KISAN GILLA 2 COMPLETE

K


 IS AN GILLA2
Littafi Na Biyu (2)
Complete Book
.
Marubucin Littafin
Abdul Aziz Sani M/Gini
Typing Suleiman zidane kd
.. ....... .......
Filine mai fadi wanda aka kewayeshi daragar karfe musamman sarki zamaru yasa aka shirya
wannan wuri domin baiwa kansa horon yaki
tsawon shekaru ashirin da daya kullum sai sarki
zamaru ya jarraba jarumtakarsa akan dakarunsa acikin wannan fili kuma yana yin yakine da mutum arba in shi kadai
yake ragargazarsu a cikin kankanin lokaci saboda jarumtakarsa
da iya yakinsa, mutum daya daga cikin arba in din baya tsira
da lafiyarsa wani lokacin ma idan tsautsayi ya ratsa wasunsu
na rasa rayuwarsu
banda sarkin yaki Amzad babu wani sadaukin daga cikin mayakan kasar wanda
sarki zamaru bai kaishi kasa ba shima din don
basu taba kafsa wa bane
yauma kamar kullum sarki zamaru ya tunkaro wannan filin jarumta a cikin gagarumar
shigar yaki yana rike da wata zabgegiyar takobi gami da wata garkuwa irin ta
gidan sarauta mai tambarin karagar mulkin birnin
madinatul hashwar bisa mamaki sai sarki zamaru ya hango
filin yakin wayam babu ko badakaren guda
cikin tsananin mamaki da fishi sarki zamaru ya buda baki ya kwallawa wani
hadimin kira mai suna zabbaru nan da nan saiga zabbaru ya rugo har yana sassarfa
don biyayya da isowarsa gaban sarki zamaru sai ya zube kasa
bisa gwiwoyinsa cikin biyayya sarki ya dubesu
da kakkauran murya yace menene
dalilin da yasa yau sarkin yaki bai turo da dakaru arba in wadanda zan yi yaki dasu ba?
Zabbaru ya risina cikin biyayya kansa na sunkuye a kasa yace ya shugabana ai amzad ya zo da dakaru arba in
kamar kullum amma sai gimbiya ta sallameshi tace
itace zata fuskance ka
cikin tsananin kaduwa da mamaki sarki zamaru yace wannan wace irin maganar banzace
kake mini haka ?
Tayaya gimbiya zatace zata tareni da yaki alhalin
bata taba rike takobiba a rayuwarta kafin sarki zamaru ya gama rufe bakinsa sai ya jiyo
sukuwar doki a bayansa koda ya waiga sai yayi arba
da yarsa gimbiya Musaira bisa wani farin ingarman doki tayo shigar yaki na bakin sulke bata
rufe fuskarta ba da hular karfe kuma ta tattare gashin
kanta ta daure ya zubo har kasan kwankwasonta
duk inda ake neman mace mai kyau da sura gimbiya musaira ta kai ta wuce misali
sai abinda ido suka gani
kafin sarki zamaru ya ankara tuni musaira ta dako
tsalle a sama tana mai barin kan dokin kawai sai ta zare takobinta ta
kawo masa wawan sara a wuya saboda karfin saran sai da sarki zamaru ya durkushe kasa a lokacin da yayi wuf ya kare harin da
takobinsa musaira na dira a kasa bisa kafafunta
sai taci gaba da kaiwa sarki zamaru sara da suka cikin zafin nama juriya da bajinta nan fa suka kacame da azababben
yaki
tamkar tsofaffin abokan gaba, sai da suka shafe kusan
dakika dari da arba in suna bakin gumurzu dayansu bai samu nasarar kowa
lakutar jikin daya ba
Al amarin da ya matukar fusata sarki zamaru kenan
kawai saiya shammaci gimbiya musaira ya sauya salon yaki ya fyalli kafarta tayi katantanwa a sama sannan ya
doki kirjinta da kafarsa guda ta fado kasa a matukar galabaice ta mike zaune da
kyar ta tofar da yawun jini
kawai sai sarki zamaru ya kyalkyale da dariya sannan ya mikawa gimbia musaira
hannunsa ta kama ya tashe ta tsaye ya dubeta yace yaushe ne sarkin yaki amzad ya baki horon yaki haka bansani ba
a tunanina ko rike takobi baki iya ba menene dalilin
da yasa kika bata lokacinki kika koyi yaki haka kuma me yasa
kika boye mini
koyon yakin naki sa adda gimbiya musaira taji wadannan tambayoyi sai tayi murmushi
a lokacin da tasa tafin hannunta ta share dan jinin
dake kan lebanta tace yakai abbana na sani cewa zaka iya kare rayuwata da lafiyata a ko da yaushe to amma ranar da babu kaifa waye zai
kareni
a matsayina na yarka guda daya jal a wannan duniya
mai shirin gadon karagar mulkinka wata rana ya kamata ace na zama
jaruma kamarka
tun ina karama na gane cewa nasha jarumtaka a nonon uwata kuma na gajeta
a cikin jininka, don me bazan koyi yaki ba in zama
cikakkiyar jaruma
ka sani cewa wannan duniya cike take da masoya da makiya
ba mamakima a cikin fadawanka da makusantar ka ko talakawanka akwai mai shirin daukar fansa
a kan ka kaga kenan idan bai sami damar cutar da kai ba zai iya kokarin cutar dani ko
mahaifiyata a yanzu ko nan gaba
na sani cewa idan na sanar da kai cewa ina son
na koyi yaki hanani zakayi saboda ganin cewa kowa
na shakkarka a garinnan kai
bama a garinnan ba a gaba daya kasashen dake makwabtaka
damu ba masarautar da bata shakkarka. Waishin menene dalilin da yasa kai da sarki huzainu kuke girmama juna kuma sarakuna ke nuna biyayyar dole
a gareka suna kawo maka gaisuwa da dukiya amma banda sarki huzainu gashi a kasarsa babu tarin dakaru da mayaka kamar namu?
