TARIHIN HAMSHAKIN MATAFIYIN DAYA ZAGAYE SASSAN DUNIYA, IMAM MUHAMMAD IBN BATTUTA.

TARIHIN HAMSHAKIN MATAFIYIN DAYA ZAGAYE SASSAN DUNIYA, IMAM MUHAMMAD IBN BATTUTA.

Tare da SADIQ TUKUR GWARZO
08060869978

A yau, muna farin cikin fara kawo muku tarihin babban matafiyin duniya, wanda yaga tudu yaga kwari, ya kuma kwashe shekaru ashirin da hudu yana ta fagafniya da yawace-yawace a sassan duniya, sannan daga bisani ya rubuta taqaitaccen tarihin tafiyar sa a wani littafi maisuna "RIHLA".
Kamar yadda hausawa ke cewa tafiya mabudin ilimi, to haqiqa ta hanyar tafiye-tafiye, Imam ibn Batuta ya tara dumbin ilimin da ayau sai an tara dumujin farfesoshi ba'a samu rabin ilimin saba.
Cikakken sunan sa shine Abu Abdullahi Muhammad Ibn Abdullahil Lawatit Tangi ibn Battuta, amma yafi shahara da sunan Muhammad ibn Battuta. An haifeshi a ranar 25 ga watan fabrairu na shekarar 1304, a wani da ake kira Tangier dake qasar Morocco a yanzu.
Ibn Battuta ya samu ilimin addinin islama a qarqashin tsangayu masu bin mazhabar imamuna Maliku, inda kuma a watan yuni na shekarar 1325 ibn Battuta ya kamu dason tafiya qasar Saudiyya don yin aikin Hajji, alokacin kuwa yana da shekaru 21 ne kachal da haihuwa. Allahu Akbar!
Abin mamakin shine, a wancan lokacin, dukkan mai son risqar birnin Makkah daga garin Tangier, sai ya shafe watanni goma sha shidda yana yawo a dazuka da sahara sannan zai isa. Amma hakan bai tsorata ibn batuta ba, hasali ma shi kadai ya tattara 'yan komatsan sa yayi haramar fara wannan gagarumar tafiya mai cike da hadari. Ga abinda ya rubuta dangane da hakan a farkon littafin RIHLA.
"Na fara rptafiya ta ne ni kadai, bani da kowa dake biye dani, babu wasu matafiya kuma da nake bi. Ina tafiyar ne cikin zumdi da qwarin guiwa, saboda tsananin son yin tafiyar ya cika mini zuciya. Wannan kuma shine silar data sa na dauki qaddarar rabuwa da masoyana na gida, mazan su da matsan su kamar yadda tsuntsaye ke barin sheqoqin su. Iyayena sunyi matuqar shaquwa dani, wandaa hakan ke nuna rabuwar mu zan sanya damuwa a zukatan su. Hakika kuma rabuwa dasu yayi matuqar sani damuwa, amma haka nan na tsallakesu cikin jimami"
Sannu a hankali, ibn Batuta na tafiyar sa a dokar daji, wani wurin ya tsallake ruwa, wani wurin kuma ya kutsa kai cikin sahara har ya isa wani gari mai suna Tlencan, anan ne kuma yaci karo da wasu tarin matafiya wadanda wasunsu ke maniyyata ne izuwa kasar Sa'udi Arabiya don gudanar da aikin hajji. Kun san a wancan lokaci, tafiya mutum daya nada matuqar hadari saboda dumbin ababen tsoro daka iya faruwa, kamar misalin 'yan fashi da masau farautar bayi, ko muggan dabbobin daji, shiyasa akanyi dabarar hada gungu na matafiya, wanda za'a samu sadaukai a ciki, wadanda zasu iya tarar duk wani hatsari da zai iya fadowa.
Ibn Batuta, ya bayyana mana cewa acikin wadannan matafiya, akwai wadanda suke haye bisa dawakai, akwai na kan jakuna, harma dana kan raquma. A gurin wasu mutanen , haduwa da wannan ayari babbar ni'ima ce saboda tsira daga sharrikan tafiya, amma a gurin Ibn Battuta, wata kafa ya samu ta sanin abinda bai sani ba daga wurin wadannan matafiya.
