ANA BINA BASHIN AZUMI SABODA CUTAR OLSA

*ANA BINA AZUMI SABODA CUTAR ULCER* !!
:
Daga zauren
Khulafa'ur-rashiidun
:
Assalamualaikum warahmatullahi wabarkatuhu. Nine wancan ramadan din daya wuce ana bina azumi guda 15 sakamakon ulcer dayasani agaba kwanaki harna kwanta a gadon asibiti saboda ita amma Bayannan dakya nabiya 6 duk innayi azumi saiya Tashi niyita kokarin naga nabiya amma abun ya gagara damn har likitoti sunce ciwon kodane daga baya aka gane chronic ulcer NE yanxu haka inashan magani amma a haka MA yakan tashi ga Ramadan yaxo ,To mlm Yaya zanyi ??
:
                       ******
:
Wa,alaikumussalam
Ki cigaba da shan magani, kijira zuwan ramadan, idan ya tashi, seki ajjiye, randa kika samu sauki, seki rama iyaka adadin azumummukan da aka biki. Domin fadin ALLAH ta'ala
:
"Watan Ramadana ne wanda aka saukar da Alƙur'ãni a cikinsa yana shiriya ga mutãne da hujjõji bayyanannu daga shiriya da rarrabẽwa. To, wanda ya halarta daga gare ku a watan, sai ya azumce shi, kuma wanda ya kasance majinyaci ko kuwa a kan tafiya, sai ya biya adadi daga wasu kwanaki dabam. ALLAH Yana nufin sauƙi gare ku, kuma ba Ya nufin tsanani gare ku, kuma dõmin ku cika adadin, kuma dõmin ku girmama ALLAH akan Yã shiryar da ku, kuma dan kuzama masu godemasa. (baqara ayata 183)
:
Seki rubutasu a takadda,saboda yanayi.
  (hadisi ya tabbata acikin bulugul maeam babi na qarshe cikin kitabus siyam) cewa "wanda ya mutu kansa da azumi, waliyinsa ya rama masa"
.
Idan kuma akasamu tabbaci daga likita, sakamakon bincike bazaki warkeba(saboda tsufa kowani dalili), seki riqa ciyarwa, dana yamxu dana baya wanda suka ku6uce miki
.
Saboda a sharia, ALLAH baya daurawa rai face se abinda zata iya, "idan kin gagara seki ciyar, musammam in tsufane ya kamaki". 
        Wallahu a,alam
:
➡ Muhammad Auwal Hussain Abu ja'afar
========================
*```Date* ```[28-08-1439]Hj {05-05-2018} 
  Kuna iya samun mu ta Internet/website http://khulafau.cf
_Masu buqatan Group suyima daya daga cikin Number's innan maga ta whatsApp_
+2349033206238
+2347035269582
+2348063796175
           *```Kuna iya samun mu ta facebook*```
facebook.com/khulafaurrashidun
((سُبْحَانَكَ اللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ، أشْهَدُ أنْ لَا إِلَهَ إِلاَّ أنْتَ، أسْتَغْفِرُكَ وأَتُوبُ إِلَيْكَ))
〰〰〰〰〰〰〰〰✔
*Wanda yaga gyara, yasanar damu !*


1 Comments

Post a Comment