Hm Yarinya kenan baki san waye ubanki bane da bakiyi
wannan Tambaya b nine Al amin Ahmed Guyson
me zai hana mu shirya yakin sumame muje mu murkusheshi domin mu fadada
kasarmu mu bunkasa arzikin tunda kasar tasa na
daf da tamu ni ina tabbatar da cewa a dare daya zamu iya
cinsa da yaki ko kuwa saboda ana cewa babu matsafi kamarsa
a wannannahiya shi yasa kake shakkarsa yakai abbana kayi sani cewa matsafa sunfi sarakai
son duniya komai daren dadewa wata rana
Sai yayi ynkurin mallake tamu kasar, sa adda gimbiya
musaira tazo nan a zancenta sai sarki zamaru ya tari
numfashinta cikin fishi gami da daga murya yace kada ki sake shiga tsakanina da
sarki hizaunu domin amininane kuma akwai babban
sirri tsakanina dashi wanda ba zaki taba sanin saba
bisa laifin da kika aikata na koyon yaki ba tare da sanina ba na kafa
miki takunkumin fita ko ina na tsawon kwana bakwai
koda gama fadin haka sai sarki zamaru ya juya ya nufi cikin gidan sarautar ya bar gimbiya musaira a tsaye cikin tsananin fishi domin a rayuwarta babu abinda ta tsana sama da irin
takunkumin da sarki yake yawan kafa mata na fita da
yin rangadi a birnin
Tun tawowar gimbiya musaira daga kuruciya kawo izuwa
yanzu da ta cika shekara goma sha tara a duniya duk inda zataje tana tare da dakaru gami da kuyangi ba a barinta ta sami sakewa
bata da kawa bata da aboki sai dakaru da hadimanta kadai
su kansu da zarar anga ta fara sabo da dayansu sai a sauyashi sarki zamaru ya tsara hakan kuma umarnin boka hizainu ne gimbiya musaira tasha yin kuka akan hakan kuma duk da ita don tabbatar da tsaron
lafiyarta ne
nan dai gimbiya musaira ta tafi zuwa masarauta cikin
fishi da matukar damuwa saboda a yau dinnan ta shirya zuwa kasuwa da yamma
kuma gashi an kafa mata dokar fita
a rayuwar gimbiya musaira tana son tayi mu amala
da talakawa kuma tana son ta yawata a cikinsu ba tare da an gane ko ita wacece ba amma saboda sarki zamaru
yasa idanuwa a kanta damar hakan ta gagara
lokacin da gimbiya musaira ta iso cikin turakar ranta a bace harma idanuwanta sun ciko
da kwalla saboda takaici da bakin ciki sai tayi arba da wani hadiminta a tsaye yana gyara shinfidar gadonta
wadansu kuyangi guda biyu na gefensa hagu da dama suna gyara matasan kan gimbiya sai yai sauri ya sunkuyar
da kansa kas kuma ya juyo ya nufi kofar fita daga turakar kawai sai yaji
gimbiya ta kira sunansa tana mai cewa yakai udez tsaya anan ina son yin magana
da kai
udez ya tsaya cak jikinsa na kyarma saboda tsoro da mamaki
ba komaine ya fefa udez a cikin tsoro da mamaki ba face tunda ya fara yiwa gimbiya
aiki bata taba kiran sunansa ba kuma bai taba magana da ita ba tsawon dakika biyu face
tace dasu ku fita ku bani wuri
ba cikin sauri da biyayya kuyangin sukafice kuma suka
janyo kofar turakar suka rufeta bam ya zamana cewa
udez da musaira kacal a cikin turakar musaira ta
tunkaro udez gadan gadan tamkar zata rungumeshi
al amarin daya kara dugunzuma hankalinsa kenan ko ina a jikinsa ya
ci gaba da karkarwa yaji kamar ya fasa ihu koya
runtuma da gudu don gudun kada ya aika ta wani babban
laifi wanda zai iya zama sanadin ajalinsa tunda yasan halin sarki zamaru ba sani ba sabo
sai da muraisa tazo daf da udez yadda suna iya jin
numfashin juna sannan tace nayi bincike akanka na sami tabbacin cewa kafi
kowa dadewa a bauta a wannan gidan sarauta kafi
kowa sanin sirrin mahaifina da kuma sirrin masarautar
nan
ance kana da tarihin sarakunan da suka gabata har
izuwa kan mahaifina saboda yardar da mahaifina yayi maka kaine kadai da namiji daya taba shigowa nan cikin turakata har yayi mini
hidima mahaifina ya boye mini wadansu al amura nasa wadanda nakkishirwar saninsu
lallai daga bakin kane kadai zanji amsar tambayoyin da na dade ina yi masa su yaki bani amsar tasu tambayoyina
guda biyu ne rak
mafi mahimmancin ..