Ibn Battuta yace Ayarinsu ya dunguma bisa hanya, tafiya akeyi babu qaqqautawa. Shikuma matsar mutane yakeyi don jin labari, da koyon ilimai. A haka suka iso gavar kogin Algiers inda akace yawan Ayarin ya qaru sabili da hadewar wata tawagar matafiya da tasu, sannan suka dunguma bisa hanya baki daya.
A wani gari mai suna Bijaya, Ibn Battuta ya kamu da rashin lafiya. Sai wasu abokan tafiyar sa suke shawartar sa da ya sauka a wannan garin ya huta. In yaso idan ya samu lafiya sai ya nemi wani Ayarin yacigaba da tafiya. Amma Ibn Battuta yace sam haka bazata faru ba, shine ma yake cewa "Idan har Allah Ta'ala ya qadarta mutuwata, ina fatan ta sameni alhali ina bisa hanya, fuskata tana fuskantar garin Makkah" don haka sai aka kyaleshi aka cigaba da tafiya.
Bayan tafiya tayi tafiya ne, sai ayarin ya risqi wani gari mai suna constantine, wanda yake wani gari ne babba a wannan yanki. Anan ne akace Ibn Battuta ya samu damar ganawa da gwamnan garin, harma gwamnan ya tausaya masa ya bashi kyautar kudi da kuma kayan sawa na masu kyau don ya sauya kayan dake jikinsa wadanda sukayi cidin-cidin kuma suka yayyage. Ibn Battuta yaji dadin wannan kyauta, kuma ya bayyana kyautar a matsayin kyauta ta farko da akayi masa a halin tafiyarsa.
Bayan sunyi hutu kadan a garin sai suka cigaba da tafiya, anan ne kuma akace rashin lafiyar Ibn Battuta ta qara yin tsamari, inda har saida takai baya iya zama akan sirdi, sai da abokan tafiyar sa sukayi dabarar daureshi da igiya yana bisa doki don gudun fadowa sannan akaci gava da tafiya sannu a hankali har suka risqi wani hamshaqin gari mai suna Tunis. A wannan lokaci rashin lafiya ta galabaitar da ibn batuta sosai, shine ma yake cewa "zuciyata ta cika tsananin baqin ciki saboda ciwo da yake damuna. Idanuna sun wanzu zubar da hawaye, na wanzu cikin kadaici da bacin rai. A haka wani daga cikin mahajjata ya fahimci halin da nake ciki, shine ya tunkaro ni da gaisuwa gami da zantuka na abokanta, ya wanzu yana rarrashina a haka har muka shiga cikin garin"
A cikin garin ne kuma ibn Battuta ya bayyana Tunis a matsayin qasaitaccen birni wanda yake dauke da dogayen masallatai ginannu, da fadoji na alfarma da kwalejojin ilimi gami da lambunan shaqatawa masu kyau. Ibn Battuta yace birnin Tuniss gari ne wanda ya shahara a fannin al'adu da malamai na fannonin ilimi. Sannan kuma gavar teku ce da akebi don daukar kayayyaki misalin Bayi, hatsi, man zaitun, fata da alharini daga Afirka ta yamma izuwa sassan duniya.
Ibn Battuta ya shafe watanni biyu a garin Tunis, a wata makaranta, inda yayi jinya daga baya kuma ya shiga fafutikar daukar darasi bayan ya samu lafiya.
