Gudun Tsira 5 Complete





GUDUN TSIRA 5
LITTAFE NA BIYA
COMPLETE BOOK
TYPING SULEIMAN ZIDANE KD...
NA
Abdulaziz sani madakin gini
.
...............
HAKA DAI SU SIYAMA suka ci gaba da tafiya a cikin shigar dakarun birnin darul Hunam,har suka iso birnin.Da isowarsu bakin kofa sai daya daga cikin masu gadin kofar ya dauki fitila ya bude wata yar karamar taga a jikin kofar wacce ta kasance ta karfe ya haska.Koda yayi arba da fuskar sadauki Samhur wanda shine ya jagoran dakarun da suka fita dazu sai yayi murmushi ya bude kofar.Nan take su Siyama suka kunna kai izuwa cikin birnin.Kwatsam sai sukaga wasu dakaru masu yawa sun taso musu sunyi musu kawanya suna masu ritsa su da makami.Daya daga cikin dakarun ya dubi sadauki Samhur yace,yaya dazu ka fita tare da dakaru kimanin dubu uku,amma yanzu ka dawo da yan tsiraru,kayi bayani mu ji idan bamu gamsu ba yanzun nan zamu kaddamar daku.Koda jin wannan batu sai sadauki Samhur ya dakawa mai maganar tsawa yace kai Zambaru shin ka sami tabin kwakwalwa ne?Ya za ayi na dawo tare da dakaruna gaba daya alhakin harin sumame muka kai don gamawa da yan kabilar Banu Hanzar?Ai mun isa har can sansaninsu mun tarwatsa su sun gudu,kuma sun bazama izuwa cikin daji.A dalilin hakane na bar dakaruna a can suka lallabe domin idan suka dawo su gama dasu.Yanzu na dawo ne da tsirarun yarana domin na sanar da gwamna halin da ake ciki,saboda asan matakin da ya kamata a dauka a gaba.Lokacin da Zambaru yaji wannan batu sai jikinsa yayi sanyi bisa dole ya gusa daga kan hanya,suma yaran nasa suka kauce suka baiwa su Siyama hanya suka wuce gaba.Har su Siyama suka bace musu da gani suna nan a tsaitsaye suna wasuwasin bayanin da Samhur yayi musu.Haka dai suka ci gaba da tafiya a cikin birnin na Darul Hunam suna wuce unguwoyi da gidaje har suka iso gidan gwamna.A bakin kofar shiga gidan gwamnan ne aka sami matsala aka ki bude musu kofa.Aka ce sai an tantance su daya bayan daya.Koda Siyama taga cewa lallai asirinsu zai tonu sai tayiwa yaranta alama aka ruguntsume da yaki cikin kankanin lokaci suka kashe gaba dayan dakarun dake bakin kofar suka falfala cikin gidan da gudu.Siyama na tusa keyar Samhur yana nuna mata hanya har saida da yakaita har cikin turakar gwamna.Duk inda suka iske dakarun tsaro saidai kaga yaran Siyama sunyi musu kisan sunkuru sub zubar dasu kasa.Lokacin da suka iso bakin kofar falon gwamna sai Siyama tasa kafarta ta dama ta doki kofar.Saboda karfin dukan nata sai da kofar ta jijjigo daga cikin gini ta fadi kasa rikica Kawai sai Siyama ta hango gwamna zaune a kasa dirshen ya harde kafafu yana jan dogowar casbaha kuma yana fuskantar bakin kofar,sannan kuma yayi shiga gagaruma shigar yaki.Al'amarin dayai mutukar razana Siyama kenan,kuma yai matukar bata mamaki,kawai sai ta saki Sadauki Samhur ta dubeshi tace,maza ka fice daga cikin gidan nan ka tafi wurin iyalanka idan baka son su rasa ka.Batare da gardamar komai ba kuwa Samhur ya juya da baya da gudu ya bace daga wajenTun daga nesa Siyama ta karewa gwamna kallo tayi nazarinsa sosai sai taga ashe basamuden kato ne mai kira irin ta sarkinsu na kisra wanda ta kashe,amma shi nasa jikin ma har yafi na sarkin kauri,murdewa gami da tarin jijiyoyi.Nan take Siyama taji zuciyarta ya buga da karfi