Ta farko mutuwar dan uwansa sarki hisham wanda akace cutar kankanin lokacine ta
zama sanadin ajalinsa? Tambaya ta biyu kuma itace menene dalilin da yasa sarki ya hanani tarayya da ko wa a birninnan na taso a cikin rayuwar kadaici ta rashin
kawa ko aboki?
Bayan wadannan tambayoyi bani da wata bukata daga gareka sai guda daya bukatar
kuwa ina son duk yadda za ayi a daren yau ka fitar dani daga cikin gidan sarautar nan ka kaini inda zanyi nishadi
domin na huce bakin cikin zuciyata, in kaimin haka cikin sirri ba tare da kowa
ya saniba zan sa sarki ya mallaka maka gida ka huta da biyan haya
a cikin aljihunka zan baka kudin da zaka iya yin noman bana a gonarka harma ka dawo da dabbobinka da suka mutu a cutarna na annoba
koda gimbiya musaira tazo nan a batunta sai idanun
udez suka zazzaro ya rasa abindake masa dadi a duniya
domin ga bikin zuwa amma babu zanin daurawa
ehm Al amin Guyson Sunana Dan Misau, tabbas bashi da burin da yafi ya mallaki gida
a rayuwarsa kuma yayi noma da kiwo to ammafa idan ya
biyawa muraisa bukatarta har sarki ya gano hakan
tamkar ya siyar da rayuwarsa ne koda ganin hakan sai hawaye ya zubowa muraisa nan da nan kuma fuskarta ta juya
izuwa tsananin fishi da rashin imani kawai sai ta zaro wata sharbebiyar
wuka a jikinta ta dora kaifin ta akan makogwaron udez ta dan danna ta yankeshi jini
ya zubo udez yayi dan ihu sakamakon zafi da zugin da yaji ta dubeshi tace na rantse da girman
uwata idan baka biya mini daya daga cikin bukatuna ba yanzu take zan aika ka barzahu maimakon ajalinka ya rataya a hannun
sarki zai rataya a nawa
saboda tsananin firgici udez baisan sa adda hawayen tsoro ya zubo masa ba ya budi baki da kyar cikin hadiyar
miyau yace zanyi iya biya mikiBukatarki ta karshe na fitar dake daga cikin gidannan
a sirrance batare da kowa ya sani ba har ki dawo amma bazan iya sanar dake amsoshin
wadancan tambayoyi ba guda biyu, muraisa tace ashe kenan har abada bazan daina bakin
cikida ya addabi zuciyata ba tunda sanin amsoshin nanne kadai
zai yaye min su
in kuwa hakane gwara na kashe ka muryar udez na rawa yace
aa zaki iya sanin amsar tambayoyinki daga bakin sarkin yaki shine ma
yafi kowa saninamsar amma bansan ta yadda zaki
iya shawo kansaba har ya amince ya sanar dake sa adda gimbia muraisa taji
wannan batu sai tayi shiru tana tunani kawai sai ta
tafi izuwa wata turaka ta dauko auduga tazo ta likata
awuyan udez don tsai da jinin dake diga sannan ta dubeshi
cikin murmushi tace misalin wane lokaci zaka fitar
dani daga cikin gidannan
Koda jin wannan tambaya sai murmushin farin ciki ya subucewa udez saboda
yasan cewa ya tsira daga hannun mutuwa don haka sai
ya dubi muraisa cikin fara a yace bayan rana ta fadi gari
ya soma duhu a lokacin da ake ta hada hadar cin abinci kedai kawai
kiyi duk abinda zan umarceki da yi sabawar hakan zata janyo rashin nasara
udez na gama fadin haka sai ya mika mata wani kullin kaya dake hannunsa
yace wannan kyana aikina ne na gidannan da zarar rana ta fadi gari yayi duhu ki shiga cikin kewaye ki cire tufafin dake jikinki
ki sanya wadannan ki tabbatar da cewa kinyi shigar maza kin
batar da duk wata sura ta ya mace ajikinki
udez na gama fadin hakan sai ya juya da sauri ya fice
daga cikin turakar har yana
tuntube kamar ace kyat ya saki fitsari a wando
burinsa kawai yaga ya fice lafiya ba tare da ya rasa rayuwarsa ba
ita kuwa gImbiya muraisa
sai ta bishi da kallo tana yi masa murmushin
dariya gami da farin ciki bisa ganin cewa zata sami biyan
bukatarta.....
Suleiman zidane kd...
Whatsapp 09064179602
.....
