👩🏼♠ *MUSLIM LADIES WW* ♣👩🏼
*TUESDAY TEAM*
BAYANI DAGA MASANAN TARBIYYA
1 Ta hanyar bayar da labarai da kissoshi, misali na san mahaifinmu ya taba ba mu labari kan hadarin wulakanta mutane domin ba ka sani ba ko wani waliyyi ne ka wulakanta sai Allah (s.w.t) ya yi maka azaba, wannan kuwa ba na mantawa a shekarar 1983 ne, sai ya zamanto idan mun ga wani yana tsokanar wani mutum saboda tawaya ta halittarsa mukan gaya masa ba ka sani ba ko waliyyi ne.
Yaro mutum ne mai son tarihi da labarai, kuma a lokacin da nake koyarwa a Furamare da kuma Sakandare na ga amfanin haka sosai, ta yadda soyayya da kaunar juna ta faru tsakanina da dalibai, har ma koda a kan hanya ne wani ya gan ni yakan taho a guje ya ce: Gobe tarihi fa za a yi mana.
Babu wata hanya da tafi a wurin tarbiyyantarwa kamar hanyar tattaunawa, a cikin wadannan hanyoyin kuwa duk babu wacce ta kai hanyar bayar da kissoshi, da hikayoyi, da tarihi.
Ta hanyar labaru kakan iya koya wa yara jarumtaka da girmama mutane, da son al’ummarsu, da neman kawo gyara cikinta, da jin lallai dole su dauki nauyin isar da sakon Allah ga mutanensu, da son kyauta da taimaka wa marasa shi, da nisantar rowa, da sadaukarwa don mutanensu, da son iyaye da rashin saba musu, da kaskantar da kai ga mutane, da sanin Allah.
2 Abokantaka da yaronka ta yadda zaka iya yi masa tasiri ta hanyar hira da shi da nuna masa shi ma mutum ne mai iya tunani, har ma ka dauki shawara daga gare shi ta yadda zai ji cewa shi ma mutum ne kamili.
Rashin wannan ya sanya yara suna jin su tauyayyu ne, kamar dai yadda al’adu suka nuna mata ne a cikin al’ummu har wannan ya yi musu tasiri a tunaninsu, haka nan suka dauki yara a matsayin kaskantattu, aka yi musu irin wannan mu’amala har ya yi musu tasiri, shi ya sa sau da yawa sukan taso ba su san al’ummarsu ko duniyar da suke cikinta ba.
Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: “Yaro a shekara bakwai na farko shugaba ne kuma sarki, a shekara bakwai kuma bawa ne ribataccen yaki, a shekara bakwai kuma dan’uwa ne kuma waziri” [7] . Wannan Hadisi yana nuna mana shekara ishirin da daya da zaka yi tare da yaro, da irin mu’amalar da zaka yi da shi a kowacce daga shekaru bakwai.
3 Koyar da yaro kada ya cuci wani ta hanyar sanya tausayin al’umma a zuciyarsa kuma da koya masa kada ya karbi a zalunce shi, da tausaya wa wanda aka zalunta da nakasassun mutane kamar mai bara da talaka, wannan yana iya faruwa ta hanyar ba su labarai da tarihi na magabata domin ya yi tasiri a kansu.
4 Sanar da yaro tarihi da labaran yadda kasarsa take da kuma abin da kakanninsu suke a kai na alheri da kwadaita masa wannan, da sanar da shi kabilun kasarsa da hakkokinsu a kansa, da koya masa yadda zai kiyaye hakkin sauran abokan zamansa na kasarsa musulminsu da wadanda ba musulmi ba.
5 Nisantar kalmomin banza da gulmar wasu da duk abin da bai dace ba a gaban yaro, da dukkan wani abu mummuna, domin shi ma ya yi koyi da na gaba. Abubuwan da aka hana munana yin su a gaban yaro yana dada munana su, domin yana nufin bata asasin ginin al’umma wato Yara .
6 Yi wa ‘yayanka addu’a kullum da alherin Duniya da na Lahira, wannan ya zama abin da ba zaka taba mantawa da shi ba, koda kuwa ka manta da yi wa kanka addu’o'i to kuskure ne babba ka manta da yi wa yaranka.
7 Shawartar yaro kan wasu abubuwa kamar abin da ya shafi rayuwar gida da zai iya bayar da nasa ra'ayi, ko inda zaku je ziyara a gidajen 'yan'uwa, ko wurin wasannin yara.
Wata rana da watan Azumi wani daga dalibanmu na bangaren Hausa a Jami’ar Azad da take birnin Tehran ya gayyace mu gidansa shan ruwa sai na ji yana sharwartar ‘yarsa wane kallo ne ya kamata ya sanya mana? Ita kuwa sai ta mayar wa Uban da cewa: Zabi yana hannunmu duk wanda muke so. Kafin nan shi da dansa da suka zo daukarmu a mota sai yakan ce da shi dan da yake tuka mu cewa: Ai wannan abokina ne kuma dana.
8 Yana da muhimmanci a rika gode wa yaro duk sa’adda ya yi wani abu na kirki, da yabonsa kan haka don a kara masa himma a kan abubuwan da yake yi na alheri.
Godiya ga wanda ya kyautata wani abu ne da yake kara masa himma yake karfafa shi, kuma yana nuna masa irin kaunar da mai godiya yake yi masa, sannan yana faranta masa rai. Sai dai godiya iri-iri ce, wani lokaci da baki za a gode, wani lokaci kuma godiyar aiki ce. Dukkaninsu ana bukatarsu; sai a yi masa godiya da harshe idan ya kyautata, sannan kuma wani lokaci a biya masa wasu bukatu nasa da suke damunsa, ta yadda zai fahimci cewa; kirkinsa ne ya sanya ake yi masa wannan alherin.
9Nuna wa yaro kuskure kan abin da ya yi na kuskure, da nuna masa cewa; zai iya kai wa ga wani abu da zai cuce shi a Duniya ko a Lahira ko a duka gida biyu. Kurakuran da yara suke yi kamar na manya ne ta fuskacin cutuwa, sau da yawa wani kan yi kuskuren da har ya mutu yana nadamarsa, wani kuwa yakan yi kuskuren da hatta da a lahira sai ya kasance masa azaba. Don haka nuna wa manyan gobe irin wannan darussa yana da muhimmanci matuka.
10Hanyar kwadaitawa ta fi yawa a kan hanyar tsoratawa, wato a fi gaya masa Allah zai ba shi kaza a Lahira in yana biyayya ga iyaye ko wani aiki na alheri maimakon a rika cewa: Ai in ka mutu, mu binne ka a kasa, kuma kunama, da maciji, da mala’ika mai sandar wuta, su kama ka, su cije ka.
Irin wannan ya zama kadan ne; domin yana iya sanya masa tsoron komai, da sukewa daga rayuwa, da kashe karfin zuciya, da sanya shi gajiya wurin aikata kyakkyawa, ko ya sa masa kosawa daga jin nasihar, idan tsoro ya yi yawa yana iya hana shi sukuni a rayuwa.
*SHDG*
_(SMASHER,HUBBEEY,DIDEEYLOV & GENTLE)_