ta ayyana a ranta cewa lallai yau fa ta gamu da gamonta.Kuma ta taro fadan da bata da tabbacin samun nasararsa.Amma data tuno da kalamin mahaifinta Shugaba Sharwan cewar idan bata sami nasara ba a wannan yaki data kirkiro har abada bazai taba yafe mata ba,sai taji dukkan tsoro ya gushe daga zuciyarya,kawai sai ta zura hannu cikin wuyan rigarta ta tabo wannan sarka wacce marigayi Sultan ya bata tun tana yarinya Karama.Nan take sabon karfin gwiwa ya shigeta kawai sai ta bude hannunta mai rike da takobi ta durfafi inda gwamna yake zaune cikin sauri ba tare da shakkar komai ba.Yayi daya rage saura baifi taku biyar ba ta isa gareshi sai kawai taga ya daga hannunsa yana mai dakatar daita,kuma yayi shiru yana ci gaba da kan wannan casbaha ta tsafi dake hannunsa har saida yakai karshenta,sannan ya ajiye casbahar ya mike tsaue suka fuskanci juna,akayi kallon kallo na tsawon yan dakiku.Gwamna yayi wani irin murmushin mugunta sannan yace.Haba yarinya saurin ne kike haka na gaggawar karbar mutuwarki.Kiyi sani cewa Sunana Gumaizu Ibini Kamzaru,kuma ni jinin sarautar kisra ne,sarki da kika kashe 'da ne ga baffan mahaifina.Nasan duk abinda kika aikata a birnin kisra kawo izuwanki nan,don haka dama ina cikin shirin jiran isowarki domin na dauki fansar ran dan'uwana a kanki.Ina mai tabbatar miki da cewa wannan buri dake cikin ranku keda mahaifinki da kabilarku ta Banu Hanzar mafarki ne wanda ba zai taba tabbata gaskiya ba,domin har duniya ta nade zuri'armu ce zata ci gaba da mulkin birnin kisra badai wata zuria ba kuma har abada babu wani talaa dazai sami yancin kansa tunda babu mai iya hana mu yin mulkin zalunci,danniya da murdiya.Ina fatan dai kinyi bankwana da iyayenki kafin ki iso nan fadata don ki gutsuren sassan jikinki guda daya jal bazasu sake gani ba.Koda gwamna yazo daidai nan a jawabinsa sai jaruma Siyama ta tari numfashinsa tana mai daka masa tsawa tace,kai tsohon annamimi bakin azzalumi kayi sani cewa zuciyata ta kekashe ga barin tsoron duk wani azzalumi domin komai rintsi da tsanani sai na sami nasara a kanka.Koda jib haka sai gwamna ya fusata ainun ya zare wata sharbebiyar takobi daga kuibin cinyarsa ta hagu ya rugo da gudu izuwa kan Siyama yana mai kwarar uban ihu mai tsananin firgitarwa.Ai kuwa ita ma sai ta ruga izuwa kansa tana mai kurma ihu amma sai karfin ihun nasa ya danne nata,kamar yadda ruwan teku ke kwararowa cikin gari ya shafe komai.Suna haduwa suka ruguntsume da azababben yaki,ana fara yakin Siyama ta raina kanta domin kuwa karfin saransa ya ninka nata sau uku.Duk sa'adda ya kawo mata sara ta kare sai taji kamar katon dutse mai nauyin tsiya aka buga akan takobinta da kyar take iya tareshi,wani lokacin ma har durkushewa take kamar zata fadi kasa,amma saboda juriya da naci sai kaga ta mike cikin hanzari taci gaba da artabu.Lokacin da dakarun Siyama suka ga anayin wannan azababben yaki tsakanin Gwamna da Siyama sai suka firgita ainun bisa ganin irin jamrumtakar gwamna da tsagwaron karfin damtsemsa gami da kwarjininsa.Da farki sai suka fara wurga mugayen makamansu da nufin su hallakshi,amma duk makamin da aka jefa masa sai ya dawo da baya ya soke maishi ya fadi matacce.Kafin kace wani abu kimanin dakaru arba'in na Siyama sun zama gawa.Abinda yayi