KAMAR YADDA udez ya umarceta da yi haka tayi
wato rana na faduwa muraisa ta shiga kewaye ta cire tufafin dake jikinta ta sanya wadanda udez ya bata ga shin kanta
kuwa saita tattareshi ta sanya wata hula sai ta zama kamar askin kwalkwal Gimbiyq tqyi
Ta boye gashin ko alamarsa ba agani dama an bayar da dokar kada kowa ya sake shigowa cikin turakarta face bawa udez
sai da gimbiya muraisa ta shafe sa a na wani lokaci
a wannan lokaci tuni an dan jima da fara hada hadar cin abinci
nan fa hankalinta ya duunzuma tafara tunanin ko bawa udez yaci amanar tane yaje ya sanar da sarki duk abinda ya faru a tsakaninsu tana cikin
wannan haline kawai taji an turo kofar turakar tata
nan take zuciyarta ta buga da karfi saboda ta san cewa in banda sarki babu wanda ya isa yayi mata irin wannan shigowar ta banko kofar daki ta wangame gaba daya haka kuma
da karfi har tana dukan bango bisa mamaki sai gimbiya taga ashe bawa udez ne dauke da wani kwanan abinci babba kwanan a cike yake da abincin dakaru udez ya dubi gimbiya cikin alamun tsoro yace
ki gafarceni ya shugabata yau zan saki dako gashi baki taba
daukar abu mai nauyin kamar haka ba
tayi murmushi tace waya gaya maka ban taba daukar
abu mai nauyin wannan ba to ka sani cewa na dauki dutsen da yafi wannan kanon nauyi sau uku a lokacin da nake
karbar horon yaki a wajan sarkin yaki
udez ya maida mata da martanin murmushi yace tabbas
na gamsu yanzu ina son ki bini a baya ki sunkui da kanki har mufice daga cikin gidan nnan kada ki dago
da fuskarki kuma ka da kiyi magana da kowa
mutum daya ne jal zai iya gane ki a wannan shiga da kika yi
kuma ba kowa bane face sarki amma na tabbatar da cewa babu abinda zai fito da sarki daga cikin turakarsa a wannan lokaci zomu tafi
udez na gama fadin hakan sai ya juya ya fice yana dauke da wani babban tambulan na ruwan inibi ita kuwa gimbiya muraisa sai tayi sauri ta dauki wannan kwanon abinci ta aza a kanta kuma ta
sunkui da kanta kas tabi udez a baya tamkar bawa da ubangidansa komai kallon kurillan mutum bai isa ya gane cewa muraisa mace ce ba namiji ba, haka dai suka ci gaba da tafiya a cikin harabar gidan sarautar suna wuce dakaru
hadimai da barori harma da kuyangi
da yake bawa udez na hannun daman sarkine duk abinda yake yi a gidan sarautar babu mai tuhumarsa sai da suka iso har kofar karshe ta fita daga gidan ba tare da sun fuskanci wata matsala ba
kwatsam ba zaato ba tsammani saiga sarkin yaki amzad
ya shigo cikin gidan sarautar da sauri har suka bangaji juna
shida udez
cikin sauri udez ya zube kasa a gaban amzad yace ka gafarceni ya shuagaban mai makon
sarkin yaki amzad yayi fishi sai ya wuce gaba ko kallonsa baiyi ba koda amzad da muraisa suka gifta juna sai tsigar jikin amzad ta tashi don haka sai ya
waigo da sauri ya kwalawa udez kira udez ya juyo a firgice hantar cikinsa na kadawa a lokacin da idanunsa suka zazzaro ya tako a
hankali ya iso gaaban sarkin yaki amzad
ya dubeshi a nutse yace yau kuma nenene dalilin
da yasa zakayi irin aikin da ba naka ba na tabbatar da cewar wannan tambulan da kake dauke dashi na ruwan inibi na masu gadin kofar gidannan ne saboda me zaka wulakanta kanka haka alhalin kaine babban
hadimin sarki
koda jin haka sai bawa udez yayi murmushi yace
haba ranka ya dade baka lura bane da kyau ai wannan tambulan din irin na sarki ne kuma ruwan inibin dake cikinsa na musamman ne gidan
waziri zamu kai
koda jin wannan batu sai amzad yayi murmushi ba tare
da ya kara cewa uffan ba sai ya juya ya nausa izuwa cikin gidan sarautar cikin hanzari udez
da gimbiya muraisa suka ci gaba da tafiya har suka sami nasarar ficewa daga cikin gidan sarautar gaaba daya ba tare da sun
fuskanci wata damuwa ba
Nine Al amin Ahmed Misau, Guyson sunana kenan
kai tsaye suka kunna kai zuwa cikin gari basu
zame ko ina ba sai wani babban gidan saida abinci mallakin wata mace da ake kira kimaratu
shi dai wannan gidan abinci ya shahara a cikin birnin na madinatl haswar domin matattara ce ta manyan baki da kanana
kimaratu karuwace ta manyan mutane domin daga sarakai
