MUNGO PARK MABUDIN KWARA 35

35. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
www.bukarmada.blogspot.com
...


 
Muka shirya, muka tashi cikin jiragen ruwa daga Sami zuwa Sansandin. Da ya ke a ran nan babu iska, kuma jiragen babu rumfa, mun yi fama da zafi kwarai. Zafin ya yi zafi har kaina ya rika ciwo. Ni dai ban taba jin zafin rana irin na ran nan ba, don kamar a gasa nama a ciki. Mun shige ’yan tsibirai, da masunta da yawa a cikinsu, har dai muka kai Sansandin da hantsi karfe goma. Muka cim ma bakin ruwan dankare da jama’a wadanda suka zo ganimmu. Muka nemi yadda za mu sauke kayammu ma, muka rasa, saboda yawan jama’a, sai da Sarkin Sansandin, Kunti Mammadi, ya sa aka yi ta duka, ana kora. Nan da nan Mammadi ya sa aka kai mu masauki, muka zuba kayammu. A daren ran nan soja biyu kuma suka mutu, da Marshall da W. Garland. Amma kafin safe kyarkeci sun dauke gawar Garland, sai Marshall kadai aka tarar.
Ran nan muna zaune, sai Sarkin Sego ya aiko mini da kundun bindiga guda biyu da wata katuwar bagwanja burmammiya, ya ce in gyara. Na ce da dan sakon duk cikimmu babu wanda ya iya wannan aikin, ba sana'armu ba ce. Da kyar dai ya yarda ya koma da su. Ran nan kuma sai babban dan Sarkin Sego, wanda a ke kira Da, ya aiko mini da jirgi guda kyauta, amma ya ce yana so in sayar masa da bindiga irin wadda na ba uban, da takubba uku, da turamen ajanaku biyu. Na aika masa da takubba uku, da ajanaku kuma goma, shi kuma ya aiko mini da farin kudi dubu shida.
Sansandin gari ne babba, don Sarkin garin, Kunti Mammadi, ya ce mutanen da ke ciki sun fi dubu goma sha daya. Tana da masallatai a cikinta da yawa, har na ga biyu da suka ba ni sha'awa, ko da ya ke ginin Kasa ne. Akwai kasuwa babba, da rumfuna na zana da tabarmi. Kasuwar tana cika kwarai har dare. Akwai wani layi inda babu kome a rumfunan sai duwatsun wuya iri iri, wadansu kuwa shuni, wadansu sabulun toka, wadansu tufafi, sakar Jinne da ta Hausa. Har na ga wata rumfar ba a sayad da kome cikinta sai kwalli, wata kuwa sai farar wuta, wata kuma zobba da warwaro iri iri na farin karfe, da na tagulla, da na azurfa. A kofar gidajen da ke duban kasuwar kuma ga tufafi iri iri an rarrataye. Kusa da su ga layin 'yan gishiri. A wata babbar inuwa ta tsakiyar kasuwar a nan karagar mahauta ta ke, ga nama mai mai kamar na Ingila. A wata fuskar kuma ga layin masu giya. A kan jera kore kamar dari duk na giya. Kusa da su ga layin dukawa, suna aikin fatu iri iri da fara da ja da rawaya.
Ko da ya ke a kullum akwai mutane a kasuwar, amma babbar ranar cinta, Talata ne. Ran nan, irin mutanen da ke duruwa a wannan kasuwa yawansu yana da ban mamaki. Da mutanen gari da na kauyukan kusa duk su kan zo, su sayi abubuwa. ’Yan kiri kuma su kan kwashi hajja su kai kauyuka suna yankawa. Duk ranar kasuwa a kan yanka bajimai kiyayayyu kamar ashirin.
Bayan mun yi ’yan kwanaki sai na ga ya kamata ni ma im fid da wadansu kaya in sayar, in sami kudin sayen jirage, don kuwa na ga alamar ruwan Kwara ya fara ja da baya. Saboda haka sai na shirya rumfa, na bude kanti, na shirya abubuwan ado daki-daki yadda a ke yi a kantunan Turai. Nan da nan gari duk ya barko, kafin a yi haka an saye kayan nan duk na caje kudina. Rana daya kurum na yi cinikin farin kudi fiye da zambar dubu ashirin da biyar. Wannan kasuwa da na samu ta jawo mini bakin jini wajen fataken Jinne Larabawa. Saboda haka suka shiga yi mini kulle-kulle kamar yadda Larabawan Sego suka yi mini, da suka ce da Sarkin Sego in ya kashe ni za su ba shi dukiya wadda ta fi kyautar da na kawo masa. Suka ce masa kome na gaya masa dalilin zuwana kasarsa duk karya ne, na zo in kashe shi ne, in kashe dansa da magani, don Turawa su zo su sami kasar. Amma da ya ke Sarkin Sego ba mutumin banza ba ne, sai ya toshe kunnensa, ko da ya ke yawancin mutanen Sego da na Sansandin duk sun yarda da wannan makirci.
