ita sai mijinta da zuwa sai ka farwa mijin nata ka kasheshi sannan itama ka far mata. Idan ka kasheta sai ka suri gawarta ka yi ta gudu da ita, har sai ka shiga cikin daji na uku sannan ne ka tsira daga sharrin 'ya'yanta.
In kuwa kace zaka tsaya farde cikinta ka debi kitsenta to tabbas 'ya'yan nata zasu iya zuwa su riskeka su hallakaka. Shi kuwa daji na uku shine wanda ake kira shajaril maurud inda zaka riski giwa wacce ta haura shekara hamsin a duniya. Ita dai wannan giwa mallakar wani sihirtaccen dodone mai suna gurmazu.
Dodo gurmazu ya kasance matsafi kuMa rikakken dan fashi wanda ke TARWATSA MAZA komai yawansu don haka fiye da shekaru hamsin baya ya kashe hanyar ba a ratsawa. Kai bama mutumba hatta aljanu da dabbobi tsoron shiga dajin sharjaril maurud suke, saboda masifar dodo gurmazu. Idan gurmazu ya kama aljani yakan yi kilishinsa ne, ya cinye domin yana matukar jin dadin dandanonsa a baki, tamkar mutum ya sami kaza. Idan kuwa dabba ya kama daranta yake cinyeta, babu fida ko gashi mutane kuwa koda sunkai dubu dari biyarkuwa sai ya cafkesu, ya zuba su a cikin wani katon keji ya rinka zararsu da dai-dai yana kalaci dasu. Matsafa da mayaka sunsha yin gangami wa 'yanda suka yarda da kansu domin suga bayan gurmazu, amma da zarar sunyi arba dashi tasu ta kare ko mutum daya bazai koma gidaba kai ko duriyarsu baza a sake jiba. Dole kakashe dodo gurmazu kafin ka sami damar kashe wannan giwa da yake kiwo har ka yanko harshenta sannan ka kawo mini abubuwa ukun a hada wannan magani da zaka shafe jikinka dashi".
Sa'adda sarki hasanul mauzur yazo nan a zancensa sai gimbiya shulaira ta gyara zama kuma ta tattara hankalin ta a waje daya tana mai kura masa idanu tace, "ina sauraronka ya kai abbana, bani labarin abinda yafaru gareka yayinda ka shiga wadannan dazuzzuka guda uku da yadda aka yi ka sami nasarar dauko wadannan abubuwa uku, hakika ka cika namijin duniya, dolene nayi maka kirari da jarumi uban jarumai, mai TARWATSA MAZA ".
Koda jin wannan batu, sai sarki hasanul mauzur ya fashe da dariya sannan yace, ai kowa yazama wane babanzaba duniya bata samuwa daga zaune sai an mike tsaye baki ance yaro bata hankalin dare kayi suna ba?" Hasanul mauzur yai gyaran murya. Sannan yafara bayani kamar haka......
"Yake 'yata kiyi sani cewa, kashe garin ranar da boka surub yai mini bayani nayi shiri na debi makaman yakina gami 'yan guraye da laloyina na tsafi, nayi sallama da mahaifiyarki awannan lokacin tana dauke da tsohon cikin ki saura baifi kwana arba'inba ta haihu. Dama tun a daren jiya nalabarta mata inda zan tafi da kuma abubuwan da zan tafi nema. Har yau har gobe bazan taba mantawa da wannan tafiya ba, domin ina yawan tuna abinda ya faru tsakanina da ita, da duk irin kalaman data gaya mini sa'adda muka zo yin sallama.
A wannan lokaci ana tsala ruwan sama kamar da bakin kwarya, kuma ana tafka tsawa da walkiya, wadanda suka tsorata gaba dayan mutanen garinnan kowa ya shiga gida yai zamansa, babu batun a fito yin harkoki, amma ni a sannan ne na gama shiri tsaf zanfita.
Koda mahaifiyarki taga na tsaya a gabanta da nufin muyi bankwana bisa tafiyar da bani da tabbacin da wowa gida sai ta fashe da matsanancin kuka kuma ta rungumeni al'amarin da ya karya mini zuciya kenan naji kamar na fasa yin wannan tafiya amma da na tuna irin matsayin da zansamu da daukaka idan har nai nasara, sai zuciyata ta kekashe gaba daya cikin raunin zuciya mahaifiyarki ta budi baki a lokacin da take rungume da ni tace, "yakai mijina saboda me zaka tafi kabarni alokacin da nake bukatarka fiye da ko yaushe? Kasani cewa abu ne mawuyaci na haura kwana hansin nan gaba ba tare da na haihuba.
Shin baka son kaga magajinka ne, kokuwa so kake magajin naka yazama maraya? Nikam na tsorata ainun da wannan tafiya daza kayi, domin ban taba jin labarin mutumin daya taba keta wadannan dazuzzuka uku ya dawo arayeba. Me zai hana kabari na haihu sannan kayi wannan tafiya?"