attajirai ke zuwa wajanta don haka babu wanda yayi mamakin yadda ake yi ta mallaki wannan gidan abinci
wanda a kullum ta Allah akanyi ciniki na sama da dinare dubu dari
fiye da shekaru goma sha biyar baya wannan gidan abinci ya bunkasa don
haka ne kimaratu ta zamo babbar attajira
A dai dai lokacin da bawa udez da gimbiya suka
iso wannan gidan abinci ne wasu bakin fatake suka iso
bisa dawakai kimanin su dari uku shugabansu na cikin wani babban keken doki na alfarma
su kuwa sauran jama ar tasa suna bisa ingarman dawakai cikin shigar yaki mai kwarjini
da ban tsoro domin kai da gain kura kasan zataci mutum
nan da nan wani yaron kimaratu ya kai mata labarin cewa yaufa ga wadansu manyan baki sunzo
dajin haka sai kimaratu ta mike zumbur ta rugo waje da gudu ta zube kasa a gaban shugaban fataken a lokacin da ya zuro kafafunsa kasa daga cikin keken doki
babu abinda zai baiwa mutum mamaki kuma ya bashi dariya face ganin yadda
kimaratu ta rugo da gudu duk da Cewa nauyin jikinta yakai na buhun alkama biyu sakamakon
kibar da take da ita nan fa ta zube kasa wanwar a gaban shugaban fataken ta kama kwasar gaisuwa
hakika rashin
sani yafi dare duhu inda kimara tasan wanene wannan shugaban fatake kuma ta san abinda ya kawo shi wannan gidan abinci nata da tayi babbar nadamar yi masa marhaban
nan dai tana rawar jiki ta yiwa shugaban fataken jagora shi da jama arsa suka shiga cikin gidan
gidane babba mai dauke da babban falo cike da kujeru da tebura gidan a cike yake da mutane maza da mata ana ta ciye ciye da shaye shaye ma aikatan wannan gida masu raba abinci a abin sha a kalla sunkai su dari da sha daya kuma kaso biyu cikin
ukunsu mata ne sannan akwai dakaru masu tabbatar da tsaro ,
lokacin da kimaratu da wadannan bakin bafatake suka shiga cikin gidan abincin bawa udez da gimbiya muraisa na tsaye a gefe daya a kofar gidan abincin
koda muraisa taga yadda ake ta haba haba a wannan wuri cike da jama a sai zuciyarta tayi sanyi ta kamu da matukar
farin ciki nan daisuma suka shiga cikin gidan
da shigarsu sai suka nufi wani teburi daban wanda babu kowa a kansa suka je suka zauna nan take suka bayar da umarni aka kawo musu ruwan inibi
caraf sai gimbiya ta tari numfashin bawa udez tace
A'a ni ba zansha ruwan inibi ba abinci zak sa a kawo mun
cikin tsoro da mamaki udez ya zaro idanu ya dubeta cikin rudu yace haba
ranki ya dade yaya ke da kika saba cin abincin irin na gidan sarauta mai
lafiya da daraja yanzu kuma zaki zokici na kasuwa
koda jin haka sai gimbiya tayi murmushi tace ai mahaifina yace idan kaje gari kaga kowa da bindi kaima ka nemi wani abu ka daura
haka dai udez ya sake bayar da umarni aka kawowa gimbiya farfesun kifi da gurasa
ta fara ci koda ta dago kai saita hango shugabawadannan bakin fatake tare da wani yaronsa suna kalle kalle a cikin gidan kuma suna yiwa junansu rada koda ganin haka sai hankalin
gimbiya ya tashi ta dubi bawa udez cikin alamun tsoro tace ban yarda
da wadancan mutanenn ba ba cin abinci ne ya kawo su nan ba
da jin haka sai udez yayi murmushi yace saboda me kika ce haka
gimbiya ta numfasa tace sarkin yaki ya gaya min cewa alamar munafiki shine yawan
kallo da gulma nidai jikina ya bani cewa wadannan
mutanann barayi ne
kafin kowa ya ankara zare takubbansu sun ritsa dukkanin dakarun dake tsaron gidan
shikuwa shugaban dakarun fataken sai yayi wuf ya cafko kimaratu ya dora wata sharbebiyar wuka a kan makoshinta yace maza kisa a kaimu inda ma ajiyar kudinki suke
cikin razani da firgici gami da rawar murya kimaratu tace aini bana ajiye
kudi a nan gidan
shugaban yan fashin ya daka mata tsawa ta firgita ainun sannan yace idan kika raina mana hankali zaki rasa rayuwarki
yanzun nan ki sani cewa kafin muzo nan saida muka san sirrinki da sirrin gidan nan a cikin dakarunnan can guda goma sha biyu akwai rijiya a cikin na tsakiyarsu a cikin rijiyar akwai wata katuwar akwatin karfe mai tsawo da fadin kamu ar ba in mukullin wannan akwatu muke bukata yanzu yanzu ko kuma ki rasa rayuwarki
koda jin wannan batu sai tsoro da mamaki suka baibaye kimaratu ta tabbatar
