Takalmin Buba Danbauri

✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴
 *ABOKIN FIRA * 
 *Rubutawa:* _Dr. Muhammad Mansur Sokoto_
 


 
 *DRS NA 006* 
 *Takalmin Buba Danbauri*
A wani gari da ke gabar teku mai suna Tarabulus aka yi wani mashahurin attajiri, dan kasuwa, marowaci, da ake kira Alhaji Buba Danbauri. Yana da wasu tsofaffin takalma da ya kasa
canjawa saboda matsolancinsa. Saboda yawan faci da ya yi ta yi
masu, takalman sun yi nauyi sosai. Sun kerkece ta ko ina, amma
ba ya iya rabuwa da su, don kada idan ya cire su ya ba wani. Duk garinsu kowa ya san da wadannan takalman nasa har akan buga misali da su.
Watarana Alhaji Danbauri ya yanke shawarar rabuwa da
takalman nan nasa don ya huta da tsegumin mutane. Danbauri ya dauki takalminsa ya ajiye shi a wani makewayi inda mutane ke zuwa don biyan bukatarsu. Ya ce, watakila a samu wani
mabukaci da zai dauka. An yi daidai wani dan Sarki ya shiga wurin ko da ya fito varawo ya dauke takalminsa. Da Askarawa suka ga takalmin Danbauri sai suka je suka kama shi suka
tuhumce shi da satar takalmin dan Sarki, suka yi masa matsiyacin duka sannan suka kai shi ga Alqali aka sa ya biya kudin takalmin da aka sace, kuma aka daure shi. Daga bisani aka sake shi kuma aka ba shi takalminsa.
Sai ya je ya jefa su a cikin Juji. A kan hanyarsa ta dawowa gida ya shiga kasuwa ya sawo wasu irin manyan kwalaben karau
da turaren Almiski a cikin su, da nufin idan ya dawo gida ya aika da su kasar waje don a sayar ya samu gagarumar riba. Da ya zo gida ya shanya manyan kwalaben nan a tsakar gida sai ya ji ana
sallama. Kafin ya amsa sai ya ji an kyaro masa takalminsa ana cewa, ga takalmanka nan barawo ya sace, na tsinto maka su.
Kyararas! Takalman sun fada kan kwalaben turare duk sun kashe su. Ya ruga da gudu bai ga kowa ba. Ashe wani bawan Allah ne ya san shi kuma ya yi haka da kyakkyawar niyya don ya yi amanna Danbauri ba zai iya yar da takalminsa ba. Kuma tun da ya jefa masa su ya tafiyar sa.
Alhaji Danbauri ya ji duk ya tsani takalmin nan sai ya jefa shi a wata magudanar ruwa kusa da gidansa, yana ganin ya huta ba wanda zai sake ganin takalmin. Bayan ‘yan kwanaki kadan sai
magudanan ruwa na gari duk suka toshe. Aka zo da ma’aikatan shara suka tone magudanai, sai suka tsinci takalmin Alhaji Danbauri. Nan take aka kai karar sa ga Alqali, ya sa aka yi masa
bulala gami da tara, da zaman fursuna na wata daya. Bayan ya kare zaman fursuna sannan aka hannunta masa takalminsa.
Alhaji ya shiga damuwa matuka. Ya zauna ya yi tunani sai ya je ya jefa takalmin nasa a teku. Bayan ya wuce wani mai kamun kifi ya zo da homarsa. Garin kama kifi sai ya farauto
takalmin Alhaji. A ransa sai yace, lallai wadannan takalman sato su aka yi. Bari in maida ma sa da shi na san zai ji dadi sosai. Da aka kawo masa shi. Sai ya dora shi a kan Katanga don ya sha iska
kafin ya yanke shawarar yadda zai yi da shi. Sai wata Mage ta zo ta gan shi kamar nama ta sharba ta ruga aguje tana tsallaka gidajen mutane. Ko da ta yar da shi sai ya fada kan wata mata mai ciki, ta firgita ta suma har ta yi barin cikin nata. Maigidanta
ya dauki takalmin nan ya nufi kotu wurin Alqali. Aka kira Alhaji ya yi rantsuwa bai san yadda aka yi ba, amma kuma shaidu sun tabbatar takalminsa ne. Don haka, alqali ya yi masa tara, sannan ya sa shi biyan diyya, ya mayar masa da takalminsa.
Kashegari sai Danbauri ya fita bayan gari da nufin ya yi gina ya rufe takalmin nan ya huta. Da ya tafi bayan gari bai sani ba an yi kisan kai, kuma an tarar da wata jakar kudin wanda aka kashe an rufe ta cikin kasa daidai wurin da aka yi kisan. Don haka sai
Askarawa suka labe suna jiran wanda zai zo ya tona don ya dauki kudin su kama shi, tun da sun san shi ne ya yi wannan ta’addanci. Da ya zo sai ya ajiye takalminsa, ya sa fartanya yana gina. Sai suka yo wuf! Suka ce, da wa Allah ya hada su ba da shi
ba. Danbauri ya sha dan karen duka kuma ya kasa kare kansa.
Daga karshe aka kai shi wurin Alqali ya daure shi tare da biyan tara mai nauyi wadda ta kusa ta tsiyata arzikinsa.
Da Alhaji ya ga duk dabaru sun kure masa, sai ya bari sai da dare ya raba ya fito ta jikin gidansa yana gina don ya rufe takalmin nan, sai makwauta suka ji karar fartanya suka fito suka
kama shi sai ya ce, shi fa yana gina ne don ya rufe takalminsa. Ba
su yarda ba. Suka ce daman jiya an kama shi da satar takalman dan Sarki don haka suka kira Folisawa suka kama shi. Kuma karshen labarin dai ba ya da dadi.
Daga karshe Alhaji Danbauri ya tafi da kansa wurin Alqali ya kai karar takalminsa. Ya ce ma Alqali don Allah ka rubuta takardar barranta tsakani na da wannan la’anannen takalmi. Ya azabtar da ni, ya halaka mani dukiya, kuma ya zubar min da mutunci. Daga yau ba ni ba shi, kuma duk abinda ya janyo babu ruwana.

 *Darasi:*
▶ Rowa sanadin tsiya ce

▶ Wanda bai ji bari ba ya ji hoho!

▶ Wanda ya taka sawun barawo shi ma barawo ne
Post a Comment (0)