✤ INGANTATTUN MAGUNGUNA ✤*
*ISLAMIC MEDICAL CENTER*
☏+2348037538596
*SINADARIN YALWAR GASHI*
duk macen da take son gashinta yayi yawa, kuma Yayi tsawo ya dinga sheki sai ki samo wadannan maya-mayan da Zan fadi
● man habbatussauda
● man zaitun
● man kwakwa
ki dinga shafa su a kowane lokacin
*SINADARIN HANA ZUBEWAR GASHI*
duk matar da take son kar gashinta ya zube kuma taga yana Kara tsaho to ga dama ta samu, sai a samo wadannan maya-mayan da za a fada ta dinfa shafa su sune:
✤ man gelo
✤ man basilen
*SINADARIN SAMUN RUWAN NONO*
yar'uwa duk macen da take da karancin ruwan nono, to ga hadin da Zaki yi yar'uwa, za ki sami ruwan nono mai yawa, ga mahadan da Zaki tanada ki dinga sha aka-akai sune:
↳ madara ( peak)
↳ garin gero
↳ zuma
*MAGANIN CIWON NONO*
maganin ciwon nono ya kasu kashi daban-daban amma ga kaso daya daga cikin su, duk macen da take fama da ciwon nono da kuma rashin ruwa to sai ta sami garin hulba da garafin ta kwaba su da ruwan dumi, ta shafa tayi haka kamar sau uku, ( 3 ) ma'ana wuni uku Allah yasa mu dace.
*MAGANIN CIWON MARA*
ciwon mara wani abune da yake yawan damun ya'ya mata musamman a lokacin al'ada, to shi yasa na kawo maganin wannan matsala a cikin wannan post duk lokacin da kika fara jin ciwon ciki, sai ki sami:
৲ zuma
৲ zaitun
sai kowan ne ki sha babban cokali ( 2 ) da safe da yamma
*MACEN DA TA SAMU BUDEWAR GABA*
duk matar da gabanta ya bude amma ba ta San yarda zatayi ya koma ba, taba dama ta sami yar'uwa ita dai wannan hanya tana da yawa, amma ga wata hanya da Zaki Bi mafi sauki itace:
ki samo wadannan mahadan da Zan fadi.
ki tafasa shi ,ki matsa lemon tsami dan kadan a ciki, ki dinga zama zai hade ya koma dai-dai
⊗ sassaken bagaruwa
*MAGANIN RAGE GIRMAN NONO*
Mace da Allah yayi mata wannan baiwar kuma take jin yana damunta kuma take son ya rage girma, sai ki samo MUSDAKKIRIN ki shafawa nonuwa insha Allah zasu rage girma
*DOMIN SA GIRMAN NONO*
macen da take son nonuwanta su Kara girma to ga dama ta samu, domin da yawa zaka ga mata, suna da sha'awar haka, to ga hanya mai sauki
∩ cukui
∩ gero
∩ alkama
∩ citta
∩ masoro
sai ki dake su gaba daya a guri daya, sai ki samo madara mai kyau sai ki ringa debo wannan garin kina zubawa a madarar kina sha Zaki ga abin mamaki.
*DOMIN SAMIN NI'IMA*
macen da bata da yawan ni'ima a jikinta kuma tana bukatar ta samu ni'ima to ga dama ta samu yar'uwa in kina wannan Zaki ga abin mamaki
∞ dankalin Hausa.
∞ dabino
∞ madara
∞ aya
∞ alewar mata
∞ kwakwa
∞ gyadar mata
YADDA ZAKI HADA
yar'uwa ki sami aya ki jika ki sirfa ki wanke ki rage ki fitar da dusa, sai ki dauko dabino ki ki wanke shi, ki cire kwallayan ciki ki zuba a kan ayar ki, sai ki dauko kwakwarki ki fasa ki tsiyaye ruwanta a kofi, ki ajiye ruwan a gefe guda, ki dauko kwakwar sai ki yankata kananu, ki zuba a kanarki da dabino, sai ki dauko dankalinki, sai ki dauko gyadar mata ki gyara ta ki zuba a Kai sai ki sa kayan kamshi kadan sai ki bayar akai miki markada kar a sa ruwa mai yawa, idan aka kawo miki markada sai ki tace dusar ki ajiye ta daban, ruwan ma daban, sai ki dauko alewar mata sai ki zuba a ciki, sai ki zuba sikari a ciki, sai ki jujjuya kullum ya juya sai ki sa kankara ko kisa a firji yayi sanyi sai ki mai da shi ruwan sha kullum ki dinga yi ba Zaki yi kwana bakwai kina yi ba, sai kin ga ni'ima yadda zat a baibaye ki:
√ gyaran gashi
√ ruwan nono
√ maganin ciwon nono
√ samun ni'ima
√ gyara jiki
√ ciwon Mara