da cewar lallai wadannan bakin fatake rikakkun yan fashine kuma lallai sun sami hadin kan daya daga cikin
hadimanta wanda ya sanar da su sirrin ma adanarta
har kimaratu ta budu baki za tayi magana sai akaga an banko wannan kofar daki dake tsakiyar dakunan goma sha biyu wani kyakkyawan saurayi ne ya fito daga cikin dakin
ma abocin kyawu da kwarjini kallo daya zaka yiwa wannan saurayi ka gane cewa ya cika
sadauki domin kirar jikinsa itace amsa riga mai yankakken hannuce wadda ta
bayyana faffadan kirjinsa gami da damatsan hannayansa saurayin na dauke da wata zabgegiyar takobi goye a gadon bayansa
hannunsa na hagu na rike da wata katuwar kuba
fuskarsa cike da murmushi ya dubi shugaban yan fashin
yace lale marhaban da sarkin barayi Huzaga bn Salfas ka sani cewa wannan kuba dake hannuna itace mabudin wannan akwatin kudin da aka zo nema nine
maigadinta wannan mace daka ritsa da wuka mahaifiyata ce idan ka kuskura kayi
mata rauni kwatankwacin girman silingashi zaka koma gida
ka iske gawar matarka razina da danka Darsil wadanda
ka rabu dasu a jiya sun tafi izuwa birnin darul hasin
kamar yadda ka shafe kimanin watanni uku kana nazari da bincike akan dukiyar
mahaifiyata haka nima na shafe watanni uku ina nazari da bincike akan ka da iyalanka
don tabbatar da tsaron dukiyar mahaifiyata
kasani cewa shekarata goma sha shida ina karbar horon yaki a wajan sarkin yakinmu ba don komai ba sai domin na kare
wannan dukiya ta mahaifiyata
ga fili ga mai doki ga makullin akwatin kudi kuma gaka ga yaranka
idan zaka iya karbar makullin ku jarraba mu gani
sa adda wannan saurayi yazo nan a zancensa sai shugaban
yan fashin ya kamu da tsananin mamaki ya kurawa jarumin saurayin idanu kawai kuma yayi shiru har zuwa tsawon
yan dakiku
A wannan lokaci gaba dayan mutanan dake cikin wannan dakin
abinci a firgice suke kowa ya kame kamar gunki an daina ci da shan komai
wasu da yawa jikinsu kyarma yake yi babu wanda yafi bawa udez firgita da
Da shiga tashin hankali domin yasan cewa idan wani abu ya sami gimbiya tasa ta kare gaba daya dakin cin abincin yayi tsit
tamkar babu mai rai a cikinsa kawai sai akaga shugaban yan fashin ya ture
kimaratu daga gabansa ta fadi can gefe daya cikin zafin nama ya zare takobinsa
maimakon ya afkawa saurayin sai ya dubi wasu daga cikin
dakarun nasa yace ku cisgo mun kan wannan yaron ai kuwa nan take kimanin su dari suka rugo da gudu izuwa kan
jarumin saurayin
wohoho bala i ba a sa masa rana kuma mai karfi sai Allah
ya isa nan fa aka ruguntsume da masifaffen yaki da farko hankalin gimbiya a tashe yake donji take kamar ta rusa ihu amma ana fara
bakin gumurzun tsakanin yan fashin da saurayin
sai ta sami abin debe kewa abu na farko da ya jefata
cikin tsananin mamaki shine ganin irin salon yakin da
jarumin yake yi iri daya ne sak danata
shin malamin da ya bata horon yaki shine ya koyar da wannan saurayi
amsar da bata sani ba kenan suma sauran jama ar
dake wajan sai suka kamu da tsananin mamakin jarumtar wannan saurayi saboda
yaune karo na farko da aka ga irin jarumtakarsa
A lokaci guda dakarun darin sukayi masa rubdugu suna kai masa sara da suka ta ko ina yayinda ya rina yin wata irin katantanwa
a tsakiyarsu yana kare
dukkan hare harensu ba tare da ya maida martani ba sai da aka shafe kusan dakika dari uku da sirrin ana wannan fafatawa ba tare da
dayansu ya sami nasarar koda karzanar jikin jarumin
ba
tabbar jarumin ya nuna ba ajinta da jarumtaka a mma fa hantar cikin kowa ta
kada a dakin saboda babu wani tebur ko
kujerar da bata ragargaje ba a cikin dakin sakamakon
wadannan artabu
hankalinn kowa sai da ya dugunzuma banda na Guyson mai typing din littafin
hatta ita kanta gimbiya data kasance jaruma sai gashi tana buya da labewa a karkashin
abubuwa don kada
tsautsayi ya sameta bisa dole wadannan dakarun
dari suka janye daga kan jarumin suka koma can baya
inda shugabansu yake sukayi cirko cirko suna haki saboda gajiya suna sauraron
umarnin da shugabansu zai sake bayarwa ......
Zidane kd
Labari ya isowa AA Misau cewa...
