SHARRORIN BOKAYE

SHARRORIN BOKAYE :
***********************
Alhamdulillahi na rubuto wannan ne ba don alfahari ko cin mutuncin wani ko wasu ba, sai domin fadakar da al'ummah game da sharrin bokaye da kuma hanyoyin da suke bi wajen dulmiyar da al'ummah cikin duhun shirka da kafirci. 

Acikin jerin wasu ruqyah da muka gabatar acikin kwanakin nan, an samu mutane da dama wadanda chutar dake jikinsu ta shafi bangaren sihiri ne. Kuma Falillahil Hamdu, bayan gudanar da karatun Alqur'ani Mai girma, wasu daga cikinsu an samu shaitanun Aljanu sunyi magana ta bakinsu. Amma wasu kuma basuyi magana ba, sai dai sun samu saukin abinda ke damunsu. 

Daga cikin wadanda nasu sukayi magana sun fa'di abubuwa da dama. (duk da cewa shaidanu suna da Qarya kuma sukan yi Qarya domin ha'da husuma atsakanin jama'a). Sukan yi bayanin cewa an turosu ne domin si chutar da marar lafiyan. 

Wasu daga cikinsu mukan tsaya mu saurari abinda suke fa'da, musamman saboda alamomin dake nuna gaskiyarsu cewa turosu din akayi ta hanyar tsafi (sihiri) kuma mukan gane cewa ayoyin karya sihiri sunfi yin tasiri akan irin wadannan din, ba wai zallar ayoyin ruqyah ba. 

Akwai wasu wadanda sukayi bayanin cewa wani saurayi ne ya turosu jikin budurwarsa bayan ta rabu dashi saboda miyagun halayensa da zafin ransa. Shine yaje wajen wani boka a kauye domin wai ayi mata wani tsafi mai suna "Karfa".

Wato ayi mata sihirin da zai sanyata tsananin baqin jini har sai ta rasa wanda zai aureta, sannan su rabata da iyayenta da danginta har ta rasa wanda zai damu da ita balle ayi mata maganin chutar. 

Na tambayi su shaidanun game da hanyar da bokan yake bi wajen mu'amala dasu, sai suka ce "Sun hanashi yin sallah, kuma suna sanyashi yin zina ko yaushe, kuma yana yi musu yanka suna shan jini".

Sannan akwai na wata yarinya (Matar aure) wacce bayan anyi karatu sai shaidanun suke cewa wata ce taje wajen boka tasa akayi sihiri aka turosu. Bayan sun sha wahala (anyi karatu sosai) shine suke tona asirin bokan suka ce shi mazinaci ne. Yakan yi zina da duk matar da taje wajensa kafin yayi mata aiki, kuma ba ya sallah ba ya azumi.

Kafin wannan din akwai wanda aka kawoshi (Namiji) bayan an karanta musu ayoyin Alqur'ani sai suka ce "Kafin bokan ya turasu jikin yaron, sai da suka sanyashi yana yin takalmi da Alqur'ani. Wato yana tattaka hizifi talatin a kowanne sawu daga sawayensa (Allah shi kiyayemu daga shirka).

Akwai kuma wasu shaidanun da suke ce nasu bokan sai yayi zina da muharramarsa ('yarsa ko Qanwarsa ko mahaifiyarsa) kafin su yarda su amsa kiransa. 

Dalibanmu na Zauren Fiqhu Whatsapp sun saurari wasu audios dake kunshe da irin wadannan abubuwan da dama. 

Kuma na kawo wannan ne duk domin jan hankalin ire-iren Matan dake zuwa wajen Malaman tsubbu (bokaye da 'yan duba) domin neman biyan bukatarsu ta alkhairi (kamar neman farin jinin aure) ko ta sharri (Haukata kishiya, mallakar miji, wofintar da kishiya ko 'ya'yanta).

Har ma Mazajen dake zuwa wajensu (kamar 'yan siyasa, 'Yan kasuwa, da Ma'aikata) masu zuwa don hassada da mugun nufi akan abokan aikinsu ko makwabtansu ko domin samun nasara akan wata bukata. 

Kuji tsoron Allah ku sani cewa su bokaye fa makiyan Allah ne da Manzonsa (saww). Kuma wakilan shaidan ne. Suna taimaka masa wajen dulmiyar da al'ummah acikin shirka da kafirici. Zaka gansu sunyi shigar Malamai amma ba Malaman bane. 

Idan kaje neman addu'a wajen mutum kaji yana cewa za'a neman rago kalar baqi-Qirin, ko baqar kaza, ko baqin taure, ko kuma ya baka wasu layoyi wai kaje ka binnesu a Qabari, to kaji yace sai an nemo Qasar Qabari, to tabbas wannan ba Malami bane boka ne kuma matsafi.

Kuma bayani yazo daga Manzon Allah (saww) yace idan kaje wajensa kuma ka yarda da zancen shikenan ka kafirce ma dukkan abinda Annabin namu yazo dashi (saww). 

Ya Allah ka ganar damu, ka kiyaye mana imaninmu ameen. 

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (2) 07/10/2018 27/01/1440.

Zaku iya tura ma jama'a domin isar da saqo ba tare da chanza ko da harafi guda ba.


Post a Comment (0)