Daga qarshe, Ibn Battuta yabar Tunis yana cikin wani Ayarin matafiya gagarumi wanda yake dauke da sadaukai kala-kala na gwamnan garin wadanda zasu basu kariya daga Mahara da larabawa 'yan tawaye, sannan kuma Ibn battuta ya samu tagomashi babba a wannan ayari, inda har aka nada shi Alqalin ayarin duk kuwa da kasancewar sa matashi mai qananun shekaru.
A cikin wannan halin tafiyar ne suka keta ta kasar libya, suka fara yunkurin ketawa ta garin Tripoli. A nan ne kuma Ibn Battuta ya nemi auren 'yar wani na hannun damar gwamnan Tunis wanda shima yake haramar zuwa aikin hajji, sannan kuma garin Tripoli aka gabatar masa da budurwar tasa, amma kuma sai akace sabani ya shiga a tsakanin ibn battuta da sirikin nasa abinda yayi sanadiyyar warware maganar auren, daga bisani Ibn battua ya nemi auren 'yar wani Malami kuma mahajjaci dake cikin tawagar wanda ya fito daga wani gari waishi Fez, wannan mata kuma itace matar ibn Battuta ta farko.
Ibn Battuta yace sun bar garin Tripoli kadan, sai sukaga qura ta turnuqe sama, wasu gungun mahara 'yan ta'adda suna fuskanto su riqe da muggan makamai. Amma Ibn Battuta yace cikin ikon Allah sai wannan runduna ta zagaye su ba tare da anyi wani artabu ba. Daga nan kuma basu qara cin karo da wani abu ba har suka isa karshen gabashin kasashen larabawa, kimanin tafiyar mil dubu kenan daga garin su Ibn Battuta Tangier, wanda yayi dai-dai da watanninsa tara rabonsa da gida, sannan kuma sauran sa watanni takwas ya risqi kasar saudiyya, don haka sai yayi shawarar leqawa garin Cairo (Alqahira) na qasar egypt don yawon bude ido.
Ibn Battuta ya bayyana Alqahira a matsayin gari mafi girma a duniya bayan qasar china a wancan lokaci. Inda ya kimanta mazauna garin da cewa adadinsu ya tasamma mutum dubu dari shidda. Ya kuma ce garin shine mafi girma sama da duk wani garin larabawa a duniya a wancan zamani.
Daga nan tawaga ta dora da tafiya, inda suka sauka a wani qasaitaccen gari mai suna Alekzandariya. Gari qayatacce wanda yake a gavar teku inji Ibn Battuta. A wannan shekara ta 1326 ne ibn Battuta ke samun tarihin cewa Sarkin Alekzandariya asalin sa bawa ne wanda ya kwace mulki daga hannun ubangijinsa tun ashekarar 1260, sannan kuma yayi nasarar yaqi da mongwalawa, wasu mayaqa wadanda suka qwace garin bagadada da sauran garuruwan musulunci. Don haka a wancan lokacin, sarkin Alekzandariya ke mulkin qasashen egypt dana syria.
A garin alekzandariya Ibn Battuta yace ya hadu da wasu manyan mutane guda biyu. Na farko shine Imam Burhanuddin wanda yayi hasashen cewar Ibn Battuta shine matafiyin duniya, har ma yace masa "Na fahimci kana son yin tafiye-tafiye, don haka ina ganin cewa zaka samu damar ziyartar yanuwana fariduddin a indiya, da Rukunuddin a birnin Sind da kuma Burhanuddin a China. Dukkan su ka isar min da gaisuwa ta agaresu". Daya mutumin kuwa sunan sa Imam Murshidi, shine kuma wanda ya fassarawa Ibn Battuta wani mafarki daya tava yi a garin, inda Iman Murshidi ya sanar dashi cewar ma'anar mafarkin shine Ibn Battutan zai zamo shahararren matafiyin duniya...THIS IS A KHUTBAH WHICH WAS GIVEN BY ONE USTAZ FROM OSOGBO, OSUN (NIGERIA)
 
