TUN KAFIN AURE💐 9
Wani irin kuka ne mai tsuma zuciya take yi tunda Mama tayi mata wannan tambayar. Wai ko wani abu ya shiga tsakaninsu??? Lallai ta jawo wa kanta tunda an fara zargin ko lalacewar tata ta kai nan. Gabadaya filon ta gama jika shi da hawaye dadin bakin cikinta ma rashin duriyar Saif. A wannan yanayin Ummati ta shigo itama kukan take yi don a falo Mama da Maman Ummati suka hada su ana ta fada gadon itama ta hau suka jeru kamar masu gasar kuka. Iyayensu sunyi fushi sosai. Tayi nisa da tunani kamar daga sama taji wayarta na ringing. A firgice ta tashi don tasan ko waye me kiran. Ringtone dinsa daban ne....ummati ce ta doke mata hannu da sauri tana kokarin dauka. Ta galla mata harara to banza mara zuciya..duk abinda ya samemu a dalilinsa sai yau zai wani nemeki. Cikin muryar data dashe saboda kuka tace bafa ki san me ya same shi ba. Don Allah ki bani wayar Ummati. Ni wallahi haushi kike bani mtww karbi ni ta dangwara mata wayar ta koma gefe. Ba zancen fita don iyayensu mata suna falo ana ta maida zance.
(Matar ina kika shige ina ta waya.)
Kaji rainin hankali yau fa kwanansu shadaya bata samunsa a waya(kai zan yiwa wannan tambayar. Sai da kaga matsala ka guje ni Saif) kuka ne yaci karfinta.
Shima a hankali yake magana( kiyi hakuri ni kunyar sake haduwa dake da kuma Baffa nayi. Matar ina tsoron zama sirikinsu har abada Baffa bazai dena ganina da wannan tabon ba)
Wani irin faduwar gaba taji (me kake nufi? Baffa fa sun taho gidanku tare da baban ummati)
(Nasani na kuma nayi musu bayani. Tun ranar da ya ganmu na sanar da umma don bana son rufafa a maganar aure. Kunya tasa na guje ki don naci amanar Baffa. Kiyi hakuri muyi rabuwar arziki amma bazan iya aurenki ba.)
Yana kashe wayar wani kuka ya kwace mata har su Mama suka shigo. Ummati suka fara tambaya tace bata san me ya faru ba. Kasa fada musu tayi tana ta kuka. Gajiya suka yi da tambayar aka kyaleta. Sai da Baffa ya dawo ya sanar da Mama yadda sukayi mahaifin Saif yace aure ba fashi tare da basu hakuri shi kuma dan yace bazai iya sake kallonsa ba. Zai fadi haka mana tunda yaso gurbata mana rayuwar yarinya. Suna ta maganganu Hafsi na jinsu daga daki tana kara tsanar kanta da abinda tayi.
******************
Junaid mutum ne mai son jindadi, bashi da magana sosai sai ta zama dole. Ko kadan baya daukar raini wannan kuma hali ne ya tarar da dukiyar da ya taso cikinta. matashi ne dan shekara 30 ga tsaho ga kyau ga fatarsa mai kyau saboda tana shan hutu. Gashin kansa da saje kuwa a kwance yake don kudin da ake ajiyewa don gyara shi daban ne. Yana son kula da gashin kansa ko kadan baya son abinda zai bata shi.
Yana kwance kan kujera kansa a cinyar Tilly tana fara shafa masa kai. Doke mata hannu yayi yana magana kasa kasa ki dena taba min kai I hate it. Dan tabe baki tayi to yi hakuri naga ko wanka baka yi ba meye abin bacin rai don na taba? Tashi yayi ya bude fridge ya dauko lemon gwangwani ya fara sha. Ki shirya muje party amma bana son wannan faratan naki kamar mayya ya juya mata baya ji yadda kika kusa kwashe min baya. Yi hakuri Juni ta fada tana murmushi bari na cire su nayi wanka.
Lallai ma yarinyar nan wallahi kinyi kadan abinda ya fada kenan lokacin da ya fito daga wanka ya kama Tilly tana satar masa kudi. A fusace ya karaso gabanta tasha mari hagu da dama. An fada miki bani da hankali ne? Kumatu ta rike tana kuka ni ka mar Juni? Ke 'yar waye da bazan mareki ba? Barauniya kawai get out of my room. Kafa yasa yana kai mata duka tana ta ihu. Da kyar ta rarrafa ta fita ya jefo mata jakarta waje ta ce zaka san ni kayiwa haka Juni sai na bata maka rayuwa. Ta mike da kyar tana dingisawa mugu ko kudina bai bani ba duk kwanakin nan dana yi.
*******************
Dai dai yake kallon mutane kowa da budurwarsa ana ta sha'ani. Shegiya Tilly da nasan haka take ai da tun wuri na nemi me rako ni nan. Kai da wa kake magana Juni? Shafa kansa yayi zancen zuci ne ya fito fili birthday boy...Imi dan wani gwamna ne abokin Junaid ne tun suna secondary duk watsewarsu tare sukeyi. Ina babe din da na ganku tare ne jiya? Tilly barauniya? Ai na bata takardar sallama dazu....sata fa tayi min don rainin hankali. Imi da buduwarsa suka fashe da dariya ai abokina ka fiye kwashe kwashe ne. Ya rungumo yarinyarsa ya Simy akwai wata a kasa ne kada yayi kwanan kadaici yau. Kai kyale ni kawai. Maybe na tafi portharcout gobe. Dont worry I will pay bana son ganinka so quite. Wayarta ta dauko ta mika masa ga hotunan wasu nan duk kawayena ne idan ka zaba kayi min magana. Bakin ruwan suka koma ana ta wasa da raye raye shi kuma yana kallon 'yan mata kala kala a wayar. Tsaki yayi zai kira Simy ta karbi wayarta sai kawai yaci karo da hoton da ya daga masa hankali. Zuciyarsa ce take bugu da sauri da sauri...he wants this girl at all cost abinda kawai yake fada a ransa kenan.
Batul Mamman💖