Koda jin wannan batu sai tausayinta ya kamani har idanuna suka ciko da kwallah, sannan na janye jikina, daga cikin nata muka fuskanci juna yayinda yayinda hawaye ke shatata bisa kan kumatunta. Kawai sai na ruke kafadunta da hannayena biyu, nace kamar yake matata uwar magajina, kiyi sani cewa kamar yadda na kasance jarumi kuma sadauki, haka mahaifina ya kasance, kuma na sami labarin cewa, shima a kokarin nemo wadannan abubuwa uku yabar gida. Har yau, har gobe bai dawo ba, kuma ko duriyarsa ba a ji ba yayin da zai bar gida ya tafi da wata sandar mulki ta wannan birni namu mai albarka na sharas, wacce ya gajeta a hannun mahaifinsa.
Masana tarihin sharas sun tabbatar da cewa sandar tafi shekara dari a cikin wannan gidan sarauta tamu kuma a salinta gunki hurzas ne ya samar da ita, don baiwa birnin da sarkin dake mulki cikakkiyar kariya da daukaka. Tunda mahaifina ya tafi da sandar sai arzikin birnin nan ya raunana, kuma kariyar da muka samu ta harin 'yan sumame a gefen kauyuka ta yawaita.
Lallai bincike ya tabbatar da cewa, a yanzu haka wannan sandar mulki na nan a cikin gidan dodo gurmazu ni kuwa na dade da shan alwashin sai na dawo da wannan sanda. Kinga kenan riba biyu zan ci a cikin wannan tafiya kuma ina neman daukar fansar ran mahaifina a wajen dodo gurmazu, domin boka surub ya tabbatar mini da cewa mahaifina ya haye sharrin dake cikin dajin darul shajar da shajaril mausuba. A cikin dajin shajaril maurud ne ya hallaka, yayinda yai arba da dodo gurmazu yake matata ina tabbatar miki da cewa sai dai ki yi hakuri domin babu abin da zai hanani yin wannan tafiya, muddin ina raye cikin koshin lafiya, amma dai ki yi sani cewa bani da tabbacin dawowa wata kila wannan shine ganina dake na karshe".
Sa'adda nazo nan a zancena sai ta sake fashewa da kuka sai da muka jima a manne da juna sannan na saketa na janye jikina na cire wata sarka mai dauke da hatimin sarautata dake wuyana na dorata bisa tafin hannunta nace, "Ga wannan ki adanata da kyau, duk abinda kika haifa walau mace ko namiji kisanya a wuyansa, don
minshi ne alamar cewa zai gajeni idan kuwa nna dawo gida a raye, da hannuna zan cire sarkar a wuyansa domin babu mai daura wannan sarkar a wuyansa face mai mulkin birnin sharas, kin kuwa sani cewa, ba a sarki biyu acikin birni guda.
Koda gama fadin haka, sai nayi bankwana
da mahaifiyarki, na juya na fice daga cikin
dakinta ban yarda na juyo na kalli
fuskartaba, don na tabbatar cewa hawaye
take zubarwa , in kwa na ga hawayen
zuciyata zata sake karaya na Fasa yin
tafiyar.
Dama tun a daren jiya boka surub ya hadani
da wani hadiminsa aljani barzila wanda zai
yi mini rakiya acikin tafiyata domin ya zame
min dan jagora, kuma mai debe mini kewa.
Koda fitowa kofar fidan sarauta yayinda ake
ta Cada wannan ruwan saman mai karfi sai
aljani barzila ya baiyana agabana yana mai
yi mini sujjada yace, "maza ka hau bayana
ya shugabana zan baka kariya daga wannan
ruwan sama".
Ba tare da gardamar komai ba na hau bayan
nasa na zauna. Shi kuwa sai ya bude biyu
daga cijin fuka-fukansa shida yai sama dani,
yana mai yi mini rumfa da fuka-fukai biyu.
Take na jiruwan saman ya daina jikani. Nan
fa muka fara keta giza-gizai muna ta tsala
gudu a cikin gajimare.
Abinka da al'amari na aljan a cikin abin da
bai wuce rabin sa'a ba muka iso farkon daji
na farko, wato dajin darul shazar inda
rikakken goggon biri yake koda aljani barzila
ya sauko kasa ya dira bisa turba nima na
sauko daga kansa sai yakoma bayana ya
rakube jikinsa na kyarma ace kyat ya fita da
gudu.
Al'amarin daya matukar bani mamaki kenan,
na juyo na dubeshi nace meye haka saboda
me zaka koma bayana ka ra kube, maimakon
ka wuce gaba kayimin jagora har izuwa inda
rikakken goggon biri yake?".
