TUN KAFIN AURE 08


 TUN KAFIN AURE💐 8


Juni dear....yes Tilly ya amsa mata yana daga kwance. Jin tayi shiru ya taso ya dafa bayanta Tilly ya akayi ne? Ko akwai abinda kike so ne? No tambayarka kawai zanyi. Nawa ne kudin hotel dinnan ne per night? N150,000. Wage baki tayi ko wane kwana daya? Eh menene wai duk kin wani rude. Gani nayi kudin da yawa kuma gashi yau kwanan mu hudu banda abinci da kudin da kake kashewa a club. Wani shekeke ya kalleta kin ma raina ni to ko don ban biya ki naki kudin bane...yana gama magana ya mike daga shi sai gajeren wando ya jefo mata cheque. Ganin kudin dake jiki dubu dari biyar ba shiri ta rungume shi tana ta murna. Hmm kudi a kasar nan yana hannun masu shi suna kashewa kadangarun bariki da kayan maye wani lomar tuwo ta gagare. Masu kudi a rinka cin halal dai.
*******************

Hajara tana kwance tana chatting da kawayenta a group taji shigowar messages. Tana dubawa hotuna ne kamar bazata bude ba don bata da data sosai sai ta bude daya. Zumbur ta mike ta bude sauran. Babu shakka ita ce a duka hotunan biyar. Wadda ta turo cewa tayi ga wani style din pre-wedding pictures. Nan da masu cewa sunyi kyau da masu zaginsu. Wani gumi ne taji yana karyo mata lallai baa shaidar mutum, yarinyar da kullum take shigar mutumci ita ce a haka. Tsam ta tashi ta dauki mayafi ta sauka kasan gidanta wurin makociyarta. A'a Hajara shigo mana ina kitchen...a sanyaye ta karasa dama wani abu zan nuna miki a waya. Maimakon kiyi min forwarding, menene mu gani. Ruwan ruden tuwon da take ne ya fallatso mata a hannu da gefen fuska saboda tsabar rudewa. Na shiga uku ni Hadiza me zan gani haka. Hajara tace a group na gani shiyasa na nuna miki don nasan wace Hafsi. Muciyar ta karba ganin yadda hannun Hadiza ke rawa ta karasa mata tuwon. Daren ranar bata yi baccin kirki ba. Mijinta zai tafi office ya ajiyeta a gida duk da bata fada masa abinda ke faruwa ba yasan babu lafiya.

A falo ta hadu da Baffa zai fita ta gaishe shi. Lafiya dai Hadiza irin wannan sammako ko duk saurin ki taya ni cin kosai ne. Murmushin karfin hali tayi. Baffa akwai wasa sai dai baya sake wa yara suyi yadda suke so. Ganin bata biye mishi ba ya mike muje ciki. Mama na shafa mai suka shigo dakin. Hadiza lafiya kuwa...nan taji tsoron nuna musu hoton sai dai tasan yadda irin hotunan nan ye kawo a social media. Wasu mutanen basu da aiki sai ture turen abinda bai shafesu ba karshe su kunna wuta mai wuyar kashewa. Wayar ta mika wa Mama shima Baffa ya zauna kusa da ita yana gani. Hankalinta bai tashi ba sai da taga 'yarta babu ko dankwali ta shige jikin namiji sai kace kanin uwarta ko na ubanta. Nan take numfashin Mama ya fara sama sama dama ita haka take idan ranta ya baci. Haka ta fita daga ita sai daurin kirji ta shiga dakin 'yan matan. Wayar chaja ta fizgo daga jikin bango ta fara tsula mata. Hafsi ji tayi kamar a mafarki ana dukanta tayi saurin tashi. Yaya Hadiza ta gani sai kannenta. Cikin rashin fahimtar laifinta ta fara rokon gafara. Sai a lokacin Baffa ya shigo ya dakatar da dukan. Kyaleta haka ku zauna. Wayar Hadiza ya bata hoto daya ta kalla ta kama kafar Mama tana kuka...don Allah ku yafe min wallahi bazan kara ba. Ki ma kara mana don ubanki...wai ni dame muka kuskure miki ne Hafsa. Lokaci guda kin fara taka rawar gangar shaidan. Wai ma yaushe akayi wannan hoton? Shiru tayi ba amsa. Nace yaushe akayi hoton nan...lokacin...lokacin. Hadiza ce ta katse ta lokacin me? Uhm lokacin da muka ce miki zamu daukar hoto da ummati. Nasan za'a rina cewar Baffa. Dama nasan da taimakon wani a lalacewar da kika soma yi. Amma wallahi ba a gida na ba. Gidansu Saifullahin zani in nunawa mahaifinsa, ki kwana cikin shiri aurar dake zanyi cikin kankanin lokaci mutuniyar banza. Nan dai ya hada duka yaran nasa sun sha fada da nasiha. A dakinsa kowa yace da Mama ta tabbatar ta tuntubi Hafsi ko babu wani abu da ya shiga tsakaninsu domin shi yanzu ya tsorata da halin yaran zamani.



Batul Mamman💖

Post a Comment (0)