matukar razana dakarun kenan suka ja da baya.Suna buya suna kallon gumurzun a firgice.Lokacin da aka shafe kusan sa'a guda ana wannan artabu ya zamana cewa dayansu bai sami nasarar koda lakutar jikin daya ba.kuma karfin sihirinsu na tsafi yayi kunnen doki sai ran gwamna ya baci,zuciyarsa ta harzuko ya sauya salon fada ya hada da naushi gami da bugu da kafa da hannu.Naushin farko da yayiwa Siyama saida tayi katantanwa sau uki a tsaye,sannan ta sulale kasa magashiyan.Gwamna ya sunkuyo ya kamo gashin kanta a wulkance da nufin ya kara gabza mata naushi a fuska.Ba zato ba tsammani sai yaji tasa kafarta ta naushi tasa fuskar da dukkan katfinta.Saboda karfin dukan saida yayi tsalle sama da baya tamkar an janyeshi da majaujawa,bayansa ya gwaru da bango ya fado kasa,jini na yoyo a hancinsa da bakinsa mma sai ya mike tsaye zumbur ya rugo da gudu izuwa kan Siyama ya sureta da hannayensa biyu yayi wurgi da ita sama,fuskarta da cikinta suka gwaru da rufin dakin taga wadansu irin taurarin wuya a idanunta kuma taji cikinta ya kulle kamar zata amayar da hanjin cikinta.Tana fadowa kasa sai Gwamna ya cafke ta ya juyata da nufin ya buga gadon bayanta akan gwiwar kafarsa don ya karairaya kasusuwan gadon bayan nata.Cikin wata irin gwaninta da tsananin zafin nama Siyama ta wulkila jikinta ta zulle daga cikin hannayensa kuma ta kamo kansa ka kafafunta biyu ta wurga shi sama.Ai kuwa sai gadon bayansa ya maku a jikin wani karge dake rataye a jikin bangin dakin.Take gwamna ya kurma uban ihu sakamakon tsananin zafi da zogin da yaji,a zatonsa ma daya daga cikin kasusuwan bayan nasa ya karye domin daya fado kasa tim kasa mikewa yayi ya rike kugunsa yana yoyon jini daga cikin hancinsa.Damar da Siyama ta samu kenan ta mike tsaye tana layi har a sannan itama bata daina zubar da jini ba daga cikin hancinta da bakinta.Kawai sai ta gyara tsayuwarta ta dunkule hannayenta biyu ta tsaya tana jiransa.Gwamna ya shafa gadon bayansa yaji babu inda ya karye,sai ya mike tsaye zumbur.Kawai sai ya kama rigar jikinsa wacce ta kasance mai kaurin gaske ce ta kirgi amma saiya tsargeta ta rabe gida biyu,yayi jifa da ita sannan ya ruga da gudu izuwa kan Siyama yana mai sake kwarara uban ihu a karo na biyu.Koda ganin haka sai ita ma ta rugo gareshi zuciyarta ta tasa cike da mugun nufi.Duk wanda yaga yadda wadannan jaruman suka rugo da gudu izuwa kan juna yasan cewa idan suka hadu dole ne abu daya ya faru cikin biyu,kodai suyi ragas ko kuma dayansu ua sami nasarar kashe daya.Ashe shi gwamna niyyarsa itace yakaiwa Siyama wawura ya matseta da hannauensa yadda zai karya kasusuwan bayanta.Ai kuwa cikin zafin nama ta shige ta karkashin kafafunsa bisa taimakon santsin dutsen Jauhar din da aka malale falon,kafin ya juyo ya fuskanceta sai ta kama kansa da hannayenta biyu ta murde masa wuya.Kawai sai gani akayi gwamna ya sulale kasa matacce,saboda tsananin mamaki da murna sauran dakarun Siyama basu san sa'adda suka kama tsalle da shewa ba,sunayi mata jinjina.Ita kanta Siyama tasan cewa tsananin sa'a ce tasa tayi nasara,duk da cewa kuwa tayi amfani da tsagwaron jarumtakarya da kwarewarta a horon iya fada.A daidai wannan lokaci ne dubunnan dakarun birnin suka shigo cikin gidan gwamna 'du...su da yawa rike da makaman yaki,amma