Yayinda aljani barzila yaji wannan tambaya,
sai ya dubeni muryarsa na rawa yace, "ya
shugabana ai bala'in dake cikin wannan daji
da zamu shiga yafi karfina domin a tarihi ma
in banda marigayi mahaifinka, babu
mahalukin daya taba ratsawa ta cikinsa ya
isa dajin gaba. Ai daga yanzu kaine mai
yimana jagora baniba domin ban san
komaiba acikin wannan daji".
Koda jin haka, saina yi murmushi na gyara
makaman jikina gami da zaman gurayena da
layu sannan na wuce gaba barzil na biye
dani tamkar dan farauta da karensa. Da fara
tafiyarmu a cikin dajin, sai na dunga jin
gilmawar wasu abubuwa a samanmu,tamkar
giftawar walkiya suna dira a can saman
karshen wadansu bishiyoyi masu tsawon
tsiya. A duk sa'adda muka daga kawunanmu
sama bama ganin komai. Al'amarin daya
firgita aljani barzila kenan ya kwakumi jikina
sai dana daka masa tsawa, sannan ya
sakeni.
Take na zare takubba biyu a jikina na fara
tafiyar sanda ina nazarin kowanne bangarena
gabas da yamma kudu da arewa da kuma
sama da kasa ina mai jiran ko ta kwana. Ba
zato ba tsammani sai naga wani jibgegen
biri ya taho kasa daga can kololuwar bishiya
zai dira akammu. Cikin tsananin zafin nama
na goce ina mai janye aljani barzila daga
gurin. Birin ya dira kasa yana mai kawo
mana wawan suka da faratan hannayensa
koda muka goce hannayensa gaba daya
biyun suka nutse a cikin kasa suka yi wani
rami zururu. Wato in ba don mungoceba da
cikin jikinmu hannayen nasa zasu lume.
Kafin birin ya sake yunkurawa tuni na fille
masa kai, ya baje a kasa matacce.
Kaico ashe na tsokano bala'I ne. Faruwar
hakan keda wuya saiga sauran 'yan uwansa
su shida suna saukowa kasa jif-jif tamkar
giwa ta fado. Kafin muyi wani yunkuri sunyi
mana kawanya, babu ta inda zamu iya
guduwa. Nan fa aka fara kallon-kallo
tsakanina da su, yayinda jikin dan uwansu
dana kashe ke malala a kasa tamkar an
bude magudanar ruwa. Kawai sai na dafa
kafadar aljani barzila yayinda yake ta
karkarwa, tamkar an tsomashi a cikin kogin
kankara, nace da shi, "Ka tsaya kyam a inda
kake kada kayarda ka gusa koda taku daya
ne"
Lokaci guda sai birirrikan su duka shidan
suka tasammana na na ruguntsume da a
zababben yaki da su suna masu kawo mana
sara da suka ni kuwa ina tarewa ta kowanne
bangare ina maida martani.
Haka dai muka wanzu muna ta artabu har
tsawon sa'a guda batare da na sami nasara
ba a kansu, suma kuma basu samu ba, abin
da ya tayar mini da hankali. Shine kokadan
babu alamar gajiya atare dabirirrikan tamkar
wasa jini suke , ni kuwa na tabbatar da cewa
idan aka kara samun wata sa'a guda nan
gaba zan iya gajiya likis su kaini kasa. Ana
cikin haka ne daya daga cikin birirrikan ya
sadado ta bayana ya shammaceni ya karta
mini farcensa a gadon bayana. Take wajen
ya dare jini yai tsartuwa saboda tsananin
zafin da naji bansan sa'adda na kwarara
uban ihuba, nayi kasa luuuu cikin wani irin
matsanancin hali mai kama da suma idanuna
na lumshewa koda ganin haka, sai birirrikan
suka yi caa a kanmu ni da aljani barzila da
nufin su tsinka gabobin jikinmu.
Ba zato ba tsammani, sai na yunkura da
kugiyata a sannan na fillewa birirrikan
kawunansu su duka shidan, take gangar
jikinsu ta zube kasa suka zama gawa. A
lokacin ne aljani barzila yai a jiyar numfashi
yana mai godiya da jinjina a gareni bisa
ceton rayuwarmu danayi, kawai sai yaga na
sulale kasa ina numfashi da kyar.
Cikin rudewa aljani barzila ya bude jakata ya
fiddo garin magani ya shafa a raunin gadon
bayana, jini ya daina zuba, sannan ya ruga
cikin daji ya samo itatuwa yazo ya kunna
wuta domin ta rage mini tsananin hunturun
sanyi dake kadawa a dajin.