What a touching KHUTUBAH please if time allows you read it. 
It's worth a REMINDER;

Forwarded as received.

"Every human is a slave. You're either a slave of your desires or a slave of ALMIGHTY-ALLAH. You either live life by your rules or the rule of ALMIGHTY-ALLAH.

How can the heart travel to God if it's chained by its desires? 

O' son of ADAM! Sell this World for the HEREAFTER and you win both, sell the HEREAFTER for this world & you lose BOTH. #DEEN OVER DUNYA

IBN QAYYIM AL-JAWZIYAH

ISLAM is not a buffet where you pick and choose what suits you. Don't obey your desires. Obey ALMIGHTY-ALLAH.
"Imprisoned is he, whose heart is imprisoned from ALMIGHTY-ALLAH. Captured is he, who is captured by his desires." 

FUDAYL IBN IYAD was asked "What do you find the strangest of all things?" He said: The heart that knows ALMIGHTY-ALLAH, yet still disobeys Him 

Don’t miss SALĀH for the sake of people. You were BORN & will DIE alone, you’ll go to the GRAVE alone & be questioned alone on JUDGMENT Day
1
الْأَخِلَّاءُ يَوْمَئِذٍ بَعْضُهُمْ لِبَعْضٍ عَدُوٌّ إِلَّا الْمُتَّقِينَ
Close friends, on that Day, will be enemies to each other, except for the righteous and GOD-FEARING..." •[Surah Az-Zukhruf:67]

FAJR you're asleep, ZUHUR you're busy, ASR you're tired, MAGRIB you're watching tv, ISHA you're eating. You can dodge PRAYER, but not DEATH.

We prepare for uncertain matters in our life like MARRIAGE etc but do we prepare for the one event that is definitely going to happen #DEATH 

The first thing a slave will be held to account for is SALAH. If we fall short on that, then we will fall short on what's to come.

FAJR: Do not fear missing sleep. Fear a day in which there will be no SLEEP.”😔

Expecting PARADISE whilst neglecting PRAYER, is like waiting for a TRAIN to arrive at the AIRPORT. Remember to pray DHUHR

Everyone DREAMS to be in JANNATUL-FIRDAUS, but ALMIGHTY-ALLAHﷻ says:
لَّيْسَ بِأَمَانِيِّكُمْ 
PARADISE is not obtained by your wishful thinking •[An-Nisa 4:123] #work hard 4 HEREAFTER 

"If you could hear the sound of the pens of the ANGELS writing your name among those who remember ALMIGHTY-ALLAH, you'd die out of joy." -IBN AL-QAYYIM 

This DUNYA Is Not A Resting Place 👉It's A TESTING Place! #Earn GOOD DEEDS!

The world is a prison for the believer and a PARADISE for the unbeliever". [MUSLIM] Your release here, sooner or later will be coming to an end.

IBN AL-QAYYIM(رحمه اللّٰه):
"He whom ALMIGHTY-ALLAH has predestined to enter PARADISE, the reasons which will cause his entrance shall spring from calamities;

He whom ALMIGHTY-ALLAH has predestined to enter the HELLFIRE, the reasons which will cause his entrance shall spring from lusts” 

Get used to a rough life, for luxury does not last forever. -UMAR IBN AL KHATTAB 

Do not be overly pleased by easy times. Verily, GOLD is tested for its purity by fire. Likewise,a righteous servant is tested by tribulations

It pains me to see born MUSLIMS chasing the lifestyle of the disbelievers by drinking, clubbing, getting high etc.

Why do you think reverts run away from that life to the deen of ALLAH. Run back to your Lord for His mercy overcomes His wrath.

How long will the person be happy with his worldly life?..Knowing that his ultimate home is the grave"

No matter how beautiful your face is, you will still be the food of worms when you are buried. Set aside your arrogance & remember your grave

Every single limb & organ in your body will speak up & bear witness against every action you committed in this DUNYA 
مَّا يَلْفِظُ مِن قَوْلٍ إِلَّا لَدَيْهِ رَقِيبٌ عَتِيدٌ
Not a word is said except that there is a watcher by him ready to record it.” [Surah Qaf:18] This includes all that you posted.

Hijab includes the way a person walks, talks, looks and thinks. All of it should be done modestly and applies to both men and women" #Hijab

My dear sisters in ISLAM. Cover up for the sake of ALLAH before its too late as today you are over the soil but tomorrow you may be under it

Yes hijab doesn't necessarily indicate your level of piety BUT it is fard (a must). So regardless of what you say, you HAVE to wear it.

Make tawba (sincere repentance) not just for sins you've committed, but also for obligations you haven't fulfilled.” [Ibn Taymiyyah]

I pray that the comfort of our graves exceeds the comfort of our beds. 

We ask ALMIGHTY-ALLAH سبحانه وتعالى to take our souls away when He's most pleased with us and make us of those who are always conscious.

AMEEN-YAA-RABBAL-ALLAHMEEN!


*subhanaka Allahuma wabihamdika wa-ashadu anla illaha anta astagfirka waatubu ilaik.


Post a Comment (0)