duk wanda yazo yaga gawar gwamna sai jikinsa yayi sanyi ya yarda makaminsa.Dama gaba dayan mutanen birnin darul Hunam sun gaji da irin zaluncin shugaban nasu hatta kuwa dakarunsa ya matsa musu da zalunci don haka babu wanda yayi bakin ciki da mutuwarsa.Nan take jama'ar gari suka rude da shewar farinciki.Gaba daya dattawan garin da masu fada a ji kuwa sai suka taru a kofar gidan na gwamna.Siyama da dakarunta guda dari da sittin suka tsaya a gabansu.Nan take Siyama ta hau kan wani mumbari ta tsaya a tsakiyar miliyoyin jama'a tamkar an ajiye dan tsako a tsakiyar dubunnan kaji tace,yaku jama'ar birnin Darul Hunam kuyi sani cewa bamu shigo cikin birnin kuba da nufin mu cutar da dayanku ba sai domin mu sami damar da zamu ci gaba da yin GUDUN TSIRAn da mukayi saboda mu kubuta daga Sharrin sarkinku Darwaz bisa kasancewar bamu da wata hanya sai nan.Yanzu zan aika aje a taho da jama'armu su shigo cikin wannan gari domin mu kwana anan kuma mu sami karin guzuri inyaso gobe da safe mu ci gaba da tafiyar mu.Burinmu kawai shine mu fice daga cikin wannan nahiya gaba daya saboda ta haka ne kadai zamu iya tsira da rayuwar kabilarmu amma ina mai yi muku alkawarin cewar komai dadewa zamu dawo wannan kasa taku domin kwato muku yancinki a wajen azzaluman sarakunanku.Koda jin wannan batu sai gaba dayan jama'ar garin suka dada rudewa da shewa gami dayiwa Siyama tafi da jinjina.Nanfa aka shiga yiwa Siyama da jama'arta hidima ana basu masauki da abinci ana karramasu.Ba tare da bata wani lokaci ba Siyama ta aika da manzanninta mutum uku izuwa can daji inda suka baro Ayarin Kabilarsu.Koda suka isa suka sanar dasu Shugaba Sharwan cewar Siyama ta sami nasarar shiga har cikin birnin Darul Hunam harma ta kashe gwamnan su sai kowa ya kamu da tsananin farin ciki,saboda hakan ne ma shugaba Sharwan,Ilela da 'yar uwarta suka fashe da kukan murna.Kamar yadda Siyama ta shirya haka al'amarin ya kasance wato bayan jama'arsi sun iso cikin birnin darul Hunam sun kwana sai suka tashi da sassafe sukayi shiri aka basu guzuri mai yawan gaske,suka bar birnin jama'ar gari nata kukan rabuwa dasu domin sun san cewa da zarar sarki Darwaz da tawagarsa sun iso birnin mulkin zalunci ya dawo kenan.Haka dai mutanen birin darul Hunam suka yiwa su shugaba Sharwan rakiya har izuwa karshen gari sannan sukayi musu bankwana suka koma da baya izuwa cikin birnin darul Hunam suna kuka da bakin ciki.Bayan tafiyarsu Shugaba Sharwan da cikar kwanaki biyar daidai sai ga tawagar su Sarki Darwaz sun iso birnin darul Hunam.Boka Hurgas nayi musu jagora,koda suka iso birnin suka iske irin mummunar barnar dasu Siyama sukayi ta kashe gwamna tare da dakarunsa masu yawa,sai Sarki Darwaz ya dimauce ya zama kamar wani mahaukaci sabon kamuwa,domin zare takobi yayi yahau kowa yana maiyin kan uwa da wabi.Har saida 'yarsa Gimbiya Huraisa tasha gabansa ta rike hannunsa sannan ya dawo cikin hayyacinsa.Da yaje gaban kabarin gwamna kuwa saiya kwanta a gaban kabarin yana ta kuka da bakin ciki.Da kyar da sidin goshi Huraisa ta lallameshi ta janyeshi daga bakin kabarin takaishi gaban Boka Hurgas inda suka zauna suka shiga tattaunawa.A sannan ne sarki Darwaz ya dubi boka Hurgas yace,yakai abin dogaron birnin kisar yanzu yaza ayi mu riski wandannan