Haka dai barzila ya zauna yana jinyata, har
izuwa tsawon lokaci, sannan yaje farauto
mini wani katon tsuntsu ya zo ya gasashi ya
bani naci. Sai da muka kwana uku a wannan
wuri ina jinyar raunina, barzila na kula dani,
sannan na sami karfin jikina. Koda naji na
warware sai na mike tsaye na kama shirye-
shirye na ce da aljani barzila, "Mike ka
kimtsa yanzu zamu ci gaba da tafiya domin
mu isa kogon da uban birirrikan nan yake,
kasan shi nake so na kashe na debi
kwakwalwar kansa".
Cikin kaduwa da mamaki aljani barzila ya
dubeni yace, "Haba ya shugabana, raunin
jikina fa bai gama warwarewa ba, yanzu
kana ganin cewa, zaka iya ci gaba da
gumurzu a haka?"
"Ko zan iya ko bazan iyaba, dole ne mubar
nan muci gaba da tafiya. Karkamanta cewa,
yau kwana uku kenan da kashe wadannan
birirrika, tabbas yanzu hankalin iyayensu a
tashe yake, tunda basu ga sun koma gidaba
kaga kenan dole ne su fito nemansu dasuzo
su ritsamu a nan gwara ace mune muka je
muka riskesu har cikin kogon da suke".
Yayinda aljani barzila yaji wannan batu, sai
yai ajiyar zuciya, yace, "Hakika maganarka
gaskiya ce".
Nan take barzila ya matso gareni ya
rankwafa na haye bayansa, na zauna ya
tashi dani sama muka kara gaba.
Kash! Rashin sani yafi dare duhu, ashe ma
duk wannan hira da muke yi iyayen birirrikan
dana kashe tuni sun iso inda muke suna labe
a bayan wata katuwar bishiya suna
hangenmu. Barinmu wajen keda wuya sai
suka fito daga inda suke boyen suka shiga
neman 'ya'yansu. Ai kuwa basu dade ba
suna neman suka hango mushen gawarwakin
wanda tuni ya gama rubewa, mikiyoyima sun
tsatstsagi iya rabonsu. Koda suka ga
wannan mushen sai suka takarkare suka
rafka kururuwa tsananin karar kururuwar
tasu ce ta firgita dukkanin halittar dake cikin
dajin. Tsuntsaye suka tashi daga inda suke
suka kama shawagi a sama dabbobi suka
kama guje-guje, na cikin rami suka firfito, na
kan bishiyoyi suka sauko. Aljani barzila dake
dauke da ni bai san sa'adda ya dimauce
baya rikito damu kasa, jikinsa na tsuma, ya
kasa ci gaba da tafiya, yayinda duk gabobin
jikinsa suka kama tsuma. A wannan lokaci
kuwa mun iso bakin kofar kogon birirrikan.
Cikin fishi na sauka daga kan aljani barzila
sannan na zare takubbana guda biyu na dubi
barzila nace, "Ni zan shiga cikin kogon
birinnan na jirashi a ciki, domin nasan cewa
cewa yana bayanmu kuma yanzu tuni yaga
gawar 'ya'yansa don haka a matukar fusace
yake. Idan zaka biyoni, idan kuma zaka nemi
wajen buya Ne, ka nema".
Koda gama fadin haka saina wuce kai tsaye
izuwa cikin wannan kogon dutse, shi kuwa
aljani barzila sai ya kama duru-duru yana
tunanin abinyi kafin ya ankara tuni na kule a
cikin kogon. Bazato ba tsammani sai barzila
ya dinga jiyo saukar wasu a bbubuwa masu
nauyi akan bishiyoyin baya jif-jif.
Cikin razana barzila ya ruga izuwa cikin
kogon yana mai kiran sunana, ko waigowa
banyi ba na saurareshi har ya riskeni. Sai da
muka isa karkashin kogon inda muka ga
kasusuwan bil'adama rututu a tsube waje
guda, sannan muka tsaya cak. Saboda
tsananin tsoro, sai aljani barzila ya shige
cikin tarin kasusuwan ya boye kansa, ni
kuwa sai na hada wuta sannan na kunna
fitilun itatuwa kogon ya gauraye da haske,
sannan na zauna ina mi harde kafafu tamkar
wanda ke hutawa a cikin gidansa. Jim kadan
da faruwar haka sai na ji saukar wannan biri
tare da matarsa a kofar kogon tamkar
faduwar giwaye, kawai sai suka shigo ciki.
Tun daga nesa suka hangoni a zaune, sai
suka tsaya cak, suka kura mini ido suna
masu mamakina.
Inda wadannan birirrka suna magana na
tabbata sai sunce wannan wane irin
hatsabibin bil,adama ne, mara tsoro.
Bayan yakashe mana yayanmu kuma har ya
iya shigowa cikin gidanmu ya zauna yana
jiranmu? Bayan biran sun gama nazarina, sai
mijin ya dakatar da matar tasa yayi mata
nunin ta tsaya a baya, kada ta biyoshi kawai
sai ya rugo da matsanancin gudu a gareni.
