*_MACE ZA TA IYA BAWA MIJINTA ZAKKA?_*
*Tambaya*
Assalamu alaikum. Malam Menene sahihi akan mace tabawa mijnta zakkah ?
*Amsa*
Wa'alaikum assalam, ya halatta a zancen mafi yawan malamai saboda hadisin Zainab matar Abdullahi Dan Mas'ud wanda Bukhari ya rawaito a sahihinsa a lamba ta: (1462) da kuma Muslim a hadisi mai lamba ta: (1000) lokacin da ta nemi fatwa akan bawa mijinta sadaka kuma Annabi S.A.W. ya halatta mata hakan.
Malaman sun kafa hujja da wannan hadisin saboda kalmar sadaka ta kunshi farilla da sunna.
Aya ta (60) a suratu Attaubah ta yi bayanin nau'o'i takwas na mutanen da ake bawa zakka, daga ciki akwai talaka, hakan sai ya nuna mutukar miji talaka ne matarsa za ta iya ba shi zakka, tun da ba'a samu dalilin da ya fitar da shi ba.
Saidai Ibnul Munzir ya hakaito ijma'i cewa: "Bai halatta miji ya bawa matarsa zakka ba idan tana fama da talauci, tun da zai iya wadatata ta hanyar ciyarwar da Allah ya wajabta masa.
Don neman karin bayani duba: Sharhul Mumti'i (6/168) da kuma Fataawa Allajnah Adda'imah (10/62)
Allah ne mafi sani.
21/11/2017
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_____________________________________
» Zauren *_📖MIFTAHUL ILMI📖_* (WhatsApp).
→ Ga ma su sha'awar shiga Zauren 🔑 _*MIFTAHUL ILMI*_🔑 a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu *(07036073248)* ta whatsApp.