Ran nan sai ga Waziri ya zo daga Sego, ya kawo mini wani jirgi, ya ce Sarki ya aiko mini da shi kyauta. Da na duba sai na ga rabin jirgin duk icen ya rube, na ce a koma da shi. Bayan 'yan kwanaki aka sake aiko mini da wani babba, amma ko shi ma ya dan rube. Sai muka shiga gyara. Na sami taimakon wani Sojana wai shi Abraham Bolton, muka gyara jirgin nan, muka nane hujehujen da ke ciki. Muka sake inda ya ruba, muka dinke. Cikin kwana goma sha takwas muka mai da wannan jirgi na Bambara ya zama jirgin mulkin Ingila, na sa masa suna “Joliba.” Tsawonsa kafa arba’in, fadinsa kafa shida.
Ran 28 ga Oktoba, da safe kamar karfe biyar ya wuce da kwata, ajali ya saukam ma abokin nan nawa Mr. Alexander Anderson. Watansa hudu yana ciwo. Saboda haka na ji a raina lalle ya kamata im fadi kyawawan halin wannan mutum. Amma da ya ke mutane kadan suka san nagartarsa, zan yi makokinsa ne kurum a zuciyata.
Abu daya kadai zam fada watau tun ran da na fara tafiyan nan babu abin da ya taba duhuntar zuciyata sai lokacin da na saka Mr. Anderson cikin kushewa. A lokacin nan sai na ji kamar ni kadai na rage a cikin dajin Afirka!
Na kare shirina kaf ba na jiran kome sai dawowar Isyaku Sego, don in sa takardun labarin tafiyan nan a hannunsa ya koma da su Gambiya. Ran nan sai ga Isyaku da zuwa ya ce wai Sarkin Sego ya ce in yi maza in tashi kafin Larabawa su ji labarin zuwana. Muka shiga daura kaya, muka sayi garkuwa don tsare kammu daga masu ko kibau na mutanen da ke zaune a bakin Kwara. A nan Sansandin muka yi sallama da lsyaku na ba shi duk takardun ya juya zuwa Gambiya, ni kuma na ci gaba. A ran nan na rubuta takardu zuwa wurin manyana a gida da kuma matata. Gasu:
Cikin “Joliba”
Sansandin.
17 ga Nuwamba, I805.
Zuwa ga Mai Girma, Earl Camden, Daya daga cikin Waziran Sarkin Ingila.
Ranka ya dade,
Ga labarin tafiyata nan tun da na taso daga Kayi. Na sani wadansu abubuwan da na rubuta ba su isa a fade su ba, amma za su taimake ni tuna halayen mutanen Afirka da al'adunsu, yadda zan rubuce labarin wannan tafiya im maishe shi babban littafi, in Allah ya nufe ni da komowa kasarmu.
Ranka ya dade, kila za ka tuna yadda na kan rika kukan daminar Afirka, na kan ce ba za ta bar Turawa da rai ba. To, in an karanta wannan labari aka ga hasarar rayukan da muka yi tun daga tasowa Gambiya har isowarmu Kwara, za a iya gano gaskiyar maganata.
Lalle kam ba mu yi wani yaki da mutanen kasar ba, babu kuwa wanda wani naman daji ya ci, ko wani hadari ya kashe. Amma duk da haka na yi bakin cikin in shaida maka cewa daga cikin Turawa arba'in da hudu da muka baro Gambiya da su lafiya lau yau sai biyar kawai suka rage, Soja uku, da Laftana Martyn, da ni kaina.
Na tabbata wannan mummunan labari zai karya maka zuciya, har ka yi zaton al'amarin duk ya baci, amma ka tabbata, ranka ya dade, zuciyata ko kadan ba ta karai ba. Da taimakon soja daya na gyara wani babban kwalekwale, na maishe shi jirgi, yau na kafa tutar mulkin Ingila a kansa. Zan kuwa fara tuka shi in nufi gabas, in yi kokarin gano karshen Kogin Kwara, ko kuwa in halaka cikin kokarin. Har yanzu dai ban ji wani tabbataccen labarin da zan kama game da hanyar da wannan babban kogi ya bi ba, amma bisa kyakkyawan zato, bai fada ko'ina ba sai cikin teku.
Abokin nan nawa Mr. Anderson da kuma Mr. Scott duk sun rasu. Amma ko da sauran Turawan da suka rage sun mutu, kuma ko da ni kaina zan zama kamar matacce, na yi niyyar cin gaba. In dai ban sami kaiwa ga bukatata ba, to, in sami mutuwa a cikin Kwara!
In na yi sa'a na kai ga niyyata, ina zaton zan iso Ingila cikin Mayu ko Yuni, zam biyo ta West Indies.