Koda ganin haka, sai na mike tsaye zumbur
na takubbana biyu na tsaya kyam a tsaye ina
jiran karasowarsa. Yayinda yarage saura
baifi taku biyar ba ya riskeni, sai ya daka
tsalle sama ya wara hannayensa ya saito
faratan hannayen nasa biyu da nufin ya
sokesu cikin wuyana. Cikin matukar zafin
nama na goce kuma na daka tsalle na dira
can gefe daya. Ai kuwa gocewar dana yi ce
tasa faratan nasa. Suka nutse cikin dutsen
kogon, sai ga shi ya ciro katon ya cisge
kaina. Nan fa muka fara kallon-kallo nidashi
domin kowannan mu ya fuskanci cewa ba
karamin gumurzu za a yiba, ita kuwa matar
tasa sai ta gyara tsayuwarta cikin nishadi da
gadara don ta tabbatar da cewa mijinta ne
zai sami nasara akaina.
Take goggon birin yasake afka mini, muka
ruguntsume da sabon azababben yaki yana
mai kawo mini sara da suka da faratan
hannayensa, ina karewa da takobina ina
mayar da martani a duk sa'adda makamaina
suka hadu da faratan nasa sai kaji kamar
karfe da karfe ne suka haduqn har tartsatsin
wuta ne ke tashi, kuma idan na daki jikinsa
sai naji kamar dutse na sara ko kwarzanewa
ba yayi al'amarin daya dugunzuma hankalina
kenan, na tabbatar da cewa yau fa na gamu
da gamona abune mawuyaci na tsira da
rayuwata. Sai da muka shafe rabin sa'a cif
muna wannan gumurzu dayanmu bai samu
nasarar komai a sannan ne kuma naji gajiya
ta fara riskata, al'amarin daya kara
dugunzuma hankalina kenan domin idan
banyi gaggawar daukar mataki ba a
koyaushe goggon birin zai iya hallakani
kawai sai na daka tsalle naja da baya, kuma
nayi wurgi da makamaina
......
Suleiman zidane kd
Littafe abdul aziz sani madakin gini...
Whatsapp 09064179602
.....
Koda ganin haka, sai goggon birin ya tsaya
cak yana mai mamaki, kuma ya kura mini
ido don yaga abinda da zanyi kawai sai yaga
na tsaya cak a waje daya, kuma ban zaro
wani makamin ba, koda ganin haka, sai birin
ya sake rugowa kaina ya afka mini da
dukkan karfinsa, ni kuwa sai na sauya salon
fada na shiga tsalle-tsalle da goce-goce ya
kasa cafkata, ko sarana, amma a duk
sa'adda ya kawo mini hari na goce, duk a
binda hannunsa ya buga walau dutse ko
bishiya sai sun tarwatse.
Nima sai na zamo kamar biri na dunga
shawagi a sama tamkar inada fuka-fukai a
haka ne na sami wata nasara na gabza
masa naushi a tsakiyar kansa ai kuwa sai
naga yayi baya taga-taga zai fadi, har layi
na dibarsa. Koda ganin haka, sai na cika da
farin ciki, na gane cewa a duk gaba daya
jikin birin babu inda za a taba ayi masa
lahani, face kansa.
Nan fa naci gaba da kaiwa kansa hari. Koda
birin yaga na gano lagonsa sai ya haukace
yaci gaba da kai mini wawan hari yana
kokarin hallakani da gaggawa. Nan fa
mukakicime da masifaffen gumurzu, har ta
kai cewa, ya sami nasarar saran kirjina,
kuma ya soka mini farcensa guda akan
cinyata. Take farcen ya nutse a cikin cinyata,
ya faso bayanta. Ni dai ban san sa'adda na
kwala kara ba, sa'adda jini da layi suka
kwasheni. Koda birin ya zare farcensa daga
cikin cinyata, sai jini yai tsartuwa dama tuni
kirjinna ma ya darejini na zuba. Kawai sai
na fadi kasa da baya na baje a kas, a
lokacin da numfashina ya sarke idanuna
suka kafe.
Koda birin yaga yasami wannan nasara, sai
ya juya ya dubi matarsa yai kururuwa, ita ma
sai tayi kururuwar don ta nuna masa farin
cikinta. Irin ya juyo ya taho gareni da nufin
ya tsitstsinka sassan jikina. Yayinda ya iso
kaina ya sunkuya zai cisge mini hannayena,
sai kawai yaga nayi zumbur na daka tsalle
izuwa samansa kafin ya dago kansa sama ya
kalleni, tuni na ta karkare na gabza masa
naushi da dukkan karfina a tsakiyar madikar
kansa take hannuna ya burma kan ya shige
ciki koda na zaro hannuna sai ga
gwakwalwarsa a cikin tafin hannuna take
birin ya sulale kasa matacce koda matarsa
ta ga abin daya faru sai ta juya ta falfala da
gudun tsiya, kafin kiftawar ido ta bace daga
cikin kogon.