abokan gaba namu kafin su sami damar fita daga cikin wannan nahiya tamu?Lokacin da Boka Hurgas yaji wannan tambaya sai yayi shiru yana mai sunkuo da kansa kas,kawai sai ya dauko wata farar sandar tsafi daga cikin aljihunsa ya saketa,maimakon sandar ta fadi kasa,sai ta kama yin zane a kasa da kanta,ta rubuta wadansu dalasiman kalmomi na tsafi wadanda babu mai iya karantasi face mashahurin boka kuma yaren da akayi amfani dashi aka rubuta kalmomin ya kasance bakon yare wanda babu wanda ya taba jinsa.Nan take Boka Hurgas ya karanta wadannan kalmomi a fili cikin wannan bakon yaren sannan yayi ajiyar zuciya ya dubi sarki Darwaz yace,ya shugabana bisa binciken da nayi yanzu idan muna son muke mu riski wadannan abokan gaba namu saidai mu dauko wadansu bakaken aljanu wadanda suka kasance hadiman sarkin aljanu na birnin HIMRAL.Idan kuwa kanason sarkin aljanun ya baka hayar wadannan aljanu nasa iya adadin yawan dakarunka da kuma mu uku don zuwa wannan gagarumin aiki,dole ne kayi masa alkawarin bashi jinin jama'arka mutum dubu uku bayan kowacce shekara uku har tsawon zamanka a kan karagar mulki.Idan ka saba wannan alkawari koda sau daya ne saika daura damarar yin yaki dashi Sarkin Aljanun.Lokacin da Sarki Darwaz da 'yarsa Gimbiya Huraisa sukaji wannan jawabi na boka Hurgas sai hankalonsu ya dugunzuma ainun suka rasa abinda ke musu dadi a duniya.Kawai Sai Gimbiya Huraisa ta kama hannun Sarki Darwaz tajashi izuwa can gaba nesa da inda Boka Hurgas ke zaune,domin suyi shawara ta dubeshi tace,yakai Abbana inaso kayi sani cewa da asara gwara gidadanci.Ni a ganina da dai mu rasa mulkinmu da rayuwarmu gwara mu rasa dubunnan rayukan talakawanmu,domin kuwa shi rai ba a bakin komai yake ba muddin akwai biyan bukata.Ya zama wajibi a garemu yanzu mu dauki wannan alkawari ga sarkin aljanu na birnin Hinral domin muga bayan makiyanmu,in yaso bayan mun cika burinmu sai mu nemi sihirin da zamu gama da sarkin aljanun,domin mu ci gaba da mulkinmu a cikin nustuwa da kwanciyar hankali.Ka sani cewa niyanzu bani da wani buri wanda yafi nayi gaba da gaba da jaruma Siyama domin na kasheta da hannuna saboda ni a ganina ma abin kunya ne a ce kai da kanka kayi yaki da ita,tunda duniya ma tasan cewa ruwa ba sa'an kwando ba ne,kuma ya ma za'a yi ace sarko mai babbar daraja kamarka ya yaki makaskanciya jaruma wacce ta fito daga cikin wulakantacciyar kabila ta talakwa.Lokacin da Gimbiya Huraisa yazo na a zancenta sai Sarki Darwaz ya bushe da dariyar farin ciki sannan ya rumgume ta a kirjinsa yace yake 'yata hakika ina alfahari dake,saboda kaifin hankalinki gami da basirarki da kuma hangen nesanki, lallai na karbi wannan shawara taki hannu biyiu.Koda gama fadin hakan sai Sarki Darwaz ya yafito Boka Hurgasa da hannu ya taho garesu,da isowarsa sai ya zube kasa a gaban sarki Darwaz cikin biyayya yace ya shugabana me kuka shawarta kai da Gimbiya bisa wannan al'amari?Sarki Darwaz ya numfasa yace,mun yanke hukuncin cewa zamu nemi taimakon sarkin aljanu na birnin Himral kuma na dauki wannan alkawari na bashi jinin jama'a ta mutum dubu uku a duk bayan shekara uku har izuwa karshen mulki na.Koda Boka Hurgas yaji wannan batu sai ya firgita ainun kuma ya kamu da tsananin mamaki bisa yadda sarki Darwaz ya aminta