Ina rokonka, ranka ya dade, ka ba abokina Sir Joseph Banks izni ya duba labarin tafiyan nan, kuma ina so a ajiye shi da kyau, don watakila wani hadari zai auka wa takardun da ke hannuna.
Ni ne mai biyayya gare ku,
MUNGO PARK.
Sansandin,
19 ga Nuwamba, 1805.
Zuwa ga matata,
A kullum in na zo rubuta miki wani abin da zai soki zuciyarki, sai in ji raina ya yi baki kirin. Amma haka Allah ya nufa, don shi kadai ke yin kome daidai. In sanad da ke kanenki, abokina, Alexander, rai ya yi halinsa. Zazzabi ne magamin ajalinsa, ya mutu a Sansandin ran 28 ga watan Oktoba. In kina son ki san kome da kome game da kanen nan naki sai ki tambayi tsohonki.
Na san yadda zuciyar mata ta ke, ku kan yi saurin firgita tun ba ma ga abin da ya shafi mazansu ba. Na tabbata yanzu kina nan kina zaton ina cikin wahala ne kwarai. To, in sanad da ke duk yadda zuciyarki ta nuna miki, dagular al’amarina ba ta kai haka nan ba. Gaskiya ne Mr. Anderson da George Scott duk sun bar duniya, kuma galibin mutanemmu duka sun mutu a kan hanya lokacin damina, amma ki tabbata ni lafiyata lau na ke. Da ma dai ruwa ne ya dame mu, yanzu kuwa ya kare, saboda haka babu sauran fargabar ciwo. Har yanzu kuma akwai sauran jama’a tare da ni wadanda za mu iya tsare kammu, ko da aka fada mu a kan hanya, har mu kai teku.
Duk mun zuba kayammu a cikin jirgi. Da ce na kare rubuta wannan takarda, im mun tashi, ba ni da niyyar tsayawa ko sauka a ko'ina sai mun dangana da teku. Na kuwa yi zaton za mu kai kafin karshen watan Janairu. Da ce mun kai teku, ba za mu tsaya ba, sai mu fada jirgin wuta sai Ingila. In ya yiwu tilas sai mun bi ta West lndies ne, to, ba za mu kawo Ingila da wuri ba, kila sai watan Mayu. Bababn abin da ya tsare mu, ya hana mu sauri tun da muka taso daga Gambiya, shi ne ruwa. Kullum fa muna shan dukansa, har ya zama shi ne asalin mutuwar wad'ansu Sojammu.
Na yi zaton ma kila kafin takardan nan ta sadu da ke, na zo Ingila - ki tabbata ba abin da zai faranta mini rai kamar in ga na sa fuskata wajen gida. Yau mun kare shirye-shiryemmu da mutanen kasar, kuma mun kafa filafilai, za mu tuka zuwa teku.
Ni ne masoyinki.
MUNGO PARK.
LABARI YA BACE, ISYAKU YA BI SAWU
TO, wannan shi ne iyakar abin da duniya ta sani daga bakin Mungo Park. Don tun da ya tashi daga Sansandin ba a sake samun ko wasikarsa ba. Shiru shiru mutanen bakin teku a Gambiya suka kasa kunne ko su ji duriyarsa, amma ba su ji ba. Har am fara fid da zuciya, sai ran nan cikin 1806 fatake suka kawo mummunan labari na mutuwarsa. Jin haka sai Kanar Maxwell, wanda ke Gwamna a Senegal a lokacin, ya aika da wannan labari Ingila. Da amsa ta dawo, sai Gwamnatin Ingila ta umurci tabbatar da labarin mutuwarsa. In gaskiya ne, a samo dalilin mutuwar da yadda ya mutu, da inda ya kai cikin tafiyarsa. Gwamna Maxwell ya cigita ko zai sami wani mutum mai gaskiya wanda za a iya yarda da magana tasa. Aka yi katari, aka sami lsyaku. Gwamna ya yi masa magana, Isyaku kuwa ya yarda zai tafi bin sawun.
Aka yi wa Isyaku shiri cif, aka ba shi 'yan rakiya. Gwamna Maxwell kuma ya ba shi badujala, da bindiga biyu, da gadon karfe, da alade biyu, da turamen ajanaku, da karnuka biyu, aka ce ya kai wa Sarkin Sego. Isyaku ya kama hanya. Ya kwana ya tashi har Sego. Da ya tafi ya tarar wancan Sarkin ya mutu, babban dansa Da shi ya zama Sarki. Ya sauka a gidan wani bafade da a ke kira Ciyawe, wanda ya je ya fada wa Sarki ga shi ya iso. Da safe bayan an dauke ruwa, Sarki ya aiko ya ce Isyaku ya tafi, amma ya tafi tare da aladen da ya kawo masa a daure, yadda ya taho da su.
Bari mu ji duk yadda aka yi daga bakin Isyaku :
....
(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
WhatsApp: +2348021218337
BBM: 2bddd505
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada
Post a Comment (0)