A sannanne na sake yanke jiki na fadi kasa
ina numfashi da kyar, kamar raina zai fita.
Kawai saina ji motsi a cikin tarin kasusuwan
nan na mutane sai ga aljani barzila yai fitar
burgu daga ciki. Ni tunima na manta cewa
yana cikin kogon koda barzila yaga halin da
nake ciki, sai ya rude nan da nan ya
gaggauta yi mini magani. Sai da muka
kwana shida a cikin kogon dutsen aljani
barzila na jinyata, sannan na sami lafiya. Ba
tare da bata lokaciba muka yi shiri muka fice
daga cikin kogon, dama tuni na tanadi
kwakwalwar birin na adanata acikin jakata,
gangar jikin birin kuwa mun koneta ta
babbake ta zama toka, don kada ta damemu
da wari.
Kawai sai muka tasamma daji na biyu, wato
dajin shajaril mausuba inda zakanya mai
dauke da tsohon ciki take, da shigarmu cikin
dajin sai na umarci aljani barzila daya nemi
bishiyar da babu kamarta a tsawo mu hau
kanta mu buya a cikin duhuwar ganyayenta.
Batare da gardamar komai ba, aljani barzila
yacika wannan umarni.
Duhuwar ganyenta.
Dama a wannan lokaci farkon safiya ce,
muna nan labe akan bishiyar muka hango
'ya'yan zakanyar su uku sun fito farautar
abincin dazasu kaiwa mahaifiyarsu har suka
zo suka wuce kasan bishiyar da muke kai
suna ta shinshine-shinshinensu amma basu
ganmu ba. Sai da naga sun yi nisa daga
inda muke har sun bace mana da gani
sannan na umarci aljani barzila muka bar
kan bishiyar muka nufi hanyar da 'ya'yan
zakanyar suka fito.
Sai da muka yi tafiyar rabin sa'a sannan
muka iso bakin kofar kogon da zakanyar
take, da saukarmu a kofar kogon sai na
sauka daga kan aljani barzila na dubeshi
nace, ko zaka shiga kayi mini wannan aiki
ne, tunda zakanyar ce kawai da mijinta a
ciki?".
Cikin firgici aljani barzila ya dubeni yace
Haba ya shugabana kasani cewa, wadannan
dabbobi fa sihirtattu ne, kai kanka in ba don
kana da cikakken shiri ba baka isa ka
tunkaresu ba. Da shirin naka ma gashi da
kyar kake kai labari, ni a wa zan ce zan
taresu alhalin bani da koda rabin shirinka?
Ai sama tayiwa yaro nisa, sai kallo".
Yayinda naji wannan batu, sai na bushe da
dariya nace, "Hakika kayi gaskiya. Ka jirani
anan yanzun nan zan fito". Koda gama fadin
haka, sai na kunnan kaina cikin kogonn. Da
shigata sai naga ashe kogo ne mai tsananin
zurfi ko karshensa bana iya hangowa kawai
sai na ci gaba da tafiya a cikinsa abu kamar
wasa sai da na shafe wata rabin sa'ar ina
tafiya sannan na iso karshensa, inda nayi
arba da wannan mijin zakanya tsaye a
gabana ya kura mini idanu kawai ita kuwa
zakanyar na kwance a bayan, ita ma ta tsura
mini ido. Tun da nazo duniya ban taba ganin
zaki mai girma da kwarjini ba irin wannan.
Nan fa muka fara kallon-kallo nida zakin,
kowannenmu ya kame kamar babu mai rai a
cikinmu don babu wanda ya motsa. Daga
can sai na zare takubbana na durfafeshi kai
tsaye. Abin daya bani mamaki shine zakin
bai motsa ba, sai da yaga saura kiris na
riskeshi, sannan ya daka tsalle ya bangajeni
da kirjinsa. Duk da cewa na goce da zafin
nama sai daya bugi gefen kafadata, inda
kuwa mun hada kirji da tuni ya karya mini
kasusuwan kirjina.
Take nayi tsalle sama da baya na fado kan
dutse a matukar galabaice, idanuna na ganin
taurarin wahala. Kafin na mike tuni zakin ya
dako tsalle zai sake dira a kaina. Koda na
sake gocewa faratan hannayensa suka sauka
akan dutsen sai dutsen ya ratattake ni kuwa
na mirgina can bayansa na sake mikewa
tsaye zumbur ganin yadda wannan dutsen ya
ratattake ne hankalina ya dugunzuma
zuciyata ta karaya da samun abin da nazo
nema Nidai a iya yawon da nayi bantaba shiga daji
mai kwarjini da ban tsoro ba, tamkar dajin
shajaril maurud. Ba komai ne yabawa dajin
kwarjiniba, face wasu irin dogayen bishi yoyi
gami da tulun ganyaye a sama da suka cika
gami gami da duhuwa mai yawan gaske, ga
kuma tarin manyan duwatsu masu siffofin
ababan tsoro da kuma jibga-jiggan tsaunika.