suna sauraron
umarnin da shugabansu zai sake bayarwa kawai sai shugaban
ya daga hannunsa na dama ya bude dukkanin
yatsunsa biyar ashe hakan na nufin
gaba dayan dakarun su dari uku su afkawa jarumin ai kuwa sai suka zare takubbansu
duka suka ruga izuwa kansa koda ganin hakan sai shima ya zare takobinsa dake bayansa ya tunkaresu
aka sake kacamewa da masifaffen yaki amma wannan karon yakin ya sauya salo domin shima jarumin ba kare kansa kawai yakeyiba yana maida marta ni
nan fa labari ya sha ban ban domin sai gani akayi yana bazar da dakarun
suka rinka zubewa kasa sakamakon jinin dake tsartuwa da feshi ajikinsu duk da kasancewar hakan in dai ba kawunansu ya tsinkeba sai gashi suna
mikewa suna kai masa muggan hare hare saboda
nacinsu da juriyarsu
tabbas masu iya magana sunyi gaskiya da sukace sarkin yawa yafi sarkin karfi
duk da cewa wannan jarumin saurayi yana da matukar karfi jarumtaka da zafin nama sai gashi wadannan
mayaka dari uku sun fara kuntata shi
domin har sun sami nasarar yi masa rauni guda biyu daya raunin akan cinyarsa
na dama
aka yankeshi
wurin ya dare jini na zuba rauni na biyu kuwa a gadon bayansa aka sareshi wajan yayi dan rami yana zubda jini
tsabar juriya da jarumta kace tasa bai sare ba bisa kwarin guiwar ganin shima ya bazar da kimanin mutane dari da sittin a cikinsu
wadanda ko mikewa ba zasu iya ba wasu ma halin da suke
ciki zai iya zma sanadin ajalinsu
lokacin da gimbiya muraisa ta lura da halin da take ciki a wannan yaki tsakanin
jarumin saurayin da wadannan yan fashi sai hankalinta ya dugunzuma taji ta kamu da tausayin saurayin komai taji tana son ya sami nasara akan yan fashin
to wai shin ma saboda me naji ina tausayinsa
tambayar da gimbiya ta yiwa kanta kenan kuma ta kasa gano amsarta tana cikin wannan tunani ne taji saurayin ya kurma uban ihu sakamakon
sara na uku da akayi masa akan cinyarsa na dama cikin tsananin fishi da juriya ya daka
tsalle sama ya sare kawunan mutum goma daga cikin
yan fashin a lokaci Guda
hakan ne ya razana su duka suka ja da baya shi kuwa jarumin sai ya durkushe kasa cikin yar galabaita yayi sauri ya yanki
rigar fatar dake jikinsa ya daure raurin cinyar don tsaida jin
koda ganin abinda ya faru sai kimaratu ta fashe da kuka don ta san cewa komai zai iya faruwa ga wannan da nata shi kuwa shugaban yan fashin sai ya bushe da dariyar mugunta ya nuna jarumin da hannunsa guda yace kai yaro karyarka
tasha karya
yanzun nan zamu yi maka KISAN GILLAH sannan mu karbe kubar dukiyar dake
hannunka ita kuwa wannan uwar taka tsohuwar karuwar
zata zamo mai shar dani ruwan giya
koda jin wannan batu sai jarumin ya kamu da bakin ciki
har hawaye ya zubo masa
nan take zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone cikin tsananin fishi ya ynkura ya mike tsaye da sauri yana mai kwarara uban ihu ai kuwa sai dakarun bayin suka sake afka masa aka ruguntsume da sabon azababben yaki
koda ganin haka sai gimbiya muraisa
ta yunkura domin ta kaiwa jarumin saurayin dauki amma sai bawa udez
ya yi wuf dakatar da ita ya dubeta cikin tsananin
tsoro yace kiyi mun rai ya shugabata idan wani abu ya same ki mutuwa zanyi
dajin haka sai gimbiya ta murrtuke fuskarta tamkar an aiko mata da sakon mutuwa tayi
wuf ta zaro wata karamar adda a jikinta ta dubi udez tace maza ka cire hannunka daga jikina ko na tsinke maka wuyanka ka sadu da abar da kake tsoro
Dajin haka sai udez yayi sauri ya janye hannunsa daga jikin na gimbiya jikinsana
karkarwafaruwar hakan keda wuya sai gimbiya ta dako tsallo sama ta dira a tsakiyar dakarun
yan fashin ta hausu da sara da suka ya zamana
cewa tana taimakawa jarumin sai gashi suna ta ragargazar yan fashin kafin cikar dakiku
dari hudu yan fasin sun zama saura su sittin da biyar
a tsaye sauran sun zama matattu
da nakasassu
koda ganin abin dake faruwa sai bakin ciki ya turnuke shugaban yan fashin ya kwarara uban ihu karfin ihun nasane ya sa tsirarun dakarun nasa
sukaja da baya suka rugo izuwa bayansa
a wannan lokacine gimbiya da jarumin suka hada baya
ba tare da sun juyo sun kalli juna ba sai jarumin ya budi baki yace saboda me ka taimakeni kuma wanene kai??maimakn gimbiya ta bashi amsar
wadannan tambayoyi sai tayi shiru don kada tayi magana yaji muryar mace
a dai dai wannan lokaci ne shugaban yan fashin ya kurawa gimbiya muraisa idanu har izuwa tsawon yan dakiku
kawai sai ya tuntsire da dariya yace haba ranki ya dade
menene ya shigo dake cikin sabgar talakawa
haka
kada ki shiga harkarmu ta neman arziki kin sani cewa ko giya na sha ba zanyi
yunkurin zuwa sata gidanku ba ki koma gefe daya kiyi kallo wannan fada ba naki bane
amma idan kika ki zan iya salwantar da rayuwarki a nan na dauki abinda