da daukar wannan alkawari mai tsananin wuya da hadarin gaske.Har Boka Hurgas ya bude baki zaice wani abu sai Sarki Darwaz ya daka masa tsawa yace,ka sani cewa bana magana biyu don haka na umarce ka daka hanzarta sanar da sarkin aljanu na birnin Himral amsar bukatarsa don cika tamu.Jikin boka Hurgas na karkarwa ya shafi kasa da hannunsa na hagu sannan ya ajiye wannan farar sandar tasa ta tsafi a kasa ya karanta wadansu dalasimai na tsafi ya tofa akan sandar.Faruwar hakan keda wuya saiga hoton fuskar sarki aljanu ta bayyana akan sandar tsafin.Saboda tsananin munin fuskar da kwarjininta saida Sarki Darwaz da Gimbiya Huraisa suka mike tsaye zumbur a firgice sukaji kamar su ruga da gudu amma saboda dakewar zuciya irin ta manyan sadaukai sai suka tsaya kyam suka kurawa fuskar sarkin aljanun idanu,amma duk da haka jikinsu na tsuma.Ba tare da bata wani lokaci ba Boka Hurgas ya zayyanewa sarki aljanu duk abinda sarki Darwaz ya shaida masa.Koda jin haka sai Sarki Aljanun ya bushe da wata mahaukaciyar dariya mai tsananin ban tsoro mai kama da saukar kwarankwatsa wacce ta kara firgita sarki darwaz da gimbiya huraisa sosai,shi kansa boka hurgas saida ya fadi kasa jikinsa na karkarwa bai ma san sa'adda ya saki fitsari ba a wando saboda tsananin firgita da razana.Lokacin guda sarkin aljanun ya tsuke bakinsa yayi shiru ga barin yin mahaukaciyar dariyar sannan ya dubi sarki Darwaz yace,shi kenan gobe iyanzu dakarunmu na aljanu wadanda zasu kaiku inda abokan gabarku suke zasu iso,amma ku sani cewa karya mana alkawari daidai yake da gayyato GUGUWAR ANNOBA wacce ba"a san farkonta ba da karshenta,kuma daidai yake da gayyato GOBARA DAGA KOGI wacce batada magani.Gama fadin hakan keda wuya sai fuskar sarki aljanu ta bace bat daga kan wannan sandar tsafi,kawai sai sarki Darwaz ya kama hannun 'yarsa gimbiya huraisa yajata suka tafi izuwa cikin gidan gwamna suka bar boka Hurgas a kasa dirshen yama mai binsu da kallo kawai cikin razani da tsananin mamaki. Al'amarin su Shugaba Sharwan kuwa lokacin dasuka bar birnin Darul Hunam suka nausa cikin daji sukaci gaba da tafiya don isa birni na biyu wanda daga shi saura birni daya kacal su fice daga cikin nahiyar gaba daya sai katsam sukayi gamo da wata runduna ta wadansu mayaka wadanda basu wuce su dari da arba'in ba.Wadannan mutane sunyi shiga ta kamala,suna sanye da fararen tufafi mazansu da matansu,ko wannensu ya boye tsiraicinsa.Har dakarun Su Siyama sun zare makamansu da nufin su yaki wadannan tsirarun mutane sai Siyama ta daka musu tsawa ya dubesu tace,ai babu yaki tsakaninmu a wadannan mutane,domin sune wadanda aka hana mu da yin yaki dasu,sune ma'abota addinin MUSULUNCI... ME ZAI FARU TSAKANIN KABILAR SU SIYAMA DA WANNAN RUNDUNA TA MUSULMAI? IDAN RUNDUNAR SU SARKI DARWAZ SUKA RISKI RUNDUNAR SU SIYAMA WANE IRIN AZABABBEN YAKI ZA'AYI? SHIN SARKI DARWAZ ZAI CIKA ALKAWARIN DAYA DAUKARWA SARKIN ALJANUN? Mu hadu a littafi na shida don jin yadda zata kasance. Saidai Littafi na shida (6) bai fito ba,sai mu tsaya sai ya fito. GUDUN TSIRA 5 Littafi na biyar Na Abdulaziz sani madakin gini Ebook creator:- Suleiman Zidane kd...
Domin samun wasu littafan zaku iya yi mana magana ta whatsapp ta wannan Number ....
09064179602

1 Comments

Post a Comment