Muggan dabbobin daji kuwa adadinsu ya
wuce kima sai dai ka gansu suna ta
gilmawa, in ba don a sama muke tafiya ba,
da sai mu yita yaki da su sai da muka yi
tafiyar sa'a hudu a sama cikin iska a dajin
na shajaril maurud, sannan muka jiyo wani
irin gagarumin gurnani na dodo gurmazu,
koda jin gurnanin wanda ya cika djin gaba
daya sai hantar cikina ta kada, duk da
jarumtaka da dakakkiyar zuciya irin tawa.
Shi kuwa aljani barzila gaba dayan jikinsa ne
ya dume da zafi, tamkar an tsomasi a ruwan
dumi mai tiriri, ya kama karkarwa bai san
sa'adda ya saki fitsarin firgita ba. Duk da
cewa a tsorace nake, sai da dariya ta kwace
mini, na ce, "Haba namijin duniya, ai ka
karya alkadarin jarumtakarka wadda kayi a
baya, domin bai kamata ba ace tsoro har
yasa ka saki fitsari saboda kawai ka ji
gurnanin dodo gurmazu ba".
Cikin karfin hali, da rawar murya barzila
yace, "Haba ya shugabana, ai bama fitsari
ba, ko kashi na saki bai kamata kayi mamaki
ba, Katuna fa cewa shi fa dodo gurmazun
nan a halin yanzu duk duniya babu wata
halitta mai karfin damtsensa da karfin
sihirinsa. An ce komai kaurin bishiya, idan
ya nausheta da hannu daya, saita ratattake,
ta fadi kasa idan kuwa ya kwarara ihu,
girgizar kasa ake yi, tsawa da walkiya na
amo daga cikin bakinsa. Komai yawan maza
a cikin dakika biyar yake tarwatsasu, walau
rundunar bil'adama ko ta aljanu". Kawai sai
nayi ajiyar zuciya, nace "Lallai kuwa baka yi
laifi ba, domin tsoro wajibine, amma fani
bana tsoron bala'I dan babu Wanda
banganiba, sai dai na firgita da shi. Ai kawai
muci gaba da tafiya, ina so ka durfafi inda
kake jiyo sautin wannan gurnani".
Cikin matukar tsoro aljani barzila yace,
"Banki tatakaba ya shugabana, amma dai
katuna cewa, "Riga kafi yafi magani. Bai
kamata mu tari dodo gurmazu gaba da gaba
ba, zai fi kyau mu dunga yin sanda da labiya
har mu isa inda yake, ai shi yaki dan zamba
ne a duk sa'adda abokin gaba ya fara ankara
da abokin gabarsa, to yana iya samun
hikimar da zai iya samun nasara akansa da
wurwuri".
Batare da wata gardama ba, na amince da
wannan shawara, saboda haka sai aljani
barzila ya sauko kasa ya dira bisa turba,
nima na sauko daga kansa muka fara tafiya
sanda muna leke-leke, wani lokacin ma har
kwanciya muke a kas muna tafiya da ruf da
ciki.
Kaico! Rashin sani yafi dare duhu, ashe duk
wannan tafiyar dudduke da mukeyi dodo
gurmazu ya hangomu tun daga can nesa,
saboda kwarin idanunsa yana iya hango abin
dake tafiyar sa'a shida a bayansa ko
gabansa, sannan duk irin abin da ya jingina
ajikinsa sai kalar jikinsa ta koma irin launin
abin sak komai hasken da ke wajen, ido
bazai iya shaidashi ba.
A wannan lokaci da muke tafiyar ruf da ciki,
dodo gurmazu na can sama bisa wata
gabjejiyar bishiya mai tsananin girma da
tsawo. Ni kam na tabbatar da cewa, wannan
bishiya babu ta biyunta a duniya, domin ko a
tarishi ban taba jin labarin bishiya irintaba.
Haka dai muka ci gaba da tafiyar ruf da ciki
har muka iso gaban wannan narkekiyar
bishiya, amma bamu ga komai ba, kuma
bamu sake jin gurnanin dodo gurmazu ba.
Mun dade a kwance muna kasa kunne ko
zamu ji wani motsi, amma ba muji ba.
Daga can sai muka mike tsaye na dubi aljani
barzila nace, "Abin da zamu yi kawai mu hau
can saman wannan bishiya mu tsaya in dai
muka yi haka zamu iya hango dodo gurmazu
a duk inda yake domin zaton da nake ba a
nan kusa yake ba. Yana nesa da mu ne".
