DALILAN DA KE JAWO TOSHEWAR BASIRA




DALILAN DAKE JANYO TOSHEWAR BASIRA
*********************************************
Assalamu Alaikum 'Yan uwana Musulmai.. Mutane suna yawan
rubutowa tambaya akan cewa wai sun kasa fahimtar Karatu,
ko suna fama da toshewar basira ko yawan kasala wajen
ibadah.
Akwai dalilai masu yawa wadanda ke janyo kasala ajikin Dan
Adam tare da toshewar basira. Ga misali akwai :
CIKA CIKI DA ABINCI
Manzon Allah (saww) yace :
"BABU WATA JAKA WACCE DAN-ADAM YA CIKATA, MAFI
SHARRI (AGARESHI) KAMAR CIKINSA. 'YAN LAUMOMI
KA'DAN SUN ISHI 'DAN ADAM. GWARGWADON YADDA ZAI
TSAYAR DA QASHIN BAYANSA (BA ZAI KASA MIKEWA
SABODA YUNWA BA).
IDAN YA ZAMTO BABU MAKAWA (SAI YACI), TO (ya raba cikin
nasa gida uku).
KASHI GUDA DOMIN ABINCINSA, KASHI GUDA DOMIN ABIN
SHANSA, KASHI GUDA KUMA DOMIN NUMFASHINSA".
(Imamu Ahmad ya ruwaito shi tare da TIRMIDHY da Ibnu
Majah, da Ibnu Hibban da Hakim).
To tunda hakane, kai da kullum kasa abinci agabanka, ci kawai
kake tayi sai kaji BABU MASAKAR TSINKE sannan ka hakura
kace ka Qoshi, yaya kenan??
Sarkin Muminai, Umar bn Alkhattab (rta) yana cewa:
"KU TSORACI CIKA CIKINKU DA ABINCI. DOMIN YIN HAKAN
YANA SANYA MUTUM NAUYIN JIKI ARAYUWARSA, KUMA YA
SANYA GAWAR MUTUM TA RIKA 'DOYI BAYAN MUTUWARSA''
Ashe kenan mutukar baka so Gawarka ta fara doyi da zarar ka
mutu, to sai ka Qaranta abincinta ka dena HAYAM HAYAM!!!
LUQMÃNUL HAKÉÉM ya cewa 'Dansa:
"Ya kai 'dana!! Idan ciki ya cika da abinci, sai basirar Mutum ta
mutu, hikimarsa ta Dakushe, kuma gabobinsa su kasa yin
Ibada''
Ance da ya gama yiwa 'Dan nasa wadannan nasihohin (har na
cikin Suratu Luqman) yaron mutuwa yayi! Saboda tsoron Allah..
YAWAN DAUKAR ZUNUBI
**************************
Yawan aikata manyan laifuka shima babban dalili ne dake
janyo kasala da mutuwar zuciya wajen ibadah da toshewar
basira. Don haka idan mutum yana basirarsa tayi kaifi kuma ya
samu kusanci da mahaliccinsa, to wajibi ne ya nisanci
kaba'irori.
Rikon hadda da kaifin basira falala ce daga Ubangiji. Kuma
hakika falalarsa bata kyautuwa ga masu sa'bonsa.
SURUTU DA JIN WAQA
************************
Yawaita surutu marar amfani shima babban dalili ne na
toshewar basira. Sai kuma yawan sauraron kade-kade da
wake-wake shim yna toshe basirar Mumini.
Kuma kamar yadda cin halal yake janyo hasken zuciyar da
Qaruwar basira, to haka kuma cin haram yana sanya toshewar
basira da dattin ruhi da dusashewa imani.
Ya Allah kasa munji mu kiyaye. Ka azurtamu da tsantsar
tsoronka da yin biyayya agareka don Tsarkin Sunayenka da
daukakar Siffofinka.

1 Comments

Post a Comment