nazo nema na bar nahiyar gaba daya idan kika mutu a nan sai mahaifinki ya dauki dubun nan
rayukan talakawa
sa adda shugaban yan fashin yazo nan a zancensa sai kowa
ya kamu da tsananin mamaki ita kuwa gimbiya jikinta yayi sanyi ta koma gefe daya ta tsaya hakanne yasa ko ya kura mata idanu
a wajan
Musamman jarumin da mahaifiyarsa kimaratu domin a sannan ne suke kokarin ganoko
wanene wannan bakon
jarumi da aka kirashi da matsayin ya mace
shugaban yan fashin ya dubi tsirarun dakarun nasa yace
kada ku shiga wannan yaki tsakanina da wannan yaron koda kuwa kunga
zan hallaka in kuwa kuka shiga to dukkaninku mutuwa
zakuyi
yana gama fadin hakan sai ya dubi saurayin jarumin
yace
yanzu zamuyi fadan karshe idan ka kashe ni ka tserar
da dukiyar wannan karuwar wacce ba ita ce asalin uwarka ba
koda jin haka sai idanun jarumin suka zazzaro ya kurawa kimaratu idanu ita kuwa kimaratu
sai tayi sauri ta sunkui da kanta kas a lokacin da hawaye ya subuto mata
koda ganin haka sai jarumin yayi kururuwa ya daga takobinsa
sama ya rugo izuwa kan shugaban yan fashin yana mai kururuwa
burinsa kawai ya gaggauta kashe shugaban yan fashin domin ya tuhumi
kimaratu gaskiyar al amarin matsayinsa a gareta
koda ganin tasowar jarumin sai shima shugaban yan fashin ya rugo gareshi ai kuwa suna haduwa sai suka kacame
da azababben yaki mai tsananin ban tsoro
wohoho ai duk sa adda tsohon gwani masanin yaki
da tuggu ya hadu da sabon jini mai jarumtaka
da juriya dole ne ayi mugun gumurzu mai ban sha awa da ban tsoro saboda
kowannensuyana da irin baiwar da Allah yayi masa
sai da shugaban yan fashin da jarumin saurayin suka shafe
sa a uku rir suna gabza yaki na tashin hankali wadda kowannansu ya galabaita ainun tamkar zasuyi ragas
wani irin salon yakin suka rinka yi ya zamana cewa suna kaiwa junansu sara da suka gami da kai naushi da bugu
hannu da kafa duk a lokaci guda, nan da nan suka hadawa juna jini da majina
da kyar jarumin saurayin ya sami nasarar yiwa shugaban
yan fashin rauni uku
shi kuwa sau shida yana yiwa jarumin rauni alhalin ga wasu
raunika ukun a jikinsa
hakan ne yasa jarumin saurayin ya galabaita ainun a lokacin
da jiri ke dibarsa sakamakon jinin dake ta zuba a jikinsa
kuma asannan ne idanunsa suka fara gani dishi dishi kawai sai ya yanke jiki ya fadi
kasa da ruf da ciki tamkar ya zama gawa koda ganin haka sai farin ciki ya lullube shugaban yan fashin ya bushe
da mahaukaciyar dariya ta murna yazo kan jarumin saurayin
ya tsaya yana mai raba kafafunsa a kansa sannan ya sunkuyo da nufin ya tallafo kan
jarumin yayi masa
yankan rago
ba zato ba tsammani sai akaga jarumin saurayin ya
yunkuro cikin bakin zafin nama na bazato ya gabzawa shugaban yan fashin wawan naushi a fuska
saboda karfin naushin sai da yayi sama yaje ya maku da bayansa a jikin bango ya fado kasa magashiyan
kafin ya samu damar motsawa tuni jarumin saurayin ya daka tsalle sama daga inda yake ya dira a gadon bayansa da kokon gwiwarsa ta dama
kowa dake cikin falon gidan abincin sai da yaji karar karyewar kashin bayan
shugaban yan fashin nan take ya baje a kasa matacce
Al amin Guyson sunana kenana koda ganin abinda ya faru sai wadannan tsirarun dakarun nasa suka zube
kasa suna masu mika wuya nan take dakarun kimaratu suka kamasu suka daddauresu
shikuwa wannan saurayin jarumi sai ya sulale kasa sumammc
e
lokacin da jarumin saurayin ya farfado yana bude idanuwansa sai yaga kimaratu tare da
bakon jarumin da ya taimakeshi da kuma bawa
udez sai sarkin yaki amzad tsaye a gefe guda a cikin daga daga cikin dakunan gidan abincin yana
bisa gado saurayin jarumin ya dubi raunikan jikinsa yaga duk an dinkesu kuma an sa musu magani kawai
sai ya dubi kimaratu ya ce wacece uwata ta gaskiya kuma wanene wannan baokn jarumin daya taimakeni??
Maimakon kimaratu ta bashi amsa sai ta fasa kuka
a sannan ne sarkin yaki amzad ya dubi saurayin
jarumin yace
mahaifiyarka itace matar marigayi sarki hisham na wannan birni namu babu wanda yasan
inda take a yanzu kimaratu ce ta reneka tun
kana jariri kuma nine na kawo ka gareta na baka horon
yaki ne domin ka dauki fansar ran mahaifinka akan sarki yanzu
wanda ya kasance kanin mahaifinka
wannan bakon jarumin dake gabanka wanda ya taimakeka ba kowa bane face
gimbiya muraisa ya ga sarkin yanzu kasani tsakaninka
da ita babu gaba kada ka kuskura kayi tunanin
daukar fansa a kanta......
..
A nan ne LITTAFIN KISAN GILLAH NA BIYU YAZO KARSHE
MARUBUCIN YACE MU HADU A LITTAFI NA UKU.
Naku harkullu Suleiman, zidane kd..
Domin samun wasun littafan yaki and Hausa soyayya kuyi muna magana ta wannan number....
Ta whatsapp 09064179602

Post a Comment (0)