Koda jin wannan shawara tawa, sai barzila
ya cika da murna, yace, "kwarai kuwa kayi
tunani mai kyau, haka za a yi" nan take na
sake hawa bayan barzila yai sama dani, sai
da muka kure tsawon bishiyar sannan muka
sauka a kan wani katon reshenta guda. Cikin
hanzari aljani barzila ya zaro kwari ya dana
akan wannan katuwar baka tashi ya tabe
bakan ya shiga kalle-kalle ko zai hango dodo
gurmazu ya sakar masa harbi. Ni da Nake
bayan barzila sai na daga wani gatari nawa
sama na tsaya cak! A waje daya ina kallon
gabas da yamma, kudu da arewa, kuma ina
leko kasan bishiyar. A binda bamu saniba
shine, munyi aikin banza domin kuwa mun
kulle kofar gida da barawo a ciki, domin
kuwa tsakaninmu da dodo gurmazu bai wuce
taku uku ba. Ashe shi ma yana kan bishiyar
amma da yake kalar jikinsa ta saje da kalar
jikin bishiyar ko kadan bamu ganshi ba.
Kwatsam! Ba zato kuma ba tsammani, sai
dodo gurmazu ya sauya kalar jikinsa izuwa
ainashin tasa ta gaskiya, ya baiyana daf da
aljani barzila. Koda barzila yai arba da dodo
gurmazu yaga irin kwar jininsa da muninsa
sai ya firgita kuma ya dimauce, bai san
sa'adda ya saki kwari da bakan dake
hannunsaba ya juya da nufin ya bude fuka-
fukansa ya tashi sama, amma sai dodo
gurmazu ya cabo jelarsa cikin zafin nama,
sai ga barzila na reto a sama, tamkar dan
biri na wasa.
A dai-dai wannan lokaci ne na dako tsalle
daga inda nake tsaye na taho a sama zan
kirbawa gurmazu sara a tsakiyar kansa,
amma sai gurmazu ya mangareni da daya
hannun nasa, na rikito kasa, tun asama na
fita daga haiyacina, naji kamar anyi mini
kanshin mutuwa. Ai kuwa ina fadowa kasa
na sume. Nidai ban san abin daya faruba
daga sannan sai farkawa nayi na ganni a
cikin katon keji tare da aljani barzila, da
kuma wadansu aljanu kimanin su dubu biyu,
duk suna ta faman rusa kuka shi ma aljani
barzila sai ya tayasu kukan.
Koda barzila yaga na farfado, sai ya dubeni
a fusace, yace, "Kaga irinta ko, ai dama na
gayamaka bamu isa mukawar da dodo
gurmazu ba, ga shi yanzu ya kamamu.
Wadannan aljanu duk fursunoninsa ne, kuma
sun gaya mini cewa, sudubu arba'in ne ya
kamosu, kullum yana diban biyar yana
cinyewa, yanzu saura su dubu biyu kacal,
kaga kenan muma mun zama abincin sa.
Haka kuma sun tabbatar mini da cewa babu
wani makami ko sihiri da zai iya karya
wannan keji, har mu sami damar fita daga
cikinsa. Abin da zance da kai kawai shine,
ince koka bar wasiyya a gida kafin muyi
wannan tafiya?".
Yayinda naji wannan tambaya, sai na bushe
da dariya, al'amarin daya baiwa dukkanin
fursunonin aljanun mamaki kenan, domin
gashi su a matsayinsu na aljanu, suna kuka
saboda sun shiga bala'In da babu fita, amma
ni a matsayina na bil'adama ina dariya. Ti
me nake takama dashi? Shin ina zaton zan
iya fita ne daga cikin wannan masifa? Amsar
da basu sani ba kenan, amma dai ai tunda
suna tare dani zasu zuba ido su ga iyakar
gudun ruwana.
sHIN HASANUL MAUZUR DA ALJANI
BARZILA ZASU KUBUTA DAGA HANNUN
DODO GURMAZU, HAR HASANUL MAUZUR
YA KASHE WANNAN GIWA TA DODO
GURMAZU, YA YANKO HARSHENTA?
WADANNE SAMARI Ne ZASU SHIGA GASAR
NEMAN AUREN GIMBIYA SHULAIRA, KUMA
DAGA CIKINSU WAYE ZAI CI GASAR YA
ZAMO MIJINTA.
Muhadu a TARWATSA MAZA littafina biyu
don jin cigaban wannan kasaitaccen labari.
Typing Suleiman Zidane kd
Whatsapp phone number 09064179602
ππππππππππππ
*_Haiman Raees_*
_*Phone:*_
08185819176
_*Web:*_ www.haiman.com.ng
_*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees
_*Twitter:*_ @HaimanRaees
_*Instagram:*_ Haimanraees
_*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com